Page 182
Musaddik ya dubi murtala ya ce, "Ni kaina abin yana daure min kai, ya damu kwarai da maganar aikin nan fiye da yadda Haj Hudah ta damu” murtala yace "Koma dai menene, ka sani dole sai ka natsu ka san abinda ka ke yi, saboda wanan aikin yana da hatsari “Ya ce, “Hakane Murtala, na kuma gode da shawararka, zan kuma kula sosai” Murtala ya ce "Ba don wannan wata babbar dama ce a gareka ba na yin aiki a karkashin mace kamar Haj Hudah Yar Majalisa, da nace ka yi hakuri ka jira asamu wani aikin , amma matsalar bansan iya wane lokaci za’a dauka ba’a sami aikin ba, kuma shi wannan aikin ko da ban san nawa ne albashin da za ta yanka maka ba, na san za ka sami damar wadata iyalinka, aikin kuma zai sa ma maka daraja da kima”.
Musaddik yace “Tunanin da daga ni har Afrah mu kayi kenan yasa muka yanke shawarar karbar aikin , saboda ni a yanzu banda wani buri da ya wuce faranta ran matata “. Murtala ya gyada kai ya yi dariya sosai yace “Angon Afrah,Allah yasa haka shi yafi zama alheri abokina ka kula don Allah “, ya yi murmushi yace “ kada ka damu murtala zan kula”.
Daga nan su ka cigaba da tattaunawa har zuwa lokacin da Murtala ya tashi aiki, daga nan suka dunguma tare suka fita, kowa ya yi na shi wajen domin tafiyar su ba zata zamo daya ba
Musaddik yana zaune a dabar shaye shayen su, yau dai ya dage kadan ya sha ya ki shan komai da yawa duk da har wani zafi zuciyarsa take masa don rashin shan komai yadda ya saba. Kallon abokan shashancin nasa yake yi can kasan zuciyarsa yana jin tsana da kyamatar halayensu, sau tari yakan zauna yana tunanin yadda wadannan mutanen su ka zama sune abokansa yanzun ma tunanin da yake yi kenan, wayar Alh Hamza ta shigo wayarsa, bai bata lokaci ba wajen daukar wayar, shi ma kuma bai wani ja magana ba ya sanar da shi ya shirya duk inda yake karfe biyar zai zo ya dakko shi bisa umarnin Alh yusuf sanda, Toh kawai musaddik yace masa tare da gaya masa inda zai gan shi.sannan su kayi sallama, lokaci daya musaddik na cigaba da mamakin irin wannan kaguwa da Alh yusuf sanda yayi akan aikin da yasan bazai amfane shi da komai ba, shi ne kadai zai amfana da shi amma yadda yake nunawa tamkar shi ne zai amfana fiye da shi.
Wajen karfe biyar da rabi Alhaji Hamza ya iso inda zasu hadu da musaddik ya dauke shi zuwa gidan Hajiya Hudah. Gidan cike yake da jama’a masu neman taimako , su kam cikin alfarmarsu suka shiga cikin gidan har cikin katon falon da nanne Haj Hudah take zama da duk wani mutum me muhimmanci da ya zo wajenta. Yanzu ma tana zaune Ta sha kwalliya sai walkiya take yi,kyanta ya fito sosai gafenta Alhaji Yusuf Sanda ne, shi ma ya ci shadda me tsada tamkar me shirin zuwa liyafa. Hajiya Hudah ta rasa dalilin da ya sa take rasa dukkan natsuwarta, a duk lokacin da Musaddik ke gabanta Kuma ko mutane sun kai dubu, ta kan ga Musaddik din ya bambanta da kowa, musamman wajen kwarjini, da cikar kyawu, shi din komai nasa na dabanne, hakan yasa take jin takaici idan Alh Hamza ya na nuna mata Musaddik wani wulakantacce ne, wanda baida wata kyakkyawar makoma.
Sun tattauna sosai akan aikin, Alh yusuf sanda yafi kowa zakewa shi ne kuma me fadin yadda aikin zai kasance , ido kawai musaddik yasa masa har ya gama fadan abinda yake so, a tunaninsa musaddik bazai kawo wata magana ba, ga mamakinsa sai ya ga Musaddik ya gyara zama ya fara kafa na shi sharudan.