Page 179
shiga, dole ka dinga jin nauyin aikata abubuwan da suka sha bamban da nasu halayen”, ido kawai ya dora mata har ta cigaba da cewa “Duk da dai ba irin wannan aikin bane ya dace da kai, a matsayin ka na me masters, sai dai babu komai da babu gwara ba dadi, wannan din ma Allah yasa masa albarka”, ya kara murmusawa yace “Na fahimce ki, sai dai kuma ni banji natsuwa akan wannan aikin ba, amma tunda kin kawo wannan shawarar zan amshi aikin nata”, tayi murmushi sosai tace “Alhamdulillah “, ya matso kusa da ita sosai yace “sai dai duk da haka zan fara neman aiki da takarduna, zan nemi abokina murtala zan bashi takarduna ya cigaba da nemar min aiki, a duk kuma lokacin da na samu wani aikin zan aje ma Haj Hudah nata aikin “. Afrah ta saki murmushi tace “Hakan ma ya yi yaya musaddik, Allah yasa alheri “,
Ya sa hannayensa ya kara janyota ya rungumeta, yana jin soyayyarta har cikin bargonsa. A wannan daren dai zuciyoyinsu sun aminta da soyayyar juna, wanda wannan shine mataki na farko na samun cikar burin Afrah da Mallam Mahmud da inna Halima. domin tabbas idan akwai soyayya komai zai zo da sauki.