MAHREEN

PAGE 11--20

by @swrites22

TWO YEARS LATER

Wata matashiyar budurwa na hango ba zaa kirata doguwa ba kuma ba zaa sata sawun gejerubace ba , ba fara bace amma light skin gareta mai daukar Ido tana da dogon hanci da idanuwa dara dara wanda suke zagaye da zara zaran lashes haka eyebrow ta gazar gazar batada kiba kuma ba siririya bace a dire take irin su ne ake Kira da figure 8 sanye take da ash din jeans Wanda yabi jikinta sai black top data dora wadda zata Kai guiwarta daga baya kuma takai har kasa ta yane kanta da karamin veil sai P cap data sa ta janyota gaba sosai ta yadda ta rufe rabin fuskar ta a yau ta diro naija da gudurin fara aiki a hukumar DSS dakuma yin aiki a matsayin ta na lawyer sabanin yadda ta tafi da cewa baza tayi aiki a matsayin dss ba idanunta ta daga tana kallon airport din wayarta dake Kara ta dauko a jaka Imran sunan daya bayyana Akan screen din wayar dauka tayi daga daya bangaren naji ance hello mahreen I haven't seen you yet and ur flight landed 15 minutes ago, where are you ? I'm coming kawai tace sannan tafara tafiya Kana kallonta zakasan jinin sarauta Yana gudu a veins dinta daga yadda take tafiya . tana fita tagan su nawal ce ta fara hangota da gudu taje suka rungume juna welcome back home sister murmushi ta mata taja kumatun ta how are you doing ? I'm doing good buh I missed you Imran ne ya karaso Lilly ya fada juyawa sukayi direction din da yake murmushi yasakar Mata welcome back Lilly , thank you bruh, ' so let's get home Cox ummi is so eager to see you , I missed her so much wlh, really ya fada tare da daga mata gira yeah tace kawai tayi gaba suka rufa Mata baya .

Tafiya sukeyi amma ita ta Lula cikin wata duniyar tunanin har saida Imran yace Lilly you haven't gisted me about your studies hope you did it successfully idonta akan titi tace alhamdulillah buh I'm so exhausted right now later in sha allah, "ohk no problem ur wish is my command, ahaka suka karasa gida ba wanda yakara magana a cikinsu. cikin farin ciki aunty ummi ta tarbe ta bayan sun zauna take tambayar sana bata zo ba (Sana tayi aure bayan tafiyar mahreen kuma ba gari daya suke ba)har 1am suka Kai suna hira sannan suka shiga bacci koda ta shiga daki ba bacci tayi ba tunane tunane take ta yanda zata shawo Kan aunty ummi ta yadda da abinda takeso a karshe dai ta yanke shawarar samun Imran domin yi mata jagora ta samu aiki a hukumar DSS tare kuma da fara aiki a matsayin ta na lawyer domin ta hakan ne burinta na daukan fansa zai cika da wanna tunanin bacci yayi awun gaba da ita.

THE NEXT DAY

Zaune take a garden sanye da sweet pant da top long sleeve sai P cap dinda ta kifa a fuskarta kanta ma kallon sama kafarta daya akan table din wajen tana girgizata kadan kadan Imran ne ya karaso wurin da fadin helloo lilly dagowa tayi sannan tace ah Imran I need to discuss something with you kujera yaja ya zauna sannan yace go ahead dear I'm all ears, dan muskutawa tayi sannan tace you know when I was going to Russia I told aunty ummi I wasn't going to work as a DSS girgiza kansa yayi yana bata duka attention dinsa saida ta sake nisawa tukun tace so now I have changed my mind I want you to take me to any DSS headquarters, I'm eager to start my work early, and after that Ina son fara aikina matsayina ta barrister but I prefer to work independently, without being under someone's control, and please I'm not requesting for advice and I'd like to keep this matter confidential between us between us tana gama fadar haka ta maida P cap dinta a fuska nisawa yayi yana tsinewa wa'anda suka kashe mata familynta da wargaza farincikin ta yarinya mai saukin Kai da Wasa da dariya amma yanzu duk ta zama somehow sai ahankali a fili kuwa cewa yayi ohk I will check and get back to you , great kawai tace jin bata sake magana ba yasa shima ya tashi ya tafi .

AFTER ONE WEEK

Imran yayi duk abinda mahreen tace kuma an mata komai kasancewar documents din karatun ta Bana nan bane yasa cikin sauri suka amsheta a babbar headquarter DSS ta jahar sannan ya sama mata office awani chambers din lawyoyi bai fadawa ummi aiki data samu a headquarter dinba shi dai yace mata ta bukaci ya kama mata office zata fara aikin ta a matsayin Barr.

