Musabbabi Book 1

Page 178

by @yargidanimam

tare da na yi miki alkawari ba”, ta lumshe idanunta gami da yin ajiyar zuciya ta ce "Allah ya tabbatar da hakan, Allah yasa zan kuma cigaba da yi maka addu’a “ Ya maida kanta ya kwantar a saman kirjinsa , yana cewa “Nagode Afrah Allah ya kara ba ki hakuri da juriyar zama da ni” Ta kara dagowa ta zuba masa ido gami da gyara zamanta, sannan tace '"Amma ina da shawara daya” ya saki hannunta yana cigaba da kallonta yace "Shawarar menene?”, Ta dan dube shi fuska sake, sannan tace “Me zai hana ka nemi aikin yi, ka na da takardunka, tun daga Primary har Masters, A yanzu ne za su yi maka amfani, sannan samun aikinka zai rage abubuwa da dama, kuma hanya ce ta samun natsuwarka, wannan zaman babu aiki, shi ne musabbabin kara lalacewarka" Ya kamo hannunta ya rike yana kallonta cikin wani murmushi wanda ya kara masa kyau, sannan yace “Wannan yana daya daga cikin maganar da na ke son na yi da ke, bayan wannan maganar da mu kayi,saboda ina son na nemi shawararki, don yanzu ba abinda zan yi ba tare da shawararki ba, don na fahimci ban da kowa duniya, bayan ke da kawu mahnud da inna Halimata, domin sune silar samun ki a cikin rayuwata”. Ta ji dadin maganarsa, ta yi murmushi tace “To ya aka yi?" Ya gyara zamansa ya kwashe duk yadda suka yi da Hajiya Hudah ya gaya mata,ya cigaba da cewa “shi kansa mijin nata na fahimci yana matukar son na karbi aikin, sai dai ina ganin kamar aikin yana da hatsari, kuma ba zan sami lokacin kaina ba" Afrah ta runtse idanunta cike da fara'a ta gyara zama, tabbas wannan Haj Hudah tana son ta taimaki musaddik sannan kuma irin wannan aikin irinsa yakamaci mutum irin Musaddik aikin da sam bazai sami lokacin kansa ba, balle ya samu lokacin da zai je ya aikata abinda bai dace ba. Don haka wannan aikin dole ta bashi karfin guiwar amsar aikin nan. Ta kara kallonsa tace "Yaya Musaddik irin aikin nan shi ne ya dace da kai, domin in dai har da gaske kana son daina abinda kake yi, to ka karbi aikin nan domin rashin samun lokacin naka, shi zai sa ka nisanci abokanka na banza, ya kuma nisantaka da aikata halayen banza, tunda cikin jama'ar kirki za ka dinga