Page 198
Haj kilishi ta yi dariya sosai ta miko hannunta daya suka tafa, tace “Allah ya bar min aminiyata na rantse sai yanzu na tuna, lalle abubuwan da ke kan nan nawa suna da yawa musaddik da Afrah suna neman su haukata ni”. Haj Rakiya tayi dariya tace “Kada ki damu Haj ai kin dade kina wahala don haka lokacin hutunki ya zo da ikon Allah”, ta yi murmushi tace “Nagode da gudunmawarki bazan taba mantawa da ke ba a tarihin rayuwata”, Haj Rakiya tayi dariya tace “Haba Haj ai amana daya take, ke din aiba kashin yarwa bace meye baki min ba”, tace “Duk abinda na miki tabbas kin cancanta ne”.
Haka suka cigaba da tattaunawa, daga bisani kai tsaye Haj kilishi ta wuce inda kogin yake, bayan sun isa bakin ruwan babu kowa da kanta Haj kilishi ta jefa layar cike da farinciki tana jin aranta Afrah ta gama yawo. Ita kuma Haj Rakiya babu abinda take acikin zuciyarta sai dariya tare da daukar Haj kilishi wahalalliya wacce batasan inda rayuwa ta dosa ba. Daga nan kai tsaye gidan Haj kilishi suka wuce. Ta yi ta hon, sai da aka dauki lokaci sannan Baba maigadi ya bude get din da sauri, cike da fusata ta shiga tana tsaida motar ta balle kofar motar ta fito rai a bace tana yi ma Baba maigadi wani irin kallo na wulakanci sannan tace “wane irin wulakanci ne wannan ina ta hon amma saida kaga dama sannan ka bude saboda baka dauke ni da muhimmanci ba”, Baba maigadi ya yi kasa da kansa yana neman afuwa yana gaya mata dalilin jinkirin da ya yi wanda baya wuce yana bandaki yana kama ruwa, amma duk da haka, haka ta cigaba da fada dai dai lokacin Afrah ta fito daga bangarenta rike da wata cooler abinci me kyau daya hannun rike da lemon roba.
Dif Haj kilishi tayi gaba daya daga ita har Haj Rakiya kallo suka bi Afrah da shi ita kam bata damu da kallon ba illama yi da tayi kamar bata gansu a tsayen ba. Cike da fara’a ta mikama Baba maigadi cooler abincin da lemon tace “Baba ga abincinka”, cikin farinciki ya mika hannu ya karba yace “sannu da kokari Afrah Allah ya yi miki albarka Allah ya tsare ki daga dukkan sharri”, cikin jindadin addu’ar ta amsa da amin, lokaci daya ta juya zata koma, sannan ta dan dubi gefen da su Haj kilishi suke tsaye a ciki tace “sannunku Haj”. Bata damu da rashin amsawar su ba ta shige bangarenta.
Haj kilishi ta watsama Baba maigadi harara a fusace ba tare da tace uffan ba ta wuce cikin gida Haj Rakiya na binta a baya. Cikin bakinciki ta fada kan kujera ta na maida numfashi tamkar wacce ta shiga gasar gudu, Haj Rakiya ta zauna tana kallon ta tace “Eh lalle Haj kya kara shiga damuwa, yanzu alfarmar musaddik har ta kai su dinga kyautar abunci harda lemo, bayan da abinda zasu ci ma ba su da hanyarsa”, Haj kilishi ta yunkuro ta zauna sosai tace “Gara da ki ka gani da idonki, me yasa na kara shiga tashin hankali, duk a rayuwata cigaban musaddik nake adawa da shi, gashi kuma a idona ina ganin cigaban nasa, wannan samun aiki da wannan auren nasa masifa ne a tare da ni, na rantse bazan hakura ba sai nayi fito na fito da su duka”. Haj Rakiya ta numfasa tace “Gaskiya sai kin kara tashi tsaye kada wankin hula ya kaiki dare, amma ni nasan Tsiduhu zaiyi miki duk abinda ki ke so”. Haj kilishi ta mike ta shiga daki tana fadin “Ni ma naji ajikina za’a dace da aikin nasa”, tana shiga daki Haj Rakiya ta yi mata gwalo gami da murmushi. Bata dade ba ta fito da kudi ta mika mata tace “Ga cikon kudin Tsiduhu gobe ki yi kokari ki je ki kai masa”, ta amsa sannan ta kara mika mata wani kudin tace “ga dubu talatin nan sai kiyi shatar mota ki je nagode sosai Allah yabar zumunci”. Ta amsa gami da godiya, nan ta zauna suka cigaba da yi ma juna hudubar shaidan, nan ta ci abinci ta huta, daga bisani tayi gida cike da farinciki, duk duniya ba taga busness din da zata yi ta dinga samun irin wadannan manyan kudaden irin wannan busness din da ta fara, shin me yasa tuntuni bata yi tunanin yin wannan harkar ba da tuni Allah kadai yasan irin dukiyar da ta tara, domin irin kudaden da Haj kilishi ta ba bokaye sun isa mutum ya zama me kudin kansa. Haj Rakiya ta kira Tsiduhu a waya tace ya rike dubu darin ita kuma zata rike dubu dari da ashirin din, godiya ya yi mata sosai, tare da fatan samun wasu kudin nan kusa.