Page 196
Alh yusuf sanda dai ya tattara ya tafi paris, domin shigo da wasu kaya.Haj Hudah kuwa tun bayan rantsar da ita har yanzu ta ki komawa gidanta da aka mallaka mata a Abuja sai dai duk bayan wasu yan kwanaki tana shiga Abujar, kuma ba kasafai take kwana ba a duk lokacin da ta je din, domin hakanan take jin rashin jindadi a duk ranar da zata kwana a Abuja kasancewar in dai kwana zata yi musaddik ba ya biyota sai dai idan ta dawo ya zo. Dalilin da yasa kenan bata son kwana a Abuja sai ya zama dole,Tana jin kamar ta yi matukar wauta da ta sabama idanunta ganin musaddik kullum, domin hakan na nema ya zamar mata wata illa bata san abinda zuciyarta ke nufi ba da sanya musaddik a cikin tunaninta, musamman idan ta zo kwanciya, ta kan ji bacci ya kauracewa idanunta, abin mamaki kuma bata yin tunanin kowa sai musaddik, abin takaici kuma sai zuciyarta ta yi ta bijiro mata da tunanin yana can tare da matarsa yana jindadi hakanan sai ta ji wani irin abu me kama da kishi ya tokare kahon zuciyarta, tana jin kishin matar musaddik sosai shin meye dalili?, ita kanta kai tsaye ba zata iya cewa ga dalili ba, amma wannan abin yana matukar damun zuciyarta ta kuma rasa inda zata bulloma lamarin.
Ta bangaren Haj kilishi kuwa ta kafa ta tsare ta ji Haj Hudah ta kori musaddik daga aiki amma shuru, domin dai kullum tana jin fitarsa zuwa wajen aiki da dawowarsa, ta dan ba da lokaci ta gani domin a ranta tabbas tana jin aikin boka me Rakwacam ya ci sai dai jiran lokaci kawai. Haka zalika kwanaki shidan da Tsiduhu ya dibar musu ya yi, don haka suka koma kamar yadda ya bukata, wanda kafin komawar tasu tuni Haj Rakiya ta kira shi ta bashi labarin duk abinda ke faruwa, hakan yasa da suka koma ya shiga gayama Haj kilishi tana cikin damuwa,akan aikin da ta kaima wani bokanta tana jiran taga aiki ya ci amma har yanzu ta ji shuru.