Page 172
◦ Cikin nutsuwarsa ya yi ma Baba maigadi saida safe, sannan ya wuto cikin bangarensa. Lokaci daya Haj kilishi ta saki labulen windon da ta yaye tana kallon musaddik zuciyarta a dagule, tun bayan dawowarsa gida bata san komai dangane da abinda ya faru ba, domin Afrah bata kara shiga wajenta ba tun daga ranar da ta shiga neman taimakonta.taso ta ji inda ya shiga na tsawon wadannan kwanakin,duk da tafi yarda da yawon iskancinsa da ya saba ya tafi. Sai dai kuma ta na jin damuwar yadda tun bayan dawowar tasa ya rabu da shigowa gida a buge, domin tsawon lokacin da Musaddik zai dawo tana nan makale jikin windo tana jiran dawowarsa a buge, ko yau gashi nan fes da shi, ba cikin kazanta ba, har wata kwalliya taga ya sha, don ganinsa haka sai da gabanta ya fadi domin sosai ya yi mata kama da Musaddik din da, shin meke faruwa? Me yasa abubuwa suke yin baya maimakon su yi gaba su kuma kara tsananta. Afrah, Haj kilishi ta ambaci sunan ta cikin tsana, ta gyada kai kamar tsohuwar kadangaruwa, tabbas shigowar Afrah rayuwar musaddik bata raba daya biyu shine dalilin koma bayan al’amarin ta, dama batun yau take jin wannan fargabar ba, addinin Afrah da maida lamuranta da Allah kadai tasan sun isa su rushe mugun nufinta. Sai dai kuma bata jin zata cigaba da zurawa Afrah ido, zata yi maganinta. Shigar Musaddik cikin falon Afrah da ya samu turowa kawai tayi bata rufe ba, yasa yana shiga ya maida kofar ya rufe da makulli, zaune ya tadda ta kan sallaya ta idar da nafila hannunta na sama tana jero addu’ar ta, gefenta ya samu ya zauna ya zuba mata ido shi ma ya daga na sa hannayen, ta dade tana addu’a daga bisani duk tare suka shafa, a cikin sanyin murya yace “Allah ya amsa”, tayi dan murmushi tana zube masa da ido, ganinsa babu alamar maye ya sata farinciki, kamar yasan irin tunanin da take yi ya yi dan murmushi har gefen kuncinsa daya ya lotsa, sannan yace “Babu abinda na sha, a hayyacina na ke”, ta fadada fara’arta tace “Na gani, yaya musaddik Allah yasa ka dore a hakan”,. Ya yunkura ya tashi yana cewa “Amin, ki taso ki kwanta hakanan ki huta”, ta tashi tana cire hijabin kanta.
Tace “Da so na ke na hada maka ruwan wanka kayi wanka kafin kayi bacci domin zaka fi jindadin bacci”baya son ya na yi mata musu don haka ya kyaleta ta hada masa ruwan wankan. Bayan fitowarsa kuma ta hada masa ruwan lipton me zafi ya sha ya gasa cikinsa, sosai yake jindadin jikinsa, daga bisani ya kwanta domin bacci yake ji sosai, Afrah ma tayi shirin kwanciya ta haye gefen mijinta ta dora fuskarta akan gadon bayansa, jin zuciyarta take tana mata dadi har wani sunsunar jikinsa tana jin irin kamshin da yake yi, fatanta daya Allah ya sa ya dore
Washegari kuwa musaddik bai boyewa Afrah komai ba a game da kiran da Haj Hudah ke yi masa,ta kuma yi masa addu’ar Allah yasa alheri ne, da wuri yabar gida, ya biya wajen harkoknsa daga bisani Karfe goma sha biyu dai-dai na rana Musaddik ne ke zaune a falon Hajiya Hudah, a cikin gidanta. kan daya kujerar me zaman mutum biyu kuwa Hajiya Hudah ce zaune gefenta cikin Kayatacciyar shiga Mai- gidanta ne Alhaji Yusuf Sanda. Tun shigowarsa falon masu aiki ke shigowa da kayan ciye ciye, idanun Alh yusuf sanda na dore akan abincin da ake ajewa lokaci daya kuma yana dawo da kallonsa kan musaddik kamar wanda ke ganin matsayin Musaddik din bai kai a dinga yi masa wannan bajintar ba. Irin kallon da yake ma Musaddik har ya fara tunanin ko dai cikin dabi’arsa kallo yake, domin dai maganar gaskiya ya fara gajiya dan haka ya kosa ta gaya masa dalilin neman nasa ko ya samu ya fita ya bar gidan . Tamkar Hajiya Hudah ta karanci abinda ke cikin zuciyarsa ta dan muskuta ta gyara zamanta, sannan ta fara magana, “kamar yadda na yi maka alkawarin cewa bazan taba mantawa da kai a cikin tafiyata ba, hakan yasa nayi shawara da mijina ya kuma ba ni goyon baya asalima shi da kansa ya kawo shawarar irin aikin da ya kamata na baka,domin a yadda Alh Hamza ya yi min bayaninka yace baka da wani aikin yi da ya wuce zaman banza da kuma irin aikin da muka dakkoka kayi mana”. Musaddik ya gyada kai alamar hakane, a yayinda Alh yusuf sanda ya kara wani narkewa akan kujera yana cigaba da nazartar yanayin musaddik. Haj Hudah ta cigaba da magana “kayi Kokarin da bazan taba mantawa ba, don haka zan baka wannan aikin”. Alh yusuf sanda ya amshe maganar yace “Hakanan na ji zuciyata ta sami nutsuwa da kai , tun a ganina da kai na farko a jiya, naji a raina matata zata samu kariya daga gareka, shi yasa na zabi ta baka irin wannan aikin, domin shi ne nasan ko yaushe zaka iya kasancewa tare da ita, yadda bana zama nasan zan samu nutsuwa a duk lokacin da na tuna kana tare da ita domin tsare lafiyarta”.