Page 185
Ta danna number Haj Rakiya bugu biyu a cikin na uku ta dauka, tana kokarin tsame hannunta a cikin tuwon shinkafar da take ci, “Da girman kujerarki”, cikin sautin muryarta me cike da damuwa tace “Haj bana cikin nutsuwata”, tayi tsam da ranta tace “ me ya faru Haj”, Haj kilishi ta saki ajiyar zuciya tace “Abubuwa ne na ke ta ganin canjinsu ko kinsan musaddik yanzu kwana biyun nan ya daina dawowa gida a buge, kuma ina ganinsa tsaf cikin tsaftarsa kamar yadda yake da, yadda yake zama duku duku yanzu babu datti a kayansa, yadda kuma yake shigowa ya gaishe ni ina shan kamshi shi ma duk ya daina shigowa, itama kinibabbiyar matarsa ta daina shigowa,” Ta ja numfashi ta cigaba da magana ba tare da Haj Rakiya ta katseta ba, “Ni daman batun yau ba nasan auren wannan fitinanniyar yarinyar da Musaddik fitina ne kawai a gare bi, shi yasa ban so akayi ba don dai banda yadda zanyi ne kawai,” Haj Rakiya tace “ ki kwantar da hankalin ki Haj, ke yanzu meye tunaninki”, a daburce tace “ ina tunanin ko wani yaje ya tone asirin nan ne”, da sauri tace “ wa haba Haj ki daina wannan tunanin, yadda na ke kula da kaina haka nake kula da wannan ajiyar, ta yaya zan dauke kaina a kai bayan irin alherin da kike yi min, duk don na kula da wajen”. Haj kilishi tace “ Na sani Haj amma yanzu ki je ki duba wajen ki gani ko na samu sukuni”. Ta yunkura ta tashi tace “ tunda kin damu bari naje yanzu”, ta kashe wayar, ta wuce ta wanke hannunta, ta zari gyale ta fice da sauri. Ta je ta samu bakin kukar lafiya lau babu inda aka tone, tun a bakin kukar ta kira Haj kilishi ta sanar da ita komai lafiya lau ta kwantar da hankalinta, canjin da ta gani ba wata bace sila illa Afrah amma batun shaye shaye babu abinda zai hana shi yi. Karo da dama kenan da Haj kilishi taji tsanar Afrah ta kara baibayeta, tana ganin lokaci ya yi da zata kai maganarta wajen boka mai rakwacam.
Ita kam Afrah a dai dai wannan lokacin suna can cikin farinciki ita da Musaddik, domin Afrah tafi kowa jindadin samun aikin nasa, ga albashi mai tsoka, gashi an kwashe masa mafiyawan lokacin da yake da shi, don haka dole ayyukan da yake aikatawa masu muni su ragu.
Har ya sayyadi Habib washegari da taje islamiyya sai da ta gayama. Sosai shi ma ya jidadi, domin yadda yaga farinciki a fuskar Afrah ya fi masa komai dadi ya yi addu’ar Allah kara kawo sanadiyyar shiryuwar musaddik ko don Afrah ta cigaba da samun farinciki.
daga Islamiyya kuwa bayan an tashi kai tsaye Afrah gidansu ta wuce, domin ta sanar da mahaifinta kyakkyawan labari. Sai dai kamar kullum Babu wata kyakkyawar tarba da ta samu da ga gun Mama Hauwa, sai ma harare-harare gami da kumbure-kumbure da take yi. Ita kuwa Na’ima dama ba ta nan, ta tafi Suleja bikin kawarta. Haka Afrah ta ci-gaba da zama a darare tana zaman jiran mahaifinta, yana ko dawowa, ta gaya masa maganar samun aikin Musaddik har da iya adadin albashin da zai dinga kwasa duk wata, Mama Hauwa na gefe tana ji, bakin-ciki ya cika mata ciki, hatta numfashi wahalar fita yake mata saboda tsananin hassada, nan da nan idanunta suka rine su ka yi jawur,Yaushe Musaddik har ya yi hankalin da zai yi tunanin neman aiki, kuma aikin ma me tsoka haka, kuma ma ko ba komai yana tare da manyan mutane Hajiya Hudah yar Majalisa guda, ai alheri kala-kala ya dinga samunsa kenan daga gareta, kilama har daga abokan arzikinta. Zahiri ba ta ji dadin wannan al'amari ba.
A yayin da Malam Mahmud farin-ciki ya cika zuciyarsa ya ji dad sosai, ya kuma yi masu addu'a ta-gari, tabbas tun bayan auransu da Afrah Sai yanzu ya dan fara samun natsuwa, domin tabbas sun fara ganin cigaba, a yau kuma ya kara jin karfin guiwar cewa in sha Allah Afrah zata zama silar maida musaddik nagari cikin taimakon ubangiji.Ya so kwarai ta tsaya ta ci abincin dare, tunda an kusa gamawa, amma Afrah ta ki, saboda yadda ta ga Mama Hauwa take kaiwa da komowa cikin tsananin fusata .
Yar gidan imam ✍️ MUSABBABI
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM