Musabbabi Book 1

Page 189

by @yargidanimam

Lalle wanda Allah dai ya batar ya batar domin dai duk wanda ya rike wanin Allah Tabbas! Ya tabe.Haj Kilishi tana cikin hallaka, tunda ta maida boka Mai Rakwacam me biyan bukatunta, ta manta duk wanda ya je gidan boka, Ya gaya masa bai yarda ba, bai Kuma yi amfani da abinda ya fadan ba, to Allah ba zai taba karbar sallarsa ba ta tsawon kwanaki arba' in, kuma yana fushi da mutum. Idan kuma bokan ya gaya masa ya ji ya yarda ya kuma yi amfani da abinda ya fadan ya amince, to mutum ya kafirce da ga abinda Allah ya aiko manzonsa, ka yi shirka, ka fita musulunci, duk wani aikin kwarai da ka taba yi, ya goge amma duk zunuban mutum suna nan, Hmm! Jama 'a wannan wace irin masifa ce ? Saboda son duniya ka rabu da Allah da Manzonsa. Bayan ka san cewa Allah me tsananin Kishi ne, yana yafe kowane irin zunubi matukar tsakaninka da shi ne amma banda shirka, matukar mutum ya mutu yana shirka babu in da zai je, sai wuta, da shiga azaba dauwamammiya, me zai sa ka zabi duniya abinda ba dauwamamme ba, akan lahirarka wanda ya ke dauwamamme?. Me ya sa ba za mu hanu da abinda Allah ya hanemu ba? Meye duniyar balle abinda ke cikinta,Mu da mutuwa take gabannu,da kwanciyar kabari meye namu na son duniya har ya ja mu kaucewa hanyar Allah. Amma lalle irinsu Haj kilishi sun riga sunyi nisa babu Allah a zuciyarsu, idonsu rufe yake da son duniya, zuciyarta kuma cike take taf da tsanar dan kishiya wanda da ta kwantar da hankalinta sai tafi amfana da shi fiye da kowa, da ta rike shi a matsayin da, da bata kara kukan rashin da namiji da bata haifa ba, yadda ya taso baisan mahaifiyarsa ba hakika da itace zata maye gurbinta a gurinsa, amma zuciyarta ta kekashe ta manta da komai sai yadda zata sabauta rayuwarsa.