BABI NA SHAƊAYA
Tsawon daƙiƙa uku kacal da muryar matar nan ta ɗauka a cikin kunnen M-Arrow ya isa ya katse jerin tunanin da yake ciki.
Kalma uku ne kawai...
"Arrow... na dawo."
Shiru ya biyo baya.
M-Arrow bai yi magana ba.
Bai kuma yi yunƙurin katse kiran ba.
Ya tsaya yana saurare har sai da layin ya mutu daga ɗayan ɓangaren.
A hankali ya sauke wayar daga kunnensa.
His deep amber eyes suka sauka kan fuskar wayar.
Lambar ta riga ta ɓace.
Ba wani motsi ya bayyana a fuskarsa ba.
Ba mamaki. Ba firgici.Ba kuma wani yanayin damuwa.
Sai dai wani irin shiru daya karu a kan shirun sa na ko yaushe.
Ya jefa wayar a kan kujerar Private Jet ɗinsa cikin nutsuwa.
Sannan ya mayar da dubansa ta jikin tagar jirgin.
Fararen gizagizai suna watsewa a hankali yayin da jirgin ke ci gaba da ratsa sararin samaniya.
Leɓɓansa suka motsa kaɗan.
Ya furta cikin murya can kasa wan da ko da kana kusa ba lallai ne kaji ba.
"So... you finally came back."
Daga nan...
Komai ya koma kamar babu abin da ya faru.
Ya lumshe idanunsa.
Ya jingina bayansa da kujerar cikin cikakkiyar natsuwa.
Mutumin da ya iya murƙushe motsin zuciyarsa fiye da yadda yake murƙushe maƙiyansa..
---
Da alama miskilancin nasa na yau ya
ninka na kowace rana, domin ko jami'an dake hidima a cikin jirgin sun gaza matsawa kusa da
shi, sakamakon yadda fuskarsa ta
bushe ta dake gaba ɗaya, babu ko alamar sassauci.
ta bayyana ainihin sa The Executive
Director General Human Rights Majeed Burhan Sulaimanu Shadum.
Ko Air Hostess ɗin da ta saba kawo masa abin sha, sai da ta tsaya tana jiran izini kafin ta ƙaraso.
tana jan ƙafafun ta.
ta ɗan duka tana sanar da shi ga abin sha.
A sannu ya buɗe lumtsassun His deep amber eyes.
Ta yi saurin miƙa masa kofin coffee cikin girmamawa.
Ya karɓa ba tare da ya kalle ta ba.
Ta ja da baya cikin ladabi.
Babu wanda ya kuskura ya ƙara katse masa tunani.
Domin duk wanda ya daɗe yana aiki tare da M-Arrow ya san abu ɗaya.
Shirun M-Arrow yana da nauyi fiye da doguwar magana.
---
Bayan doguwar tafiya da ta ratsa tekuna da nahiyoyi, ƙasaitaccen jirginsa mai zaman kansa ya sauka a filin jirgin saman Heathrow da ke birnin London na kasar Ingila.
Da ƙafafun jirgin suka taɓa titin sauka...
Wata iska mai tsananin sanyi ta bugo, ƙanƙara ya mamaye sararin samaniya, alamar cewa lokacin sanyin dusan ƙanƙara na London ta fara nuna ƙarfi.
Tun kafin jirgin ta gama daidaita
Manyan motoci na alfarma baƙaƙe guda uku, samfurin Mercedes-Benz S-Class, sun riga sun tsaya a bakin matattakalar jirgin.
Rukunin jami'an tsaronsa na can ƙasar dake sanye da baƙaƙen kaya masu kauri trench coats.
sun yi layi kyam suna jiran fitowarsa.
Kofar jirgin ta buɗe da wani ni'imantaccen sauti.
M-Arrow ya bayyana. iskar sanyin garin London ta bugi fuskarsa, ya lumshe idanunsa a hankali kana ya buɗe yana daidaita tsayuwar sa a kan matakalar jirgin.
Sanye yake cikin tsadaddiyar rigar sanyi designer bespoke cashmere overcoat da baƙar turtleneck sweater
Gaba ɗaya rigar ta zauna daram a jikinsa, ta ƙara fito da kamalar jinin sarauta, kwarjininsa na musamman, da ainihin siffarsa ta jaruman maza masu ji da lokaci da cikar zati.
kayan da suka ƙara fito da kamalarsa da kwarjininsa.
A sannu ya janyo hular designer winter overcoat ɗin jikin sa ya saka a kansa,
sakamakon wani hucin sanyi mai haɗe da dusan ƙanƙara daya buso...
Idanunsa sanye da bakin gilashi.
Fuskarsa kuwa...A yadda ta saba take. Mai cike da natsuwa. Mai cike da iko.
