Page 181
Musaddik ya yi saurin gyara zamansa ya ce, “Alhajin Allah,barka da rana”, cikin isa Alh yusuf sanda ya ja numfashi sannan yace “yauwa kana lafiya”, ya jinjina kai yace “lafiya lau,ina fatan dai lafiya domin ban yi zaton jin kiranka ba a wannan lokacin”, Alh yusuf sanda ya wani tamke fuska tamkar yana ganin musaddik, sannan ya maida bayansa ya kwantar a kujerar da yake kai,sannan Yace “Na sami lambarka a wayar Hudah ne,sannan na kiraka ne, domin na ji shawarar da ka yanke akan aikin da Hudah ta ba ka, saboda ni Jibi na ke sa ran komawa Paris, ba kuma na son na bar kasar ba tare da na Ji abinda ka yanke akai ba”, ya yi shuru kamar me jiran tsammani.
Musaddik cike da mamakin yadda ya ga Alhaji Yusuf ya damu da lamarin aikin, wanda shi a ganinsa bai ga dalili ba, ya dan waiwaya ya dubi murtala wanda shi ma shi yake kallo, sannan a hankali ya dauke kallonsa a kansa, gami sa muskutawa, wanda zuwa lokacin Alh yusuf sanda har hakurinsa ya gaza yace “kayi shuru, wannan fa dama ce a gareka wanda ba kowa yake samun irin damar ba”, Musaddik ya kara muskutawa, bai bari tunanin da yake yi ya sa shi canja shawara ba, yace "Ba damuwa, na ji, na kuma amince zan yi aikin”.
Alhaji Yusuf sanda ya yi murmushi sosai tamkar wanda ya gama cika dukkan burinsa na duniya, ya lumshe ido ya bude ya kara baza babbar rigarsa a kan kujerar da yake zaune, lokaci daya yasa hannunsa daya yana shafa gemun da ya cika masa fuska.gami da gyada kai sannan ya ce, "To shi kenan, ina tayaka murna ,sai ka samu ka bullo zuwa yamma, domin ka ji yadda tsarin akin yake" hakanan musaddik ya ji gaba daya guiwoyinsa sunyi sanyi, a sanyaye yace “To nagode in sha Allah zanyi kokarin zuwa anjiman”, Alh yusuf sanda ya riga shi aje wayar, cike da murmushi ya mike ya shiga shawagi a tsakiyar katon falon.
A yayin da Murtala ya dubi Musaddik sosai yace “Musaddik kai da waye a waya”, ya saki ajiyar zuciya yace "Alhaji Yusuf Sanda ne Mai-gidan Hajiya Hudah, ya kira ni ne akan aikin da na yi maka bayani dazu, dalilin da yasa ya kirani kenan, shi yasa na gaya masa na amince." Murtala ya numfasa yana yi ma musaddik wani irin kallo me kama da kayi hankali,sannan ya ce "A gaskiya ka yi taka-tsantsan! Kuma ni na ma kasa gane wane irin miji ne Alhaji Yusuf Sanda, wanda baya kishin matarsa, da har neman me kare lafiyar matarsa yake a bayan idonsa, shi zaman me yake da bazai zama me kare lafiyarta din ba, musaddik bana jin nutsuwa akan aikin nan”.