RAUNIN DA BA A GANI

Chapter 17:RDBG

by @meefatinkwriters99

RAUNIN DA BA A GANI 

Meefat ink ✍️ writers 

Asabarce mai cikeda annashuwa, tun kafin karfe takwas na safe harabar ADAMAWA STATE UNIVERSITY tafara cika da mutane. Ta ko'ina dalibai ne keyawo cikin sutura mai kyau, yayinda jami'an tsaro ke tabbatarda cewa komai yana tafiya cikin tsari. Baranar faculty of pharmacy ce kadaiba, yau babban ranace ga Universityn baki daya. ANNUAL AWARD AND RECOGNITION DAY ranar da jami'an ke warewa domin karrama dalibai dasukayi fice a fannoni daban daban ;shugabannin dalibai, masu bincike, masu kirkire kirkire, masu hidimar al’umma da wadanda sukayi fice a karatu {studies}. 
A kofar wani katafaren hall wani babban banner ne, ajiki an rubuta. 

ADAMAWA STATE UNIVERSITY ANNUAL AWARD AND RECOGNITION DAY 2026 “Celebrating excellence, Leadership and innovation” 
Ana tsayawa ana daukar hotona agaban banner din, wasu dalibai acan gefe suna cewa “ai yau sai mun cika gallery da hotona” akayi dariya cikin nishadi. 
Babban hall din yayi kyau tamkar za ayi bikin kasa, an kawatashi da furanni masu kyau da daukar ido, agaba akwai babban stage a tsakiyarsa akwai tambarin jami'ar,acan gefen hagu an tanadi kujerun vice Chancellors(VC), deputy vice Chancellors, registrar, bursers da sauran manyan masu mukami a Universityn. 
A gefen dama kuma akwai kujerun special guest ciki akwai commissioner of health, manyan professors, shugabannin manyan companies, wakilan kungiyoyin lafiya, sai wakilan yola holdings group:companyn da yahada branches dayawa kamarsu yola health hospitals, yola pharmaceutical and logistics, yola care foundation, da shirye shiryen tallafawa matasa ta hanyar scholarship, internship da youth empowerment. Sobada irin wadannan gudummawarce jami'ar ta basu gayyata ta musamman. 
Sanye take cikin doguwar abaya mai launin ruwan toka, batacika yin kwalliyaba amma sai yau tatsinci kanta dayin light makeup, akwai wani sihirtaccen kyau atattare daita kallo daya zakamata kakara. Zaune take alayi na uku a sashen pharmacy students, kawayentane agefenta suna hira sama sama, fina tace “gaskiya kina kokari sosai, ga lectures, tests, assignments, practicals sannan idan antashi daga makaranta kiwuce shop” sai samha dake game awayarta dukda ita ba student din department din bane amma tazo tamakale a wajensu sai tadago tace “hmm wallahi ni idan na tuna yadda kike tafiya from school to fashion dinnan naki sai kawai nace allah yasaka da alkhairi” ruhy tayi murmushi tace “ai rayuwace, bani kadai bane akwai dalibai dayawa da suke wahala fiye dani” meenatce tace cikin tsokana“ya kike gani idan aka kira sunanki” ruhy tace “kada kifara, har yanzu akwai sauran categories dayawa kuma akwai manyan students na final year mafa"meenat tayi dariya dahaka wasuma suka shiga hirar aka cigaba. 
Wata bakar mota ranger over ce ta kunno kai, jami'an tsaro suka masa gefe protocol officer yayi saurin tafita zuwa wajen. Jabir ne yafara fitowa sai azan sanye suke cikin suite na jabir ruwan kasa yayinda na azan yakasance baki, tsayawa yayi yana kallon students dake tayawo a harabar makarantar sai wani murmushi yabayyana a fuskarsa, ganin sai zabga murmushi yake sai jay yace shima yana murmushin.