Page 199
Afrah dai ta dage wajen inganta rayuwar mijinta, bata barin kayansa da datti ita ke wankewa ta kuma goge, wani abin sha’awa sai gashi da kansa zai hada kayan wankin nasa ya kuma hada da na Afran ya je ya kai wanki da guga. Da ya sami kudi kuma zai je ya kai ya dakko, zuciyar Afrah tana cika da farinciki idan taga haka, dama kuma abinda yake so kenan wato farincikin Afrah.Duk asubar duniya sai ta tashi musaddik sunyi sallah sannan sunyi azkar tare bata taba yarda ya fita gida ba tare da ya yi azkar ba, ta kuma sa shi ya yi mata alkawarin yin sallah a duk inda yake in dai lokacin sallah ya yi to ya tsaya ya yi sallah, domin tana da yakinin matukar ya rike sallah to zai nisanta da duk wani sabon Allah. A kullum Afrah tana cikin yi ma Allah godiya domin tana ganin cigaba, domin dai soyayyarta da ta cika zuciyar musaddik dole yasa yake kiyayar duk wani abu da yasan zai iya sosa zuciyarta, domin dai sosai yake jin damuwar da tafi ta ta zafi a duk lokacin da ya bata mata, ya wayi gari da soyayyar Afrah me tsanani wanda har ji yake kamar ba shi ba, duk inda yake cikin tunaninta yake, Ya kuma daukar ma kansa iya lokacin da zai dauka bai dawo gida ba bazai taba shigowa hannu biyu ba sai ya sayo mata wani abu da zata ci ko zata sha don kawai ya faranta ranta. Ba wai musaddik ya daina shaye shaye bane a’a yana yi amma ba kamar da ba komai ya yi baya, domin rabonsa da yasha wani abu ya bugu ya fita hayyacinsa shi kansa ya daina kirga kwanakin, yana sha amma ya rage sosai, sannan kuma baida wani lokacin zama wajen abokan banzansa domin bai zuwa har sai ya tashi aiki karfe shida idan yaje ya kan kai takwas a wajen daganan zai tashi ya taho gida, bayan sun gama shaye shayensu sai dai su kansu abokan nasa suna mamakin wannan canjin nasa, sanin a da yafi su shan komai amma yanzu sun fi shi don sau tari wani zubin ma sai dai yadan zuki daya biyu ya tashi. Wani kuma abin burgewa a duk lokacin da ya sami lokaci ya kan je ya gaida mallam Mahmud da Inna Halima, yadda yakan je gidan inna Halima a hargitse yanzu fes zaka gan shi, hakan yasa Inna Halima bata ko gajiya da kallonsa ta sa ma Afrah albarka bata san iyaka ba. Gidan mallam Mahmud kuwa in dai yaje haka Mama Hauwa ke tsare shi da kallo zuciyarta cike da mamakin irin canjawar da ya ke ta yi, tunda ya sami aikin nan komai ya ke masa kyau, abin dake kara girgiza zuciyarta shine yadda wani lokacin da har kudi yake ba mallam mahmud, shi kuma a ranar duk abinda ya fita ya sayo na amfanin gidan ya dinga cewa “ Da kudin da musaddik ya bani na sayo”, wannan kalmar kamar ta fasa zuciyar Mama Hauwa take ji. Damuwa ta fara cika zuciyar Mama Hauwa, ko kadan bata son rayuwarsa ta baya ta dawo ba don komai ba sai don tafi son Afrah ta dauwama cikin matsala, bata son ta jidadin zaman aure ko kadan, domin tasan duk duniya babu wata masifa sama da ace mace ba tayi dacen gidan miji ba. Ga abinda ke kara dugunzuma zuciyarta shine yadda har yanzu Na’ima bata samu miji ba, babu wanda ke zuwa wajen ta da sunan soyayya, duk da kullum ta na yawon bikin kawaye, amma ita har yanzu bata dace ba,duk da itace gaba da Afrah amma ga Afrah can a dakin miji ita kuwa ko mashinshini babu har yanzu sai kace wacce akayi ma kauri da jaba.