Musabbabi Book 1

Page 197

by @yargidanimam

Cikin dimbin mamaki ta dube shi tace “Tabbas hakane, kuma bai saba min aiki na dauki wani lokaci banga ya ci ba sai wannan”, Tsiduhu yayi dariya yace “Ai saboda bai ci ba ne aikin shi yasa ki ka ga sabanin tunaninki”, Haj Rakiya ta gyara zama a cikin zuciyarta ta na yaba yadda Tsiduhu ke tafiyar da komai. Haj kilishi ta bata fuska tace “Ko da ba ji kace aikin bai ci ba”, ya gyada kai yace “kwaraibkuwa, ko da yake wannan ba damuwa ta bace, ungo nan”, ya mika mata wani kullin magani da wata laya da aka daureta tsaf da allurai. Da sauri ta amsa tana juyawa alamar neman karin bayani, Ya kara kallonta sosai yace “wannan kullin maganin duk yadda zaayi ki yi kisa mata a cikin abinda zata ci, kadan zaki barbada mata idan kika cika zata iya mutuwa, ita kuma wannan layar ki sami ruwan teku me gudana ki jefa a ciki , in dai kin bi yadda nace to shikenan rabuwar Afrah da musaddik ta tabbata, za kuma ta cigaba da rayuwar kunci.

Tayi murmushi tace “Nagode”, Haj Rakiya ta matso sosai kusa da kunnanta tace “Tunda yace wancan asirin da me Rakwacam ya yi bai ci ba, basai ki sa shi ya kara yi miki wani ba, tunda naga aikin nasa akwai nasara a ciki”, nan da nan ko Haj kilishi ta gyara zamanta ta kwantar da kai kamar wacce za’a ba kyautar duniya tace “Sai maganar wancan aikin da kace bai ci ba, wane taimako zan sanu ta bangarenka”.

Yace yana wani zazzaro ido kamar tsohon maye, “Duk abinda ki ke so zaki samu, ba so ki ke a raba shi da duk wanda za suyi huldar arziki ba, asa bakin jini a gare shi, sannan ya dauwama a shaye shaye”, sakwake tayi gaskiya Tsiduhu yana daya daga cikin bokayen da ta sani wanda suke da abin al’ajabi da yawa, ka duba yadda yake fadin abinda ke cikin zuciyarta kamar yana karantawa, duk abinda akayi a bayan idonsa ya sani zai kuma iya fada Ta aje numfashi a gaggauce tace “Abinda nake bukata kenan”, yace “To kin samu Haj ki kwantar da hankalinki kawai ki biya nayi miki aiki”, Ta gyara zama tace “Nawa ne?” Yace “wannan aikin ai mai sauki ne don haka bazai ci kudi kamar wannan ba, nera dubu dari biyu kawai da ashirin zaki bada ni ma kuma bayarwa zanyi aje a samo kayan aiki, domin babu abinda zan baki ni da kaina zanyi aikin ke kuma za kiga biyan bukata”. Ta yi murmushi tace “To babu damuwa, yanzu ban taho da kudi ba ga dai wanban”, ta bude jaka ta mika masa dubu dari tace “sauran dari da ashirin din kuma zan ba Haj Rakiya zata dawo ko zuwa gobe ne ta kawo maka”. Ya gyada kai kamar tsohon kadangare yace “Babu damuwa”. Daganan su ka yi masa sallama suka dauki hanya, Haj kilishi na cigaba da kakabin yadda Tsiduhu yasan komai har tana ma ji a ranta cewa yafi Me Rakwacam iyawa ya fi shi kuma hatsabibanci. Tun a motar Haj kilishi ta dubi Haj Rakiya tace, “yanzu ina zamu samu kogi da ruwa ke gudana”,Haj Rakiya ta yi murmushi tace “lalle Haj abubuwa sun yi ma kanki yawa, in banda haka ace har kin manta da kogin can yamma da gari kogin da muka jefa abubuwan da ba su da adadi, ko akan marigayi Alhajinki abu nawa muka je mu ka jefa”.