Page 190
Ko yanzu kwata kwata bata samu sukuni ba duk ta fita hayyacinta, haka ta uni a cikin gidan tamkar mara lafiya ko ya ya ta ji an taba get sai ta leko, ta kosa kwarai gobe ta yi ta tafi ruga domin ba zata yarda Aftah ta cigaba da dagula mata lissafi ba.
Ita kam Aftah yau duk addu’ar ta akan musaddik ta kare, Hakan yasa a ranarsa ta farko a wajen aiki bai fuskanci wata matsala ba, banda matsalar kallon da Alh yisuf sanda yake masa wanda ya ji a ransa tamkar dabi’ar sa ce ta yin irin kallon, amma me yasa ba ya irin kallon akan kowa sai akansa. Musamman da Haj Hudah ta fito cikin tsararriyar kwalliyarta cikin wani babban leshi da ya ji duwatsu doguwar riga ce irin dinkin manyan mata ne tunda tana da jiki, sai dai dan gyalen da ta makala a kafadarta sam bai dace da ita ba a matsayinta na matar aure. Musaddik ya yi mamakin yadda Alh yusuf bai damu da ya tsawata ma matarsa kan irin wannan shigar ba maimakon hakama yafi maida hankalin sa akan kafesu da wannan tsinannen kallon da ya saba, yana tsaye yana kallonsu har suka shiga mota ɗaya da Musaddik sai direba, ɗaya motar kuma Jami’an tsaronta ne suka wuce suka tafi, Lamarin ya daure kan musaddik har suka kai inda zasu cike yake da mamakin waye Alh yusuf sanda ne?.
Gidan gaisuwa su ka je Haj Hudah tayi gaisuwa gami da bada kudin da zasu cigaba da ciyar da kansu zuwa wani lokaci, siyasa riya ce domin komai ta yi yan jarida na gefe su na dauka domin su yaɗata, Musaddik dai yadan sami damar kewayawa yadan bushi sigarinsa ya fito da dan karamin turare bayan ya gama ya goga a hannunsa da jikinsa sannan ya dawo cikin mota, hakanan ya ji baya son halinsa na shaye shaye ya fito a wajen Haj Hudah hakanan ya ji yana son rike mutuncin da ya fahimci Haj Hudah ta na ganinsa da shi. Bayan ta gama abinda ya kawo su ne suka bar gidan. Wajen cin abinci suka wuce sun ci abincinsu mai rai da lafiya tebur daya suka zauna da Musaddik duk da baiso hakan ba amma ta dage akan babu komai. Suna cikin cin abincin ne musaddik yaga wannan wata damace agare shi da zai gaya mata gaskiya, ya dago ya dan dubeta fuskarta cike da nishadi ya maida kansa kan abincinsa yace “Ranki ya dade ina son na danyi wata magana da ke dafatan ba zata bata miki rai ba”, ta aje wukar hannunta tana kallonsa wani irin shauki yana kamata tace “ babu damuwa Musaddik menene?” Ya dan gyara zamansa yace "Ranki ya dade a matsayin ki na matar aure wacce akwai abubuwa da dama da yin su haramun ne a gare ki,ina ganin yakamata ki dinga suturce kanki a duk lokacin da zaki fita, sanya irin wannan mayafin bai kamata ba wannan caba kwalliyar itama sam bata kamata ba, kiyi hakuri fa tunatarwa ce kawai nayi miki”, wani irin dadi taji har cikin ranta ta zuba masa ido yau itace rana ta farko da aka gaya mata wannan maganar me tsada ko mijinta bai taba kishin fitarta a haka ba shi ne ma wata rana yake nuna mata dan gyalen da zata yafa ta fita, lalle Musaddik komai nasa da ban ne.
Shurun da ta yi ne ya dauka ko taji zafin maganarsa ne hakan yasa ya yi saurin cewa “ kiyi hakuri, na saba ganin matata bata fita saita suturce kanta tun daga sama har kasa hatta fuskarta da bata cikin al’aurar mace saita rufeta shi yasa a duk lokacin da naga wasu matan musamman na aure suna banzantar da kansu nake cika da mamaki da damuwa, don Allah kada ki ji haushi”. Tayi murmushi sosai tace "waye ya gaya maka na ji haushi, burge ni kawai kayi yadda banyi maka kwarjini ba baka ji tsoron matsayina ba ka gaya min gaskiya nagode nagode domin kayi min abinda ya kara daga darajarka a guna in sha Allah kuma zan gyara”. Ya yi murmushi yace “ To masha Allah ubangiji Allah ya bada ikon gyarawa”. Kamar daga sama haj hudah ta watso masa tambayar "Amma dai kana son matar nan ta ka da yawa”. Ya aje cokalin gami da ture farantin abincin gabansa, ya yi wani murmushi da ya ƙara narkar da zuciyar Haj Hudah sannan yace “Ina sonta Haj fiye da yadda nake son kaina, ina jinta a cikin jinin jikina ba a zuciyata ba, yanzu haka wannan abincin da nake ci baya min daɗi saboda nasan ba irinsa zata samu ta ci ba yau, ina sonta tamkar yadda nake so koma fiye da yadda nake son numfashin da ke bugawa a kirjina”.
Dauke wuta Haj Hudah ta yi ta kara zuba masa ido tana jin jikinta yana tsuma, tana jin wani irin damuwa a cikin zuciyarta da bata san dalili ba, nan da nan idanunta suka canja………
Yar gidan imam ✍️ MUSABBABI
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM