Musabbabi Book 1

Page 192

by @yargidanimam

A daren ranar, musaddik ya gama cin abinci, Afrah ta shigo ta zauna kusa da shi sosai tana rike da kofi da ruwan da ta gama tofe Ayatul sihir a ciki ta mika masa tace “yaya ka sha wannan addu’ar da bisimilla”. Ya dubeta cikin murmushi yasa hannu ya karba yace “duk abinda ki kace haka za’a yi zan sha ko da addu’ar mallakeni ne”, tayi dariya sosai tace “Bama akai ga haka ba yaya”, ya sa kofin a bakinsa sai da ya shanye tas sannan ta amshi kofin, zata yi magana kenan wayar musaddik ta dauki kara yasa hannu ya dauka ganin Haj kilishi ce yasa ya yi saurin dauka, “ kazo ka same ni yanzu”, cewar haj kilishi cikin fusata kafin yayi magana harta aje wayar.

Afrah ta dube shi tace “kai da waye na ga yanayin ka ya canja”, ya dan numfasa yana kokarin tashi, yace “Haj ce tace na je yanzu tana son ganina”, ta dan tsare shi da ido tace “To canjin yanayin na menene?”, ya ce “Na ji ta cikin fusata ne a fadace take shi yasa na ji damuwa a raina ina tunanin ko nayi mata laifi ne”. Afrah ta gyada kai tace “Ko ma meye idan laifi kayi mata sai ka bata hakuri” ya juya ya fara tafiya sai kuma ya tsaya ya waigo ya zubama Afrah ido, ta dan daga girarta sama tace “yaya dai?”, ya girgiza kai yace “Naji faduwar gaba ne da tsoro ya cika zuciyata hakanan”. Jikin Afrah ya yi sanyi kalau, ta ja hannunsa gaba daya suka zauna kan kujera tana rike da hannunsa tace a hankali, “zan karanta wata addu’a duk abinda na fada ina son ka maimaita har mu kai karshe”, babu wani musu ya gyada kai. Tace “Bismillahillazi la yadurru ma’asmihi shai’un fil’ardi wala missama’i wahussami’ul aleem”.haka shi ma musaddik ya maimaita, daganan ta dube shi tace “ ka taka duk inda ka so, babu abinda zai sameka kana cikin tsarewar ubangiji”. Ji ya yi ya sami wani irin kwarin guiwa ya mika bakinsa kan hannunta ya sumbaceta yace “madallah da samun mata irinki”. Ya saki hannunta ya tashi ya fice da sauri Afrah ta bishi da addu’a domin dai sosai haj kilishi tuni ta fara bata tsoro.

A kasan kafet din kofar falonta Haj kilishi ta daga ta sa layar da boka me Rakwacam ya bata, wanda tasan babu yadda za’ayi musaddik ya shigo cikin falonta ba tare da ya tsallaka layar ba, dama burinta kenan.

Cikin sallama ya shigo falon idon haj kilishi na kansa har ya tsallako ya shigo sai zuwa lokacin ta ji wata nutsuwa ta shigeta tana ganin asiri ya riga ya kama shi, sai dai abinda bata sani ba Allah ya riga ya tsare shi domin kafarsa kawai da ya tsallake layar tuni ta kora yin bakinkirin fiye da yadda ta karbota a wajen boka. Kan kujera ya zauna yana kokarin gaisheta ita kuma tana karewa natsuwarsa kallo domin yau cikin natsuwa yake , yadda yake shigowa a firgice cikin rashin natsuwa yau sabanin haka ta gani, shi yasa ta ji ranta ya kara sosuwa, “ Haj kin ce kina son ganina” Ta daga ido ta watso masa harara tace “To ai naga ka zama hukuma ne sai lallashi yanzu ka manta matsayina a wajenka har zaka iya yin kwanaki ba tare da ka shigo ka gaishe ni ba, har kuma zaka sami aiki amma ka ki shigowa ka gaya min sai dai matarka ta zo ta gaya min saboda kai kafi karfin ka gaya min ko?” Musaddik ya girgiza kai yace “Duk ba haka bane Haj, abubuwa ne kawai suka zo a bazata amma ta yaya zanfi karfin zuwa na gaya miki na sami aiki”.