Musabbabi Book 1

Page 176

by @yargidanimam

to wai ma me yasa kake son mu rabu akan dalilin da yasa muka hadu, ba ni da burin rabuwa da kai ko da na kiftawar ido ne”, idonsa na cikin nata musaddik ji yake kamar ana zuba masa ruwan sanyi a cikin kirjinsa.

Afrah ta numfasa ta cigaba da cewa “Duk irin abinda ka ke hange akan rayuwata a dalilin auranka, ni ma na hangi irinsa kafin na aureka, amma kai ne mijin da Allah ya kaddara min, kuma kai ne wanda na ke fatan na gama rayuwata da shi a matsayin mijina”

Haka nan wani dadì ya dinga bakuntar zuciyar Musaddik, wani irin so da kaunar Afrah me tsanani ya dinga kutsowa yana Kara samun wajen zama a cikin zuciyarsa,duk yadda ya so ya ki yarda da cewa yana son Afrah hakan ya faskara, domin a wannan daren ya tabbatar ma da kansa cewa yana son Afrah so na hakika. darajarta da kimarta suka kara fadada a cikin ransa, ta zuba idanunta a cikin nasa, sannan ta ci-gaba da magana "Eh, na yarda a lokacin da na aureka, biyayya ce da son cika buri da umarnin mahaifina, Amma babu soyayyarka a zuciyata, amma a yanzu ina tabbatar maka da cewa zuciyata cike take da soyayyarka, ina sonka da zuciya daya, ba kuma na fatan rabuwa da kai, don halayenka munana, domin a Yadda na sanka da , ina sa ran wata rana za ka koma haka, Na kuma amshi komai a matsayin Kaddarar rayuwata, don haka ni ba zan rabu da kai ba, zan zauna tare da kai da dadi ba dadì, zan ci-gaba da yi maka addu'a tare da zama mata ta-gari a gareka,”