Page 195
Cikin godiya suka tashi suka tafi, har suka kai bakin motar Haj Rakiya kara yabon aikin Tsiduhu take yi, tana karfafa aikin nasa. Hakan yasa Haj kilishi ta kara jin ta aminta da aikin nasa Afrah kam sai dai wata ba ita ba zata gane ta shigo gonarta, za kuma tasan tayi kuskuren auren musaddik domin babu komai a cikin auren nasa face masifa. Har ta aje Haj Rakiya a kofar gidanta tana mata godiya, domin dai ita din aminiya ce ta rufin asiri. Motar Haj kilishi na bacema ganin Haj Rakiya, ta juya ta shiga cikin gida tana murmushi, fuska cike da jindadi, dama ba wani damuwa ta yi da yin sallah ba ko zatayi ta fi yinta ba’a kan lokaci ba, hakan yasa dan abinda zata ci kawai ta sarrafa me sauki ta ci ta koshi ta dan huta, tasan megidanta sai dare zai dawo gida don haka ta tashi ta canja gyale ta fito ta kara kulle gidanta ta nufi bakin titi. Shatar taxi tayi zuwa kauyen da suka baro dazu,cikin kankanin lokaci suka iso inda dole zai tsaya, ta fito ta sanar da shi ya jirata yanzu zata dawo. Sannu a hankali tayi ta tafiya har ta kawo inda Tsiduhu yake, ta tura kofar galangalan din a hankali tana kiran sunan sa, Tsiduhu ya juyo suka hada ido gaba daya suka fashe da dariya harda kyakyatawa, “zauna”, cewar Tsiduhu cikin dariya, ta lalubi gefen tabarmar ta zauna tana cigaba da dariya tace “Amma fa kayi kokari, duk abinda ka fada ya zauna a zuciyarta sosai”, ya nisa yace “kai mata na zuba rashin imani akan yan’uwansu mata, yanzu ita wannan Afrah irin wannan mugun abun da take son ayi mata ina zata kai girman hakkinta idan anyi”. Haj Rakiya ta tabe baki tace “Ina ganin mata marasa imani ciki kuwa har da ni amma ban taba ganin irin haj kilishi ba, yaron nan duk abinda take son a maida rayuwarsa an maida ya zama abin tausayi amma ta kasa hakura, Afrah kuwa bokanta da kansa ya gaya mata ta kiyayeta, a gaban mu shi ma sai da ya wahala alokacin da ya yi kokarin cutar da ita, amma duk bata samu ta yi tunanin lokaci ya fara kure mata ba, shi yasa nayi amfani da wannan damar mu yagi rabonmu kafin ta gama samun matsala”. Tsiduhu ya yi dariya yace “Ai kin gama min komai rabon da naga dubu daya tawa har na manta lalle kin kawo min babbar harka, zamu cigaba da tazarta idan kura na maganin zawo tayi ma kanta mana duk bokan da yake mata aikin ai sabida kudi yake yi mata to me yasa shi bazai azurta kansa ba kawai ya huta da sai yayi aiki an biya shi”. Gaba daya suka fashe da dariya, Haj Rakiya tace “Dakko kudi mu yi kasafi na tafi nabar me mota yana jirana”. Da sauri ya janyo ledar da ya zuba kudin ya mika mata, ta amsa ta dauki dubu dari biyu da hamsin ta mika masa dubu dari da hamsin ya amsa cike da murna ji yake kamar yafi kowa kudi a duniya, lalle Haj Rakiya saninta alheri ne. Daganan su kayi sallama akan sai nan da kwana shida zasu dawo kamar yadda yace. Kai tsaye daga nan wajen me taxi dinta ta wuce zuciyarta fes da farinciki gobe kaji zata bararraka ta ci abinta ta kuma biya yan basussukan da ake binta, cin kudin Haj kilishi yanzu ta fara tunda ta fahimci babu burbushin imani a tare da ita, dama kuma irin wannan rayuwar da haduwa ta bariki ai babu amana a ciki……….
Yar gidan imam ✍️ Musabbabi
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM