Page 174
idan na yanke shawara zan neme ki na sanar da ke”, fara’ar fuskar yusuf sanda ta dauke ya dube shi da sauri yace “ Har wane tunani zaka yi akan wannan maganar cigabanka ne fa, bana jin akwai mutum irinka da za’ayi masa irin wannan tayin ya bada irin wannan amsar da ka ba da”, Haj Hudah tayi saurin dakatar da shi tace “A’a bar shi yaje ya yi tunaninsa ai babu komai”, ta dawo da kallonta gare shi tace “ kada ka damu kaje kayi tunaninka, na baka dukkan lokacin da kake so”, Musaddik yace “Nagode Hajiyan Allah”, Alh yusuf sanda ya girgiza kai yace “ shikenan amma ina fatan duk tunanin da zaka yi, karshe ya zama eh ce amsarka”, ido kawai musaddik shi ma ya sama Alh yusuf sanda yana tunanin tamkar dalilin da ya fada da yake son ya yi aiki a karkashin matarsa ba shi kadaine dalilinsa ba, domin yadda yaga tsantsar damuwa a cikin idanunsa don kawai bai amshi tayinsu farat daya ba. Ko da ya tashi zai tafi, baisan wane tunanin Alh yusuf sanda ya yi ba ya karkace ya fito da kudi masu yawa ya mikama musaddik, ya amsa yayi godiya sannan ya yi musu sallama. Har ya fice daga falon Haj Hudah shi take yi ma wani irin sassanyan kallo, shi kuma Alh yusuf sanda ita yake kallo, daga bisani ya jinjina kai gami da lumshe idanunsa.
A ranar da wuri Musaddik ya koma gida, bai bari ya yi daren da ya saba ba, sannan bai sha wani abu mai karfi ba wanda zai gusar masa da hankali saboda yana so ya yi magana da Afrah, musamman akan shawarar da ya ce ta yi. Yau ita ce rana ta biyu. Afrah na zaune akan kujera, zuciyarta cike da tunane- tunane Musaddik ya yi sallama ya shigo, cike da mamakin dawowarsa da wuri, ta amsa sallamar, Ya shigo ya zauna daf da ita, Bayan ta yi masa sannu da zuwa ne, ta ta shi domin ta dauko masa abinci, ya dubeta cikin yanayi na kulawa yace "Ina za ki je” ta dakata tana kallonsa tace “zan je na dakko maka abinci ne, nasan tunda ka dawo da wuri kila kana jin yunwa”, ya mika hannu ya hanyo hannunta ya zaunar da ita kusa da shi sosai yana kallonta yace “ zo kiyi zamanki, ba na Jindadin cikina da daddaren nan, babu abinda zan iya ci, kila ko sai dan ruwan lipton din nan naki me dadi”, tayi murmushi tace “ to bari naje na dora”, ya girgiza kai yace “ Aa ki bari sai anjima , idan mun gama magana” , ta bude ido sosai tace “ wace magana kuma zamu yi?”, ya kara matse hannanta a cikin nasa yace “ kin manta maganar mu ta shekaranjiya”, nan da nan ta canja fuska, ta shiga kokarin zame hannunta a cikin nasa, shi kuma ya kara matse hannun yana cigaba da shafawa.