Mai sa duk wanda ya kalle ta ya san cewa wannan ba mutum ba ne da ake karanta abin da ke zuciyarsa.
Ya sauko daga matattakalar jirgin cikin takun da ba ya gaggawa, ba ya jinkiri.
Takun mutum ne da ya san ko wanene shi.
Har ya isa bakin motar farko, wani dogon jami'in tsaro Bature ya yi saurin buɗe masa ƙofa.
"Welcome back to London, Sir. I hope you had a smooth flight."
M-Arrow ya ɗaga kai kaɗan.
Ya amsa cikin taƙaitacciyar murya mai cike da iko.
"It was."
Kalma biyu kacal.
Amma suka isa su sa jami'in ya sake sunkuyar da kansa cikin girmamawa.
Michael ya biyo bayansa ya rufe ƙofar.
Cikin daƙiƙu kaɗan...
Jerin motocin ya bar filin jirgin saman Heathrow, yana ratsa hazo zuwa tsakiyar birnin London.
Bayan tafiyar kusan mintuna talatin, jerin motocin suka shiga cikin unguwar Mayfair, ɗaya daga cikin unguwannin da suka fi tsada da ƙima a birnin London.
A ƙarshen wata hanya mai cike da manyan bishiyoyi da fitilun zamani, suka tsaya a gaban wani katafaren gida mai hawa uku.
Ginin ya kasance abin kallo.
An gina shi da salo na zamani (ultra-modern design) inda galibin bangon gidan gilashi ne mai kariya ta musamman, haɗe da sabbin na'urorin tsaro da ba kasafai ake samu a gidajen mutane ba.
Da ƙofar babban get ɗin ta buɗe kai tsaye ta hanyar na'ura, motocin suka shiga cikin tsari.
Suna tsayawa...
M-Arrow ya buɗe ƙofar motar da kansa.
Ya fito cikin natsuwa.
Ma'aikatan gidan sun riga sun yi layi a ɓangarorin hanyar shiga.
Kowannensu ya sunkuyar da kansa cikin girmamawa.
Bai tsaya karɓar tarba ba.
Bai kuma waiwayi kowa ba.
Ya wuce tsakaninsu cikin takunsa na ƙasaita, tamkar sarkin da ya saba da girmamawa fiye da tarba.
Michael kuwa yana biye da shi, riƙe da jakar takardu da kwamfutar tafi-da-gidanka.
Suna shiga babban falon gidan, Michael ya ɗan ƙara sauri domin ya riske shi.
Cikin kalmar turanci gami da girmamawa ya ce,
"Sir... akwai wani saƙo da ya kamata ka sani."
M-Arrow bai tsaya ba.
Sai dai ya ɗan rage tafiyarsa kaɗan, alamar yana saurare.
Michael ya ci gaba.
"A lokacin da muke cikin jirgi, na karɓi kira daga sakataren Alhaji Dad ɗin ka. Ya ce yana buƙatar magana da kai cikin gaggawa. Ya ce batun ya shafi ƙorafin da wasu manyan 'yan kasuwa suka shigar a kanka bayan taron da aka yi a Abuja."
Shiru ya ɗan ratsa falon.
Michael ya ƙara da cewa,
"Ba wannan kaɗai ba, Sir... Wasu daga cikin manyan masu saka hannun jari a kamfen ɗin Alhaji sun fara matsa masa lamba. Sun ce idan ba a dakatar da matakan da kake ɗauka a kansu ba, za su janye cikakken goyon bayansu."
A wannan karon...
M-Arrow ya tsaya.
Ba don ya firgita ba.
Ba don maganar ta ba shi tsoro ba.
Sai don ya gama sauraron abin da ake faɗa.
Ya saka hannu cikin aljihun rigarsa.
Idanunsa suka tsaya kan wani zanen zamani da ke manne a bangon falon.
Bayan ƴan daƙiƙu...
Ya juyi a hankali.
Ya kalli Michael kai tsaye.
Muryarsa ta fito a hankali.
Mai zurfi. Mai cike da iko.
"Michael..."
"Yes, Sir."
"Kashe wayarka."
"Okay Sir."
Michael bai tambaya ba. Nan take ya kashe wayar.
M-Arrow ya kuma dubansa da yanayin sa na kallo ɗaya tak sannan ya furta.
"Ka sanar wa Dad cewa..."
Ya ɗan yi shiru na daƙiƙa guda.
"...Idan yana son ganina, ya nemi lokaci na daban."
Ya ɗan matsa gaba.
"Kar ya haɗa ni da siyasa."
Falon ya sake yin tsit.
Sai muryarsa kaɗai ke fita.
