Musabbabi Book 1

Page 187

by @yargidanimam

Afrah ta yi addu’ar Allah yasa wannan aikin hanyar shiriyarsa ce, Allah kuma ya kauda duk wata fitinar da ke cikin aikin ya hadasu da alherin da ke ciki. Bayan tafiyarsa, Afrah ta dan koma bacci , wajen karfe goma ta tashi ta yi wanka ta yi kwalliyarta cikin doguwar riga me ruwan kasa, kai tsaye cikin gidan ta shiga wanda rabonta da shiga tun ranar da Haj kilishi da Haj Rakiya su ka yi mata wulakanci.har falo Afrah ta sami Haj Kilishi tana zaune tana zuba mulki tana shakar kamshi, tamkar mutuwa da rayuwa a hannunta suke, bata damu ba ta nemi waje ta zauna, gaisuwar ma daker take amsawa nan ma ko a jikin Afrah, illa gyara zama da ta yi ta sanar da ita dalilin zuwanta, wanda bai wuce yar majalisa Haj Hudah yunus ta ba musaddik aiki tare da albashi me kauri ba.

Afrah ba ta yi mamakin yadda ta ga tashin hankali ya bayyana a tare da Haj kilishi ba, domin dai da a kishingide Hajiya Kilishi take, amma tana jin wannan maganar, ta yi zumbur ta tashi ta zauna sosai, tana kallonta fuskarta cike da bacin rai hade da mamakin jin maganar, cikin wata irin murya tace “Ya sami aiki?" Afrah , ta gyada kai , sosai take Jindadin ganin damuwa a fuskar Haj kilishi, domin tuni ta gama fahimtar ba ta kaunar musaddik don haka tasan duk wani abin alheri da zai same shi ba zata taba farinciki ba.

Tace “Eh, ya sami aiki, shi ne na ga ya Kamata na zo na gaya miki, kafin shi ma ya zo ya gaya miki, don nasan zai zo”, Haj kilishi ta watsa mata harara tace “ ya zo ya gaya min ta yaya? Bayan yanzu kece komai dinsa, don haka tunda kin zo kin gaya min ai bazai zo ba” Afrah bata ce uffan ba illa kara gyara zama da ta yi akan kujerar da ada bata da ko ikon zama saboda hada ran da zata gani a gun Haj kilishi kadai ya isa ta kasa zama a kujerar, amma yau ta riga ta dake babu tsoron Haj kilishi a zuciyarta ko da kwayar zarra ne. Ta kara jifanta da wata hararar tace “yaushe rabonsa da shigowa ya gaishe ni, saboda yana cikin daula yan siyasa suna ba shi gata shi yasa ashe yake kokarin wofintar da ni, to shikenan Allah ya sanya alheri”. Haj kilishi Ta na kawo wannan gabar Afrah ta mike tace “Dama abinda nake jira kenan na ji kin fada, amin”. Bata saurari komai ba ta fice, yayinda Haj kilishi ta bi ta da wani irin kallon mamaki, Afrah ta canja fa, wai me ke faruwa ne, da sauri ta janyo watarta ta danna lambar Hajiya Rakiya ta Kira bugu daya kamar ta na jira Hajiya Rakiya ta dauka. Hajiya Kilishi ba ta damu da amsa gaisuwar da Hajiya Rakiya take mata ba , ta fara magana cikin damuwa da bacin rai,gami da tashin hankali, “Na gaya miki akwai matsala, ni fa banda wani kwanciyar hankali, ko kinsan yar majalisa Haj Hudah yunus ta ba wannan fitinannen yaron musaddik aikin yi”. Haj Rakiya itama nan da nan ta daburce tace “Assha, ta bashi aikin yi , har yaushe ya samu nutsuwar da zai yi aiki, kuma ina ma yasan Haj Hudah da har zata bashi aiki, lalle akwai matsala “. Haj kilishi ta numfasa tace “Abinda nake kokarin fahimtar da ke kenan jiya akwai matsala sosai, komai fa ya canja, ina zai santa fa da ya wuce wajen bangar siyasarsa da nake murnar karshen lalacewa ce ta same shi, sai gashi a dalilin hakan zai samu azurta”