Musabbabi Book 1

Page 200

by @yargidanimam

A ranar kuwa da Musaddik ya fara daukar albashi. Tun rana ya tashi aiki bayan ya dauki izini wajen Haj Hudah tunda babu inda za su ranar, zaune yake kawai Haj Hudah na aikin kallonsa, sai kace tsohuwar mayya, bayan yabar gidan Hai Hudah kai tsaye wajen abokinsa Murtala ya wuce, ya sanar da shi ya sami albashi shine yake son ya taimaka ya raka shi ya yi sayayyar kayan abinci.Wani irin kallo me cike da jindadi da kauna Murtala ya tsare musaddik da shi lokaci daya kuma yana yima Allah godiya, lalle musaddik ya samu,addu'ar da yake masa a kullum na dawowa hanya madaidaiciya ta fara tasiri,tunaninsa mai kyau ya fara dawowa, yau ga makudan kuɗi a hannunsa da zai je ya yi sharholiyarsa da su amma baiyi ba maimakon hakama tunanin ya sayi kayan abinci ya kai gidansa ya yi, me yafi wannan farinciki.Sosai Murtala ya nuna masa jindadin sa, duk da kuma motarsa ta lalace haka su ka dunguma suka tafi shago tare. Da taimakon Murtala musaddik ya sayi duk abinda ya dace nau'in kayan abinci da sauran tsarkake. Sannan ya sayi atamfofi guda uku.Domin dai Haj Hudah tayi masa gata ta hanyar ƙara masa wasu kuɗin bayan albashinsa, da ta nuna masa jindadin yadda yake tafiyar da aikinsa yasa ta kara masa kuɗin acewarta babu wani dalilin yi masa ƙarin bayan wannan.koma dai Meye musaddik dai ya jidadi domin duk saye sayen da ya yi sai da ya sami rarar wasu kuɗin, a ciki ne kuma ya yi ya yi Murtala ya karbi wani abu amma yace bazai karbi ko sisi ba, a hakan ma ji yake kamar ya fi kowa farinciki. Bayan sun kammala duk saye sayen ne sannan musaddik ya yi shatar a daidaita sahu ya taho gida, shi ma Murtala ya tare mashin ya haye ya koma wajen aikinsa cike da annashuwa.

Musaddik ya turo get ya shigo bayan ya sallami me adaidata sahun da ya kawo shi, Baba maigadi cike da farinciki ya dubi musaddik sannan ya dubi kayan abincin dake zube a gabansa yace “sannu da kokari musaddik Allah ya kara shiga lamarinka”, ya yi murmushi yace “Amin nagode”, muryar musaddik da Haj kilishi ta jiyo yasa ta yaye labulen windo tana kallon komai, Baba maigadi yace “Bari na tayaka kwasar kayan”, akan idon Haj kilishi Baba maigadi ya dinga diban kayan abincin yana shiga da shi Haj kilishi na kirga kayan harda katan katan din lemu,don ƙarin takaici ma harda su cakulet sai kace wasu kananan yara. Jin zuciyarta ta yi kamar zata fashe ta saki labulen gami da zuba tagumi ji kawai ta yi hawaye yana sauka a saman kuncinta, zafi take ji a ko’ina a cikin jikinta, wai meke faruwa ne?, ta tambayi kanta, kuka sosai take yi don me musaddik zai dinga cigaba bayan irin kudin da take kashewa don a datse duk wata hanyar cigaban nasa. Ta janyo wayarta cikin hawaye ta kira Haj Rakiya amma bata dauka ba ta zauna ta zubama wayar ido ta kuma kasa tsaida hawayen da ke fita mata, domin tana jin wannan itace kadai hanyar da zata sami saukin masifar dake yawo a cikin zuciyarta. Cikin kurewar hakuri ta kara danna sunan Haj Rakiya ta kira, wannan karon ta yi sa’a bugu daya Haj Rakiyar ta dauki wayar……………

Yanzu aka fara babu inda aka je, akwai badakala ta kin karawa sai mun hadu a littafi na biyu .

Yar gidan imam ✍️