"Na taɓa gaya masa....Adalci ba kamfen ba ne."
Michael ya sauke kansa cikin girmamawa.
Ya san wannan magana ba ta buƙatar ƙarin bayani.
Amma M-Arrow bai gama ba. sai dai yasan abun babbane tun da har ya yi dogon magana irin haka.
Ya ɗaga idanunsa.
A karon farko wani ɗan ƙaramin ƙarfi ya bayyana a cikin muryarsa.
"Kuma ka sanar da duk wani ɗan kasuwa da yake tunanin zai iya amfani da rashin kasancewata a Najeriya ya ci zarafin talakawa..."
Ya ɗan yi shiru.
Sannan ya ƙarasa da cewa,
"... Ya tabbata zai biya farashin abin da ya aikata."
Ba tare da ya ƙara cewa komai ba...
Ya juya.
Ya nufi matattakalar da ke kaiwa babban ɗakinsa.
Michael ya tsaya a inda yake.
Yana kallon bayansa.
A zuciyarsa ya yi murmushi kaɗan.
Domin ya daɗe da fahimtar abu ɗaya...
M-Arrow ba ya yin barazana.....
Idan ya faɗi abu... yana aikata shi ne...
Ya haura matattakalar cikin nutsuwa, ba tare da ya sake waiwayen Michael ba.
Takunsa ne kaɗai ke amsa sauti a cikin doguwar hanyar da ta nufi babban ɗakinsa.
Ya na isa bakin ƙofar, na'urar tantance fuska ta haska cikin daƙiƙa guda.
"Identity verified."
Ƙofar ta buɗe a hankali.
M-Arrow ya shiga.
yana shiga, ƙofar ta sake rufewa kai tsaye, ta katse duk wata hayaniya daga wajen.
Ɗakin nasa ya kasance haɗuwar fasahar zamani da ƙayataccen tsari.
Babban ɗaki ne mai faɗi, cike da kayan alatu da aka tsara cikin sauƙi amma masu tsananin tsada.
Ya taka a hankali zuwa gaban katafaren gilashin da ke kallon birnin London.
Dusan ƙanƙara yana sauka a hankali.
Fitilun birnin suna walkiya ta cikin hazo.
Ya tsaya na wasu daƙiƙu yana kallon sararin birnin.
Ba don yana jin daɗinsa ba...
Sai don yana tattara tunaninsa.
Daga nan ya cire baƙin gilashin idanunsa, ya ajiye shi a kan teburin gefensa.
Ya zare rigar designer overcoat ɗinsa ya rataye ta cikin tsari.
Bai yi gaggawa ba.
Domin M-Arrow bai taɓa barin wani yanayi ya rinjaye masa nutsuwa ba.
Ya taka zuwa gaban wani katafaren allon kwamfuta mai haɗe da manyan na'urorin tsaro da tattara bayanai (Cyber Security System).
Da yatsansa ya taɓa allon.
Na'urorin suka fara aiki.
A cikin daƙiƙu kaɗan, bayanai daga cibiyoyin sa ido daban-daban suka fara bayyana a jere.
Rahotannin kasuwanni.
Rahotannin hukumomi.
Korafe-korafen jama'a.
Da kuma bayanan sirri da ba kowa ne zai iya samu ba.
Idanunsa masu kaifin basira suka fara bin bayanan cikin natsuwa.
Ba ya karantawa saboda neman labari...
Yana karantawa ne saboda neman hujja.
Wani rahoto ya tsaya masa a ido.
Wasu manyan attajirai sun fara shirya wata sabuwar haɗaka domin ƙara tsadar kayan masarufi a Najeriya.
Sun tsara cewa idan suka matsa lamba a lokaci guda, za su tilasta gwamnati ta sassauta matakan da aka ɗauka a kansu.
M-Arrow ya ci gaba da karanta rahoton ba tare da wata alamar tashin hankali ba.
Sai da ya kai ƙarshensa.
Sannan ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci.
Da ya sake buɗe su...
Wani sanyin tabbaci ne ya bayyana a cikinsu.
A hankali ya furta.
"Not on my watch."
Ya ɗauki wayarsa.
Ya buɗe wani sirrin layin sadarwa da ba kowa ya san da wanzuwarsa ba.
Saƙo guda kawai ya aika.
«"Freeze every ongoing approval. Launch a full forensic audit. Effective immediately."»
Bai jira amsa ba.
Ya kashe allon.
Ya juya daga na'urorin.
A wurinsa...
Idan hujja ta cika, aiki yana farawa ne ba tare da hayaniya ba....
★★★★★
---
A halin da ake ciki kuwa...
Can cikin babban birnin tarayya, Abuja.
