Musabbabi Book 1

Page 186

by @yargidanimam

hakan yasa tasan tsayawarta cin abincin ba karamin damuwa zai haifar ba,shi ma Mallam Mahmud din bai matsa mata ba, domin ya san tana da dalilin kin tsayawa ta ci abincin , domin har kullum yasan baiyi sa’ar matar farko ba, halin Mama Hauwa na son rai da son kai, da rashin kallon dan wani a matsayin da, da yana da iko da tuni ya rabata da wannan halin, shi yasa bazai taba daina kewar mahaifiyar Afrah ba, mace me kirki da sanin yakamata wacce ta bashi gatan da bazai taba mantawa ba. Afrah ta yi masa sallama, Ita ko Mama Hauwa ko da ta yi mata sallamar a ciki ta amsa saboda bakin-ciki, ita ma Afran ba ta saurareta ba, ta yi tafiyarta, mahaifinta na sa mata albarka kamar yadda ya saba a kullum.

Afrah na fita kai tsaye gidan Inna Halima ta wuce. Ita ma ta gaya mata batun samun aikin musaddik Inna Halima cike da farin-ciki ta sanar da ita dazun nan Musaddik din ya zo ya gaya mata da kansa. Inna Halima ta yi addu’a sosai, ta kuma yi ma Afrah godiya abisa wannan canjin da ake samu. Anan gidan ta ci tuwon masara miyar kubewa danya wacce ta ji bushasshen kifi da man shanu, ta ci ta koshi, harda yi ma musaddik guzuri sanin yana son miyar kubewa tun daga danya har bushasshiya. Daga bisani ta kama hanyar gida zuciyarta cike da farinciki. Domin wannan samun aikin nasa, ya kawo farinciki a rayuwarsu duka.

Washegari kuwa Afrah da kanta ta shirya mijinta, dama tun dare ta hana idonta bacci har sai da aka kawo wuta ta goge masa kayan da zaisa gobe. Karfe bakwai saura kwata hatta abin karyawa musaddik ya gama ci, Afrah ta ta gama masa komai, sai da zai tafi ne ta dube shi tana murmushi tace “ yaya kaga yadda kayi kyau kuwa kyau ace daganan sai wani katon office”, shi ma ya yi dariya yace “Wannan duk me sauki ne idan Allah ya sa mana hannu”, ta kara kallonsa ya na kokarin fita tace “ka gayama Haj kuwa ka samu aiki?”, ya girgiza kai yace “Ban gaya mata ba ai ni rabona da shiga cikin gidan ma na so na manta”, ta girgiza kai tace “Baka kyauta ba, ai yakamata ta sani, saboda haka kafin ka wuce ka shiga ka gaya mata".

Ya wuce ya na tafiya yana fadin “ kai Afrah ki yi hakuri, idan nace zanyi hakan zan makara,ayi min addu’a “, ya karasa ficewa da sauri, Afrah ta bi shi da kallo cike da sha’awar sa, mijinta fa tamkar da dubu ne, dubi yadda ya fito ya yi kyau cikin shiga ta kamala kai idan ba an gaya maka ba babu yadda za’ayi ka dauka yana da wata nakasa ta dabi’ar rayuwa.