Page 175
A hankali cikin faduwar gaba yace “Afrah ina son na ji shawarar da ki ka yanke akan maganar da muka yi, ina son kuma ki sani na baki wannan zabin ne saboda banda wani zabi”ya fadì maganar ne cikin faduwar gaba, domin bai san dalilin da ya sa ya sami kansa da addu'ar Allah ya sa ba ta zabi rabuwa da shi ba, domin yana jin tamkar bazai iya jure rabuwa da ita ba, yana jin wani abu a game da ita me wuyar fassara. Afrah ta gyara zamanta, har yanzu hannayensu na manne da na juna. Ta dube shi sosai, sannan ta ce "Kasan musabbin aurena da kai?”, kai ya girgiza alamar bai sani ba, yace, "Ban sani ba, amma dai nasan duk wani musabbabi ba zai wuce biyayyar iyaye ba”, ta gyada kai tace “Bazan ce babu ba, tabbas akwai biyayyar a ciki, amma ina son ka sani na aure ka ne akan kyakkyawar niyyar mu na kokarin saka hanya ta-gari, ba kamun kanka na aura ba, balle nace saboda ba ka da kamun kai zan rabu da kai, babu halinka daya da ban sani ba kuma na aureka, to don me zaka kawo kalmar rabuwa a tsananin mu, bance na gaji ba, don me ka ke son ka gajiyar da ni
Yar gidan imam MUSABBABI
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM