Musabbabi Book 1

Page 193

by @yargidanimam

Haj Kilishi ta kara zuba masa harara tace “Babu abinda zaka gaya min, domin batun yau na kula da yadda tunda ka yi aure kake kokarin wofintar da ni, yanzu baka ganin kowa sai matarka”, ya kara girgiza kai yace “ki daina wannan maganar Haj, ki kuma yi hakuri don Allah”, ta saki numfahi tace “shikenan, aikin me ita yar majalisar ta baka?”, ya dan yi murmushi yace “Ba wani aiki bane aikin kula da lafiyarta ta ba ni”, ta sakar masa wani irin sakaran kallo tace “kai kaji wata maganar banza aikin kula da lafiyarta, yanzu kai don lalacewa aikin bautar kula da lafiyar mace zaka zauna kana yi to kwata wannan aikin bai dace da kai ba, wannan ai Wulakanta kai ne. Ka tuna fa Ka yi karatu har Masters gareka, amma za ka kare da yin aikin wanda bai yi karatun komai ba”.

Musaddik ya nisa sannan ya ce, “Maganarki gaskiya ne Hajiya. Amma kada ki damu wannan aikin na dan wani lokaci ne, zan sami wani aikin yanzu haka ma na riga na mika takarduna wajen neman aikin daya dace da karatuna" Gaban Hajiya Kilishi ya yi mummunan faduwa, lalle ta yi sakaci Musaddik yana neman ya dawo Musaddik dinsa na da, lalle auran Afrah da Musaddik babban kalubale ne a gareta ta ya ya ba zata tsani Afrah ba ji tayi kirjinta har wani bugawa yake da karfi, bakincikinta ya kasa boyuwa,yanzu Musaddik har yana da kyakyawan tunanin da zai tsara ma kansa rayuwa ta-gari?har yana da tunanin neman aiki a wajen da ya dace da shi. Ta muskuta daker tace “To ashe har aiki kake nema”, ya yi murmushi yace “sosai kuwa haj sai ki tayani addu’a Allah yasa na samu aikin da yafi wannan”. Bata ce komai ba sai da ta yi kasa da kanta tayi ta kokarin daidaita hankalinta, tana son boyr mugun halin da ta shiga, sannan ta dago tace “Amma dai wannan neman aikin da ka ke yi da kuma wanda ka karba yanzu ka fara, duk tunanin matarka ne ko ba tunaninka ba?”

Ya yi murmushi gami da gyada kai yace, "Eh, tunaninta ne, ai a gaskiya Hajiya na yi sa’ar mata, Afrah tana da hankali ga hangen nesa tunaninta yayi nesa da shekarunta,ina jindadin zama da ita domin a kullum burinta ta maida ni hanya ta-gari,ta maidani mutumin kirki Ita ke tunatar da ni abubuwa da yawa da na manta, mace ce ta-gari". Hajiya Kilishi ta yi murmushin Karfin hali tace “Hmmm lalle kayi sa’a, shi yasa ni baka fahimtar ina cikin damuwa akan halayenta a gare ni, kai tana mutuntaka ni kuma tana kuntata min, sam bata ganin kima ko girma na………. Da sauri ya dakatar da ita yace “Anya Afrah kuwa ina dai ganin kila kin sami kuskuren fahimta ne, domin Afrah ko karami bata raina ba balle babba”. Ta watsa masa harara tace “Ai nasan ba zaka yarda da laifinta ba tunda idonka ya riga ya rufe a kanta, kayi hakuri ba zaka kara jin laifinta a bakina ba”. Ya girgiza kai yace “Don Allah kiyi hakuri ba na nufin hakan kawai dai gaskiya ce na fada” ta daga masa hannu tace “ya isa, tashi ka tafi Allah ya tashemu lafiya. Shi ma tuni zaman dama ya gundure shi hakan yasa ya yi gaggawar tashi ya yi mata sai da safe, duk da bata amsa ba bai damu ba ya fice a binsa. Yana fita haj kilishi ta tashi da sauri ta dage kafet din ta fito da layar, yadda ta ga ta kara yin baki kamar an konata yasa taji ta aminta a ranta asirin ya riga ya gama kama musaddik.