Page 194
Tayi wani murmushi ta wuce cikin daki ta adana layar, sannan ta shiga kai gauro da mari a tsakiyar dakin har Yanzu zuciyarta a zafafe take,yadda musaddik ke yabon Afrah kadai ya isa yau ya hana mata samun bacci, ta tsaneta fiye da yadda ake tsammani, shin ta yaya zata yi maganinta, bayan boka me Rakwacam ya nuna shi ma ta fi karfinsa, lalle wannan yarinyar ta zamar mata karfen kafa.
Zahiri ta kara shiga damuwa domin ko da ta kwanta ta kasa bacci sai juye juye kawai take yi, babu wani abu daya da ke yi mata dadi a cikin rayuwarta, da kudi tana neman yadda zata sami farinciki amma ta rasa. Bata jin kuma zata hakura kamar yadda boka me Rakwacam ya bata shawara. Wasgegari Haj kilishi ta kira abokiyar sharrinta haj Rakiya, ta sanar da ita musaddik ya tsallaka laya don haka tana da yakinin aiki ya ci, sai dai kuma maganar Afarah matukar zata cigaba da sa mata ido to zata bata mata duk wani shiri da ta dauki shekaru tana yi, haj Rakiya ta yi kasa da murya tace “To kece ai haj kullum kina ganin idan ba wajen me Rakwacam ba babu inda zaki samu biyan bukata bayan akwai manyan bokaye da ni na sani da zasu iya yin abinda me Rakwacam bazai yi ba, su da suke tsafi”, Haj kilishi ta jinjina kai tace “yanzu kina ganin mu cigaba da bin wasu bokayen kina ganin babu asarar kudi irin na wancan lokacin”, cikin karfafa guiwa Haj Rakiya tace “za’a dace saboda inda zan kai ki shi ma fa ya iya aiki, ayyuka nawa ya yi min na samu nasara na kai wasu ma suma sun dace, kawai ki manta da wani Afrah ta fi karfin me Rakwacam don idan tafi karfinsa bata fi karfin wasu ba, don gaba da gabanta”. Nan da nan Haj kilishi ta ji ta aminta da ta je wajen wani bokan bayan me Rakwacam duk da dai da ta ce ta daina asarar kudinta a wajen kowa bayan me Rakwacam, sun kuma tsaida magana akan haj Rakiya zata rakata wani kauye dake can bayan gari wajen wani hatsabibin bokan. Kai duniya anya kuwa akwai wahalalle irin me bin bokaye, duk rayuwar mutum ta kare a asarar lokaci da imani da kuma rasa kwanciyar hankali da sukunin rayuwa, yanzu meye amfanin rayuwar Haj kilishi da duk daular da take ciki da bokayen da take bi bacci ba zata iya yi me dadi ba, to ina sauran dadin rayuwa. Aiki ya sami me yi domin dai a ranar karfe daya da kwata na rana, Haj kilishi da Haj Rakiya suka dauki hanyar wani kauye da ke nesa da minna, Haj kilishin ce ke tuka mota, kamar yadda ta saba tukawa a duk sanda zasu je wajen bokayensu, bata daukar direba saboda sirri.sai da su kayi tafiya me nisa karshe ma aje motar su kayi a bakin hanya suka karasa a kafa saboda mota ba zata shiga wajen ba. Tsiduhu ya karbesu hannu bibbiyu, Haj kilishi kuwa bata sami nutsuwa ba da jin ta zo inda yakamata saida Tsiduhu ya fara gaya mata abinda ya kawota wajensa, yadda yake bayanin komai kai ka rantse da Allah a gabansa akayi komai, zuciyar Haj kilishi ta kara yin sanyi a lokacin da Tsihudu ya tabbatar mata zai iya raba musaddik da Afrah zai kuma iya sabauta rayuwarta ma gaba daya, sai dai akwai tsada aikin. Haj kilishi tace “in dai za’a sami biyan bukata ko nawa ne zata iya biya”, haj Rakiya ta dubeta da sauri tace “Haba Haj yanzu har wani shakku zaki sa a ranki a wannan aikin, kina ganin yadda da zuwan mu ya fadi duk damuwarki ai ki cire shakku kawai”, tace “Ai na cire Haj lalle kin kawo ni inda ya dace”. Tsiduhu yace “zaki bada nera dubu dari hudu kudin sayen kayan aiki”, babu musu ba neman ragi tace “Babu damuwa”, katuwar jakarta ta dakko ta bude ta kirgo bandir hudu na yan dubu dubu ta aje a gabansa, baiko dubi kudin ba yace “ ku tashi ku tafi ku dauka komai ya yi dai dai ku dawo nan da kwana shida zan baki mahadin aikin”