Musabbabi Book 1

Page 173

by @yargidanimam

Ya dan rankwafo yana watsa masa irin kallon da Musaddik ya fara tsana, sannan ya cigaba da cewa “ wannan dalilin ne yasa na ce ta daukeka aiki a matsayin me kare lafiyarta na musamman, wanda duk inda zata dole ka kasance tare da ita”, A gaggauce musaddik ya dago ya na kallonsa, ya rasa dalilin murmushin da ya ga Alh yusuf sanda yana yi, idanunsa kuma suna bayyanar da wani irin yanayi sa musaddik bai fahimci komai ba. “Me kare lafiyarta?” Musaddik ya kara tambaya, Alh yusuf sanda ya kara murmusawa yace “Eh, domin a yanayin halittarka nasan zaka iya, don haka ina son ka karbi wannan aikin domin idan ka karba aiki ne wanda ba zaka taba mantawa da shi ba a rayuwarka”, ya karasa magana wannan karon dariya yake sosai ba murmushi.

Haj Hudah ta aje numfashi a hankali, sannan tace “Kada ka damu da albashi, domin zan yanka maka albashi mai tsoka, wanda zai isheka daukar dawainiyar kanka da iyalinka, tunda dama Alh Hamza ya gaya min matarka daya ba ka da da kuma, don haka abu ne mai sauki, albashinka zai jiyar da matarka dadin da kowace mace ke mafarkin samu, domin zan tsaya tsayin daka wajen ganin na inganta rayuwar ku duka kai da matar ta ka”. Alhaji Yusuf Sanda ya muskuta yace “Ka ga ka huta da zaman banza, kuma wannan wata hanya ce ta ci-gabanka, don haka me ka gani? Ina fatan ba za ka ki karbar wannan garabasar ba”. Shuru Alh yusuf sanda ya yi ya kara zuba masa ido tamkar yana addu’a a cikin ransa na cewar Allah yasa ya amshi aikin. Musaddik ya muskuta ya gyara zamansa, ransa da zuciyarsa cike da dimbin tunanin wannan aikin, da hakanan yake jin tamkar hatsari ne a gare shi. Ya nisa yace “Na ji bayananku, sai dai bazan iya baku amsa kai tsaye ba ina bukatar dan lokacin da zan yi tunani