Babi na baƙwai
by @dijensy
SHI SO DABAN YAKE🌸
By Khadija Ado Ahmad(dijensy)
7
Hassan yana jiran amsar sallamar da yayi wa Jidda tayi shiru fuskarsa ɗauke da faraa yace "Kiyi haƙuri na barki ke kaɗai idan kika gaji da zaman shiru ki na zuwa wajen Anty Ruƙayya ga yaranta nan kema ki samu abokan hira".Ta ƙasan ido take harararsa ba tare da ta ce komai ba ya ajje mata kankanar da ya sayo mata kan tebir kafin ya nufi wajen sif ɗin da yanzu ya dawo da kayansa ciki ya ɗauko daga shagon ganin shige da ficen ba me ƙare bane.Jidda kallonsa take daga tsayen bata taɓa ganinsa da ƙananan kaya ba kullum manya kaya 'Bagidaje kawai'Ta faɗa a rai tana jan tsaki a fili ya fito ya ji ta amma yayi kamar bai jita ba kayansa ya fara cirewa a hankali kullum banɗaki yake cirewa ya canja yau ta ga bai shiga dasu ba ta kawar da kai tana kallon wani waje daban Hassan ya rage kayan jikinsa yana barin singlet kafin ya shiga banɗaki da kayan da zai canja ga dukkan alama yakasa cirewa ne Jidda ta tsinci kanta ta yi dariya ita kaɗai a ciki tana karewa da hmmm "Allah na gode ma"Ta faɗa tana sakkowa daga kan gadon ta buɗe ledar kankanar ta fara sha kafin ya fito ta daddana ta da abarbar ta shanye ta cukukuye ledar tana komawa kan gado da yawanta amma sai da ta shanye duka ya fito ta yi ƙasa da ido.A shiryensa ya fito yana shafa turare tana kallonsa kayan kansu ya fi son farare sai ya jera kwana uku yana sa farin kaya daɗinta ɗaya mai tsafta ne da batasan ya za ai ba.Take faɗa a ranta daga gefen gadon ya zauna can ƙarshe "Gobe zan koma islamiya ,ban faɗa maki ba ina koyar da ɗalibaina a makarantar ranakun da nake off da safe ƙarfe takwas zuwa sha biyu sai dare asabar da lahadi fatan ban shiga haƙƙinki ba hakan ya miki?"Ya ƙare da tambayar Jidda kamar bazatace komai ba ta buɗe baki "Abinda ya shafeka ne ni ba nawa bane daga safe har ɗayan dare ma ba damuwa zan ba".Ta faɗa.
"Allah ya miki albarka nagode".Hassan ya furta har mamaki yake bata shi ko ɗan fushi da zuciya bayayi ne?ko shan kunu baya yi yana daga cikin abinda yake sake bata haushi kenan a ƙalla ai ko ɗan nuna alamu yayi amma sai ya nuna kamar bai ji haushi ko ɓacin rai ba.
"Badan kar nayi karanbani ba da na tallata maki makarantar tamu idan kina so kema sai ki na zuwa akwai ajin matan aure da safe idan kuma almuallima ce sai mu ɗauke ki kina so?"Wani malolon baƙinciki ta ji ya shaƙeta ta rasa me zatayi a ghetto ɗinnan sai makarantar matan aure ko koyar da yan islamiyya in banda gargajiya mai zai sa ya kawo mata wannan maganar taji kamar ta tsala ihu "Bazan ba ,ina da allon sauka ko in kawo maka ka ga sheda?nima da islamiyya ta akaina".Murmushi Hassan yayi "A a ba sai kin nuna min ba jazakillah kaira gobe idan na dawo da wuri sai na kai ki gidanmu ki ga aiki ko?"
"Goben ta zo tukun".Ta furta tana tashi ta shiga banɗaki don ta tsani magana da shi me tsaho ta rufe ƙofar.
