Page 180
Washegari karfe biyu na rana Musaddik yana gaban ofishin da Murtala ya koma, tun bayan barinsa kamfanin Musaddik. Murtala Ya ji dadì ya kuma yi murna da ganin ya cika da farincikin yadda Musaddik har ya yi tunanin neman aikin yi. A zahiri sai yanzu ya fara sa ran shiryuwar Musaddik, a dalilin auransa, abinda ya dade yana addu’ar tabbatarsa, domin tun barinsa aiki a kamfanin Musaddik ko haduwa ya daina yarda su yi, idan kuma ya gano shi daker, da zaran ya fara masa nasiha zasu rabu baram baram, daga bisani ma wata rana da yaje nemansa gida da kanta Haj kilishi ta fito ta yi masa gargadin kada ya kara zuwa neman Musaddik ya fita harkarsa. Tun daga lokacin ya ja baya da shi. Yau kuma sai gashi ya zo har inda yake. Cikin tsananin farinciki ya dubi Musaddik ya ce, "'Na ji dadì kwarai, da tunanin ka ya fara dawo maka. domin kullum addu’a ta kenan, saboda haka in sha Allahu zan yi iya kokarina wajen nemar maka aiki, domin ba zan taba mantawa da irin taimakon da ka yi min ba a lokacin da na ke aiki a kamfaninka, ba ka daukeni ma'aikacinka ba, ka daukeni aboki, kuma amini, kuma kaddara da karayar arziki babu wanda ya gagara Allah ya jarabce shi “. Musaddik ya jinjina kai, karo da dama Kenan daya tuna irin daula da arziki da dimbin dukiyar daya mallaka a baya, wanda babu takamaiman takamaiman abinda zai iya fadì, na dalilin faruwar abinda ya farun . Musaddik ya jinjina kai yace “Haka ne Murtala na gode kwarai da gaske. Allah ya taimaka." Murtala ya ce, yana kallonsa “Allah ya shirya mana kai ka dawo da irin rayuwarka ta asali”. A hankali yace “Amin Murtala, na gode"
Dai-dai lokacin wayarsa ta dauki ruri da sauri ya tura hannu a aljihu ya dakko wayar, ya dubi number sosai ba shi da ita a cikin wayar, don haka ya dauka lokaci daya ya kara a kunnansa gami da yin sallama.
Daga can daya bangaren, cikin wata murya me cike da izza Alh yusuf sanda ya amsa sallamar lokaci daya ya kara da cewa, “Alh yusuf sanda ne ke magana”…….
Yar gidan imam MUSABBABI
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM