Page 184
Alh yusuf sanda yace “ Sai ki gaya masa albashin sa”, Haj Hudah tayi murmushi ta kara kallon musaddik tace “Duk wata zan dinga biyanka naira dubu dari, ina fatan sun yi?”, Alh Hamza ya bude ido ya na mamaki, lalle musaddik ya haye, shi da yake wahala da ita tun da dadewa bai amfana da komai ba a duk wata, sai musaddik da ya shigo tafiyar jiya jiya, sai dinga tashi da dubu dari duk wata sannan ga wata irin daraja da yaga ya samu, ji ya yi wani abu me kama da hassada yana tsikarar zuciyarsa. Musaddik shi ma cikin farinciki yace “Nagode, sunyi rankiyadade Allah ya kara girma”, sosai yake nanata yawan kudin a cikin zuciyarsa, Afrah kawai yake hangowa da tunanin yadda zai dinga faranta mata da wannan kudin na halak domin burinsa kenan ya ciyar da matarsa da halak .jin kudin yake kamar bai taba rike irinsu ba, bayan in banda canjin rayuwa meye dubu dari a wajen musaddik kudin da bai wuce ya ba da kyautarsu ba kullum. Daga bisani Alh yusuf sanda ya mike yana dukan iska, sai dai fuskarsa dauke take da murmushin da shi kadai yasan dalili, ya shige cikin gidan. Daga karshe su ma suka yi mata sallama bayan ta sanar da shi daga gobe zai fara zuwa aiki. Ta ba Alh Hamza dubu ashirin tace yasa mai a mota, duk kuma inda musaddik zai je ya tafi yaje ya sauke shi. Ya jidadin kudin domin baima yi tsammanin zata bashi ko sisi ba, a ransa dai yace ya ci albarkacin musaddik ne. Kai tsaye gida ya aje musaddik kamar yadda ya bukata. Karfe takwas da rabi ne na dare, ko kadan babu wanda ya tsammaci dawowarsa a wannan lokacin, hakan yasa muryarsa da Haj kilishi ta ji yana magana da Baba maigadi yasa ta yi saurin dage labulen leken gulmarta, don ta tabbatar da shi ne, fuskarta ta canja bakinciki da takaici ya lullubeta, jin zuciyarta take tana bugawa. A fusace ta saki labulen, wai me ke faruwa ne? Kwana nawa kenan musaddik bai dawo gida a buge ba, yanayinsa ya fara canjawa ba taga kazanta a tare da shi ba, fes yake, yauma har wani wasa da dariya ta ga yana yi shi da maigadi, ta tsani ganin murmushi a fuskarsa ta tsani ganin natsuwa a tare da shi, shin ko dai asirin ya karye ne?. Ta tambayi kanta lokaci daya kuma ta girgiza kai tana karfafama kanta guiwar cewa asirin bai karye ba, don tasan babu wanda ya tono tukunyar nan, gabanta ya fadi ta mike ta shiga shawagi tana tunanin idan kuma wani yaje ya tone ne fa ko da da kuskure. Da sauri ta dakko wayarta