Kamar yadda ya faɗa Hassan washegari da wuri ya dawo gida idan banda tana son ganewa idonta ba abinda zai sa ta jera dashi rai a haɗe ta shirya tana yafa ƙaramin viel nata atampa ce purple mai haske ta mata kyau ba kwalliya fuskarta amma smooth nata yasa ta yi kyau kuma ta shafa gloss mai kyalli Hassan yana ta satar kallonta tana jin idanunsa kanta ,Anty Ruƙayya ya sanarwa zasu fita ta musu Allah ya kiyaye fuskarta ɗauke da faraa har suka fitan farinciki duk ya mamayeta a duniya tana so ta ga Hassan yana cikin walwala tana fatan sun fara fahimtar junansu Hassan daya tamkar dubu ne ba iya shi ba ita dai aure a family su bata da tasani dukda yau an wayi gari mijinta baya duniya amma har abada bata jin zata samu miji nagari kamar yayan Hassan yadda yake da kirki haka Hassan basu da buri irin su faranta maka zaman da tayi da sirikarta ma bai taɓa bata matsala ba suna kyautata mata tana fatan Jidda zata zama hasken idaniyansa wataran.
Jidda ranta ba daɗi suka jero da Hassan tana ankare da yadda yan layin nasu ke kallonsu kamar zasu cinyesu 'Shegu yan saido"Ta faɗa a ranta bayan sun ƙarasa bakin titi ya tare masu napep bata taɓa tsamamnin zata yi auren ɓigewa da shiga napep ba.Hassan ya faɗa masa unguwar da zasu ya ce su shiga Hassan ɗin drop ya ɗauka don baya son wani ya shigo musu.A keke napep ya ke sauke idanunsa kan hannunta ba lalle amma ya yi masa kyau a hakan yatsunta kuɓulbul yaji kamar ya kama ya riƙe amma wani abu na dakatar dashi ya basar yana ɗauke ido basu ce komai ba har aka isa ƙofar gidan ,sabuwar unguwa ce da tsirarin gina gine kuma layikansu da space amma taji wani abu ya soketa musamman da ganin gate ɗin tana kallon inda katangar gidan ta tsaya ga dukkan alamu ba wani girma plaster ce a wajen bayan ya fita ya biya mai keke ta fito kamar wacce kwai ya fashewa ya ciro mukullin gidan a aljihu ya na buɗe ƙofar ya ce mata bismillah ta sa 'kafa tana kallon ɗan faɗin tsakar gidan kama daga kitchen da wani ɗaki taji duk basi mata ba shikuwa Hassan yana ta nuna mata parlour ne babba da ɗaki ɗaya ciki sai banɗaki a ciki ta ɗaga kai tana kallon cieling ne na zamani amma ba pop bane duk jikinta yayi laasar ba yadda ta zata ba Baba sun gama da ita kam idan ma auren dolen ne ayi mata ga mai tsoka mana har gwara a haɗa ta da mai mata uku da gida irin wannan "fenti kawai ya rage banɗaki zasu ƙarasa saka tiles wane kala kike so?"Taji muryarsa tana kallon window madaidaita ansa burglar "Hassan duk abinda kake so mu koma gida yanzu kaina ciwo yake"Ta furta baƙinciki yazo mata har wuya ta fice daga gidan Hassan nan da nan ya fito ya kullo ƙofar "Yaushe kika fara jin ciwon kan ?"Ya faɗa duk a duburburce yasa ta jira ya samo napep a titi ta bisa da ido da harara duk nisan titi haka ya fita ya samo keke napep ya fito "Kiyi haƙuri da jirana zaki iya tafiya?"Ya tambaya yana ƙoƙarin riƙe mata hannu ta doje tana shiga ta ɓata fuska ya na kallonta sai zuba mata sannu yake bata ko amsashi.
