Musabbabi Book 1

Page 177

by @yargidanimam

Ta dago tana kallon rikitattun idanunsa tace “Ka ji shawarar da na yanke." ta kara gyara zamanta ta ci-gaba da cewa “ Ya rage ruwanka, ka kyautata min tare da sauke hakkin da ke kanka nawa, Ko yin akasin haka, ni dai ina nan tare da kai”. Tana gama fadin haka, ta yi gaggawar zare hannunsa a cikin nasa ta mike zata shiga uwardaka, Musaddik baisan lokacin da yasa hannu a gaggauce ya riko hannunta gami da janyota gaba daya ta fado jikinsa, a zafafe ya sa hannayensa biyu duka ya rungumeta tsam! A kirjinsa tamkar Zai tsaga jikinsa, ya sanyata a ciki. Haka nan ya sami kansa da kuka sosai, hawayensa na sauka a gadon bayanta, cikin kuka yake magana "Afrah zuciyata ta yi nauyi, tabbas na so na ba ki farin-cikin da ki ke bukata, na so na natsu, na koma mutum nagari saboda soyayyarki, ke ta dabance Afrah, ina sonki fiye da tunanin ki”, Afrah ta runtse idanunta itama hawaye ya na fita mata gabanta na faduwa saboda ta ji kalmar da take fatan ji daga bakinsa, cikin sanyin murya tace “kana sona”, ya kara matseta a kirjinsa yace “ina sonki Afrah so na hakika”. Ta saki ajiyar zuciya tace “Ni ma na ina sonka yaya Musaddik , kuma zan iya zama da kai a cikin kowane hali da yanayi." Musaddik ya ce, "Kaunarki ita ce ta sa na ke miki hangen kyakkyawar rayuwa a wani wajen, don na san ba za ki yi farin-ciki tare da ni ba" Ta girgiza kai tace “Ka yi kuskure, domin da kai kadai zan iya zama na sami farin-ciki”. Musaddik ya dagota yana kallon fuskarta gami da goge hawayen da ke zuba mata yace "Ba zan yi miki alkawarin zan daina duk abinda na ke ba, amma zan yi Kokari na dainan ba