Katafaren gidan tsohon gwamnan Jihar Adamawa da ke Shadum Estate ya shiga wani yanayi na damuwa da ba kasafai ake gani ba.
Duk da wadatar arziki, tsastsauran matakan tsaro, da walwalar rayuwar da ta mamaye gidan...
Kwanciyar hankali ta yi ƙaura.
A cikin falonta na musamman, Mom ta kasa zaune, ta kasa tsaye.
Tun bayan tafiyar M-Arrow zuwa London, zuciyarta ta kasa samun nutsuwa.
A karo na ba adadi ta sake latsa lambarsa.
Amsar da ta samu ita ce wadda ta dade tana samu.
The number you are calling is switched off...
Ta sauke wayar a hankali.
Ta runtse idanunta na ɗan lokaci.
Sannan ta furta cikin muryar uwa mai cike da damuwa,
"Ya Allah... ka kiyaye mini ɗana."
Ta buɗe idanunta.
Ta sake kallon wayar da ke hannunta.
Har yanzu babu wata alamar zai kira.
Ta girgiza kai cikin takaici.
"Majeed..."
"Me yasa kullum sai ka ɗauki damuwar duniya ka ɗora a kanka?
"Kai fa ba jinin wahala bane..... Jinin sarauta ne...
Me yasa ka kasa barin gwamnati da masu mulki su yi aikinsu?."
Ta sauke numfashi mai nauyi.
A hankali ta miƙe tsaye.
Doguwar rigarta ta alfarma tana jan kafet ɗin falon yayin da take nufar sashen mijinta.
Ta san abu ɗaya...
Idan akwai wanda zai iya fahimtar Majeed fiye da ita...
To shi ne Alhaji Burhan.
---
A daidai wannan lokacin...
Alhaji Burhan yana cikin ɗakin bincikensa (Study Room).
Takardun kamfen, rahotannin masu ba shi shawara da bayanan siyasa sun mamaye faffadan teburinsa.
Sai dai... idanunsa na kan takardu...
Zuciyarsa ba ta kansu take ba.
Tun bayan rahoton da ya samu daga sakatarensa...
Ya fahimci cewa wannan rikicin ya fara ɗaukar sabon salo.
Mom ta kwankwasa ƙofar. Dad ya ɗan dakata da abin da yake yi, ya sauke numfashi, domin ya san ko wace ce a bakin ƙofar, musamman a irin wannan lokacin. Ya gyara zamansa sannan ya ce,
“Shigo.”
"Shigo."
Mom ta tura ƙofar ta shiga.
Dad ya ɗaga kai ya kalle ta, a take...ya fahimci abin da ya kawo ta.
Ya cire gilashin karatunsa ya ajiye a kan tebur.
"Gimbiya... Kina ta ƙoƙarin kiransa kenan?"
Ta zauna a kujerar da ke gabansa.
Ta gyada kai a hankali.
"Har yanzu wayarsa a kashe take."
Alhaji Burhan ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci.
Ya sauke numfashi.
"Kamar yadda na zata."
Shiru ya ratsa ɗakin.
Mom ta karya shirun da faɗin.
"Alhaji... na fara jin tsoro. Ba wai saboda London ba... na san Majeed ya iya kare kansa, Amma ina tsoron mutanen da ya taɓa muradunsu."
Alhaji Burhan ya jingina bayansa da kujera.
Ya haɗe yatsunsa waje guda.Sannan ya ce cikin nutsuwa,
"Tsoronki yana da dalili. Saboda abin da Majeed yake yi yanzu....ya fara shafar manyan mutane."
Ya ɗan yi shiru.
Sannan ya ci gaba.
"Attajirai biyar sun janye goyon bayansu ga kamfen ɗina. Ba don sun ƙi ni ba...Sai don suna son in dakatar da Majeed."
Mom ta ɗaga kai da sauri.
"To me za ka yi?"
Alhaji Burhan ya yi murmushin da babu daɗi a cikinsa.
"Ba zan taɓa tilasta masa ya daina kare talakawa ba. Sai dai...ina son ya fahimci cewa siyasa tana da nata lissafin."
Ya ɗauki wayarsa.
Ya buɗe wani lamba.
Sannan ya ce,
"Zan kira babban amininmu da ke London. Ba don ya tsayar da Majeed ba... Sai don ya tabbatar min cewa yana cikin ƙoshin lafiya."
Mom ta lumshe idanunta.
Wannan kaɗai ya ɗan kwantar mata da hankali.
Amma har yanzu...
Wani abu a zuciyarta yana ci gaba da raya mata cewa...
Tafiyar Majeed zuwa London ba tafiya ce ta hutu ba.
Wata ƙaddara ce ke shirin buɗe sabon babi a rayuwarsa........!
Mommyn Twins ce