Hassan sai da ya tsaya a chemist ya kari mata paracetomal suka komo gida suka shiga ɗaki ,fita yayi nan da nan ya siyo ruwa ya kawo mata yana ɗakko mata cup ya zauna gefenta yana batakamar yasha mata maganin ta karɓa tana ɓalla "Ka samo min sugar toh idan ba haka ba amai zan"Ta faɗa ya tashi yana fita ta jefa ƙasan gado tana kora ruwa ya dawo "Kinsha?"Ya tambaya ta jinjina kai tana miƙa tafin hannu ya zuba mata ta watsa a baki "Sannu".Ya faɗa ta jinjina kai.Hassan magriba ta yi ya je masallaci ya dawo ya tambayeta kan ya daina tace masa eh.Anty Ruƙayya ta aiko musu da abincin dare dawowarsa daga isha ya zuba mata abincin alkubus ne da lafiyayyar miyar gyaɗa ya kira Jidda ta sakko,ta miƙe tana zaunawa "Ya min yawa"Ta faɗa ba wani burgeta alkubus yake ba yasa tun ɗaxun bata sakko ta ci ba don ta buɗe ta gani kawai yunwar da ke addabarta ce. "Toh mu ci tare".Ya faɗa ta ɗago ta kallesa fuskarsa da murmushi ya yi ƙoƙarin tsaida idanunsa kanta yana kallonta leɓenta ya zubawa ido tana ta twisting yayi mamaki da bata ce masa a a ba ya ga ta ɗauki spoon shima haka yana ƙara alkubus ɗin suna fara ci tana tauna abinci a hankula wani irin abu yake ji yana tsarga mashi ya daure suka gama ta rigashi ajje cokalin tana shan ruwa ta shiga banɗaki wanka har sannan ba a dai dai yake jinsa ba wani irin abu na fizgarsa Jidda ta fito daga wanka kamar koyaushe ta ɗaura towel tana fitowa ta zauna gefen gadon ta buɗe sif ciro kayan baccinta ta ajje gefenta counter ɗinsa ya faɗi ƙasa yana duƙawa ƙasan gadon ya xira hannu laluba ya taɓo maganin da ta jefa ƙasa ya jawo su biyu hasken fitila ne kawaia ɗakin yasa ba ta lura ba ya ɗakko su murmurshi yayi fahimtar wayo ta mashi ɗazun ya fita yana zubarwa shara ya dawo yana rufo ƙofar ɗakin window ventilation ya buɗe sosai yadda iska zata shigo duk da ba zafi sosai.Takawa inda take yayi yana mai zaunawa taji ɗuminsa a gefenta ta nisa da tunanin gidan da zasu koma da rayuwa da taƙe tsammnin zata shiga ko ya makomarta?Ɗan dagowa tayi tana kallonsa ta tamke fuska ya kasa ɓoye murmushin fuskarsa wani irin abu yake ji kamar magnet da ƙarfe tsakaninsu ƙamshin sabulun da tayi wanka da danshin ruwan jikinta ya gauraye yana mashi daɗi a hanci murya ƙasa ƙasa a tausashe yace "Shine kika min wayo baki sha maganin ba?"Ya faɗa cikin wani salon murya ta kauda ido tana turo baki ta ɗauki rigar baccin tana ɗorawa a cinya saka kayan take son yi amma zamansa ya sa ta kasa sakewa tana jin wani irin abu a jikinta bata iya amsashi ba "Faɗa min me ya sa ki ciwon kai? ko gidan ne bai maki ba? baki ce komai akai ba?"Jin bata ce uffan ba yana sake raɓowa jikinta "Inda lokaci in sha Allah zan yi mana wanda ya fi haka kuma zai zama mallakinki Jidda bani da ƙarfi amma nayi miki alƙawari bazaki kuka ba akaina ,zan kula dake Jidda ki bani dama zaki alfahari dani".Ya ƙare magana cikin wata siga da ya sa tsikar jikinta tashi don muryarshi a daf da kunnenta take ji bata yi aune ba ta ji hannunsa kewaye a bayanta yana shanshana wuyanta ta rufe ido zuciyarta na bugawa wani sanyi da take ji a ilahirin jikinta towel na jikinta ya fara zamewa ta bayan tana riƙe gaban ƙirjinta Hassan da jikinsa ke azalzalarsa ya kai hannunsa bayanta yana shafawa zuwa mazaunanta ya kai bakinsa dai dai leɓenta yana ɗora nashi wani irin zazzafan kiss yake mata yana ɗora hannunsa a ƙirjinta yana gangarawa kan breast ɗinta ɗayan hannun yake gangarowa kan santala santalan cinyarta ya na ɗage towel ɗin sama.....
*Littafi na kan Arewapen a danna mani like a cigaba da karatu kunsan dai book yafi daɗin karatu a Arewapen😉*