Musabbabi Book 1

page 191

by @yargidanimam

Musaddik bai fahimci komai ba hakan yasa ya cigaba da yabon matarsa, har sai da zuciyar Haj Hudah ta ji ba zata iya dauka ba, don haka tayi saurin mikewa ba tare da tace uffan ba, ta dube shi cikin rawar murya tace “Tashi mu tafi”, bata saurari komai ba ta wuce ayayinda musaddik ya bita da kallo, canjin yanayin da ya gani a tattare da ita sam bai sa ma kansa komai ba. Ya tashi ya bi bayanta.Har suka kai gida zuciyar Haj Hudah tafasa take, shin me yasa take jin zafi don musaddik ya gaya mata yana son matarsa?,me yasa take jin damuwa don musaddik ya yabi matarsa?. Ko da suka isa gida bata saurari komai ba ta shige cikin gida, musaddik kuwa zamansa ya yi a waje cikin mutanen da ya samu a harabar gidan. Da alama Alh yusuf sanda baya gidan, karfe shida dai dai na yamma musaddik ya kama hanyar gida ba tare da ya damu da ya yi sallama da Haj Hudah ba kamar yadda itama bata bukaci ganinsa ba, ikon Allah.

Washegari kuwa tun safe Haj kilishi da Haj Rakiya suka dauki hanyar rugar boka mai rakwacam, wanda har suka Ka rugar, la'antar Musaddik take tare da la’antar rayuwarsa, kamar ko yaushe idan suka je gaban me Rakwacam Haj kilishi tana cikin kaskantar da kai a gabansa, wannan karon ma tana zaune a gabansa cikin nutsuwa tamkar me daukar karatu, ta gama sanar da shi duk abinda ke damunta, ta kara da cewa “Bana son alakar auren da ke tsakaninsu, shi yasa nake son araba su rabuwa ta har abada, shi kuma musaddik a raba shi da duk wani mutum da zai zama alheri a tare da shi,sannan ina son shaye shayen da yake ya fi na da”.

Boka me Rakwacam ya gyada kai ya dakko kayan surkullensa ya buga katon faifan dake gabansa, ga mamakinsu kawai saiga fuskar Afrah ta bayyana, cikin shiga ta kamala tana zaune kan sallaya rike da casbi a hannunta. Boka me Rakwacam ya ja baya hannunsa na rawa lokaci daya fuskar Afrah ta dauke, Haj kilishi da haj Rakiya suka shiga kallon kallo, Boka me Rakwacam ya dago hannunsa daker da ya sage ya dubi Haj kilishi ido cikin ido sannan yace “Haj babu nasara, ki kiyayi wannan yarinyar kawai, domin kamar yadda na gaya miki babu me hana aurenta da musaddik to hakanan zan kara gaya miki yau domin tsakanina da ke babu cin amana, musaddik da Afrah ba zasu taba rabuwa ba sai dai wani iko na Allah sannan wannan yarinyar tana da tsananin addu’a ta na ambaton Allah ko yaushe, matukar kuma tana cikin wannan halin babu abinda zan iya yi mata na cutarwa da zai sameta ko yanzu wannan bayyanar da tayi sai da na sami rauni a hannuna, saboda haka ina baki shawarar ki kiyayeta”. Gaban Haj kilishi ya cigaba da faduwa ta ji komai ya tsaya mata, ta dube shi murya shake tace “yanzu kana nufin babu abinda zaka iya taimaka min dashi”, ya girgiza kai yace “Babu, domin idan ki kayi wasa wannan yarinyar itace silar tunuwar duk asiranki”. Tikisa nan ma haj kilishi dafe kai tayi wata irin damuwa tana kara cika zuciyarta. Lalle Afrah ta zamar mata masifa, ta kara duban shi tace “To shi musaddik din fa?” Ya gyara zama yace “Duk aikin da mu kayi a kansa yana nan sai dai tsananin addu’ar da matarsa take masa yana ta raunata mana aikin, saboda haka abinda kikace ayi masa yanzu zanyi masa, wannan kada ki damu tunda shi bai damu da yin addu’a ba komai zai iya kama shi”, Ananne ta dan ji sanyi kadan a ranta tace “ To a kara yin aiki a kansa, ko bamu sami nasara akanta ba idan muka samu akansa ai an gama da ita tunda koma meye dole zai tabata”. Daganan Boka me Rakwacam ya fadi kudin aikinsa ta kuma cake masa kudin a gabansa harda kari, wata bakar laya ya bata yace tasan yadda zatayi tasa a bakin kofar da tasan dole zai tsallaka to fa da zaran ya tsallaka to zai yi mugun bakin jini awajen duk wanda yake mu’amalar arziki da shi, shaye shaye kuwa da lalacewa tunda tukunyar da suka binne a bakin kuka tana nan a binne to babu abinda zai canja zai cigaba a haka har abada. Ta karbi layar gami da godiya sannan suka bar rugar cikin tashin hankali Afrah ta na neman ta zamar mata dan hakin da ka raina.