Musabbabi Book 1

Page 188

by @yargidanimam

Haj Rakiya tace “Gaskiya Haj akwai damuwa “ Haj kilishi tace “Damuwa kuwa sosai, saboda ni ko ya ya ne bana bukatar ya samu ko wace irin dama na fi son ya cigaba da lalacewa har karshen rayuwarsa , don haka nake tsoron kada aikin nan ya lalace”, Haj Rakiya ta jinjina kai tace “ Amma ke kina ganin wannan tunaninsa ne kuwa?”, Haj kilishi ta kara feso da numfashin damuwa tace “Ni kaina ban yarda wannan tunaninsa bane, don ina wani tunani ga me shaye-shaye, na dai fi Yarda da cewan wannan tunanin makirar matarsa ne Afrah, don baki ga yadda ta shigo min falo ba yanzu da gadara da isa, anya ma kuwa yarinyar nan bata gano wani abu a game da ni ba”, haj Rakiya tace “ me ki ka gani ya saki wannan tunanin”, ta nisa tana kara nazarin yadda ta ga Afrah yau, tace “ Yadda take tsorona da shakkata yau babu komai a cikin idanunta face tana min wani irin kallo da har yanzu ban fahimci ma’anarsa ba”.

Haj Rakiya tace “Idan ko wannan ne tunaninki to ya zama dole mu san matakin da zamu dauka a kanta” Haj kilishi ta mike tsaye ta shiga shawagi a tsakiyar falon, ta yi sa’a babu kowa a gidan masu aikinta biyu ta aike su, don haka ta sake sosai su ka cigaba da tattauna yadda za’a bulloma lamarin. Tace “kin fahimci cewa wannan samun aikin nasa zai iya rushe duk abinda muka kulla a kansa, kinga idan yana aiki yaushe zai sami damar cigaba da yawo da abokansa na banza, yaushe zai sami damar yin shaye shaye yadda yakamata?,haka zalika yin aikin nasa zai iya sawa wasu su ga darajarsa wanda kinsan abinda na tsana kenan duk duniya,sannan idan ya fara aiki zai dinga mu’amala da mutanen kirki, maimakon mutanen banza, tunda ga Shi da mata ga aikin yi, kuma Hajiya me ya rage a cikin cikar natsuwarsa?" Haj Rakiya ta girgiza kai tace “Babu, gaskiya wannan abu bai yi dadì ba, dole kuma a dauki mataki." Haj kilishi tace "'Mataki ya wuce na raba shi da wannan matar ta sa, domin duk ita ce silar komai Don haka dole mu je wajen boka Mai Rakwacam, don na sanar da shi halin da nake ciki, ni fa kin ganni nan rabon da nayi bacci me dadi harna manta a rayuwata kullum cikin fargabar kada a sami matsala nake”. Haj Rakiya tace “ Hakan shine dai dai sai mu je saboda kada ki tsaya garin kallon ruwa, don dai dawowar musaddik hayyacinsa matsala ce gagaruma, don Zai iya waiwayar dukiyarsa, duk da ya riga ya bayar, zai iya kalubalantar ki, kuma mafarkinki na musaddik ya kare rayuwarsa a wulakance bazai taba tabbata ba”, Haj kilishi tace “shine damuwata, bari zan gyara musu zama daga shi har matar tasa, ki shirya gobe zamu tafi ruga”, tace “Allah ya kaimu”, daganan su ka yi sallama, lokaci daya su ka aje wayoyin.