Musabbabi Book 1

Page 183

by @yargidanimam

Cike da nuna shi ma yasan yancinsa yace “Da farko kun san dai ni magidanci ne ,matata na bukatata ako wane lokaci don haka babu wani aiki da zaisa na wafintar da iyalina, don haka maganar da kayi megida na awa goma sha takwas na awannin ranata zanyi su ne wajen kula da Haj bazai yuwu ba, awa goma sha daya kawai zan iya sadaukarwa daga karfe bakwai na safe zuwa karfe shida na yamma, daganan zan tashi na je na ga iyalina”. Ya kara kallon Alh yusuf sanda da shi ma ya zuba masa ido, tunaninsa na musaddik sakaraine ya fara barin zuciyarsa. Lokaci daya ya kara sauke idonsa kan matarsa, wacce ta dazu tamkar ta manta a inda take, domin yadda ta zubama musaddik ido bata ko kiftawa. Murmushi kawai ya yi gami da dauke kansa yana cigaba da girgiza kansa. Musaddik ya cigaba da cewa “ sannan komai runtsi bazan dinga kwana a cikin gidanta ba,kuma duk wata tafiya idan ta kwana ce baza ni ba” ya dakata yana kallonsu yace “wannan sune sharudana idan kun amince shikenan ko gobe zan iya fara aiki,idan kuma baku amince ba sai a hakura”.

Da gangan Alh yusuf sanda ya yi shuru yana cigaba da nazarin yanayin Haj Hudah, so yake yasan abinda ta yanke a karan kanta,ita ko Zahiri Hajiya Hudah har cikin ranta tana matukar son ganin Musaddik kusa da ita, domin ta rasa dalilin da yasa take jin wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali a duk lokacin da Musaddik ya kasance kusa da ita, ko wannan aikin ma ta dai bukaci ya yi ne kawai, amma tana da jami’an tsaronta masu bin ta duk inda zata je, bayan masu yin gadin gidanta. don haka wannan sharadin na Musaddik, bai dameta ba, ba kuma zai hanata daukarsa aikin ba, Don haka ba tare da wani dogon nazari ba ta yi saurin amincewa, wanda dama abinda Alh yusuf sanda yake tsammanin ji kenan daga gareta.

Zama kawai ya kara gyarawa yana cigaba da girgiza kafafunsa, sannan yace “Badamuwa musaddik duk sharudan da ka aje na yarda kamar yadda Hudah ta amince “. Alh Hamza ya yi murmushi yace “Alhamdulillah musaddik ina tayaka murna, lalle ka shigo tafiyar nan da kafar dama”. Haj Hudah ta dan waiwayi inda Alh yusuf sanda ke zaune, idonsa na kafe a kanta, ta dauke idonta ta dawo da shi kan musaddik tace "Dama saboda na tabbatar da na yi tafiya da kai a cikin siyasata, bayan na ci zabe, ya sa na ba ka wannan aikin, saboda ka sami abinda zaka dinga ciyar da iyalinka, ba tare da wahala ba, uwa uba ina son na tabbatar maka da cewa tafiyata tafiyace ta amana “, Musaddik ya jinjina kai yace “Hakane, nagode Allah ya kara girma”