Da kyar aunty ummi ta rinjayi mahreen ta amince Kam cewa zataje visiting masaurauta tare suka shirya ita da nawal da aunty ummi Imran ya kaisu cikin shigarta ta kullum kamar yadda ta saba wando da riga sai after dress data daura akai wanda aunty ummi ce ta matsa Mata Kan sai ta sa ganin bai kamata ta shiga masarauta da wannan shigar ba, wani dark shade ta maqala wanda ya kusa mamaye rabin fuskarta fada suka fara shiga Inda suka tarar da Abdul hameed tare da waziri agaban mai Martaba sai fadawa, saida suka miqa gaisuwa wajen mai martaba sannan suka gaisa dasu waziri da Abdul hameed, mai Martaba ne ya buqaci mahreen tazo kusa dashi kamar zaiyi kuka saboda tunawa da dansa da yayi dafa kanta yayi tare da samata albarka dagowar da zatayi idonta ya sauka Kan wani abun daya sa zuciyar ta daina bugawa na wucen gadi , ba komai bane face tabon hannun Abdul Hamid dagowa tayi da sauri suka hada Ido tabbas shine wanda ya kashe mata familynta baza ta taba manta wanna hannun da kwayar idanun da sukayi sanadiyyar rasa duk wani gata nata ba sosai zuciyarta ta tafaso har idonta na kankancewa saboda masifa saurin maida kanta kasa tayi dan Kar su fahimci halin data shiga Abdul hameed ne yafara magana cikin karfin hali da kuma faduwar gabar data dirar masa lokacin da suka hada ido da mahreen Allah sarki ishaq yaro mai ladafi da biyayya Kai duk wanda suka masa haka baza suga da kyau ba sannu kinji yarinya Allah yakara maki hakurin rashin su hakika anyi rashi babba su aunty ummi ne suka amsa da ameen ita kuwa wani murmushi tayi kawai taji duk abinda yace saboda tanajin Hausa sosai awajen mahaifiyarta dan tun tana karama tane mi ta iya saboda idan sun dawo Nigeria ta dinga magana da family itama ace ta iya Hausa, har suka fita ranta abace yake amma tayi kokarin boyewa ta hanyar maida dark shade dinta fuskarta bayan sun fito daga fadar part din grandmothern ta sukayi .

Tazo shiga shi kuma yazo fita yana waya har suka mangaji juna juyowa tayi da masifa hey don't you have eyes....juyowa yayi ya zuba mata sexy eyes dinsa masu matukar haske da sheki take taji duk kwarjinin sa ya cika mata Ido har takasa sauke masifar datayi niyyar yi I have got perfect vision so no specs needed for me yana Kai karshe ya giftasu ya wuce , aunty ummi da nawal ma ciki suka shige kawai suka barta anan Imran ne yace haba Lilly easy mana who's he ta tambaya a fusace Imran ne ya gyara tsayuwarsa sannan yace your cousin my cousin! ta sake maimaitawa from where ta fada a yatsine from your uncle Khaled's family, he is his first son Maher and there's his brother Ayman and their sister manira I thought you met her when you visited him in Egypt right dan yatsanta tasa abaki ta ciza batare da tayi magana ba sai kuma tayi gaba binta yayi a babban parlour suka samesu , Fulani ko kuma nace grandmother dinsu tana hakimce a wata kasaitacciyar kujera kuyanginta suna Matsa Mata kafa su aunty ummi suna zaune akasa sai wani saurayi data hango shima kusa da kafar tsohuwar yana zaune , kamar da taga sunayi da wanda ya fita yasa ta gane shine kaninsa ayman dinda Imran yace mata karasawa tayi ta nemi guri ta zauna saman kujera , Fulani ce ta bukaci kuyangin su basu wuri sannan ta kalli mahreen aunty ummi ce tace mahreen get down can't you see where everyone is sitting Fulani ce ta daga Mata hannu tana cewa karaso nan kusa dani jikata zo nan naji duminki ahankali ta tashi ta karasa kujerar grandma dinta ta zauna kusa da ita cikin so da kauna da kuma tuno danta ta share kwallar data cika Mata Ido meysa bakyason zama cikinmu marin mai sa baza ki dawo kusa dani ba in diga ganinki ina jin dadi b..... tana kaiwa nan tafashe da kuka ahankali mahreen ta dafata don't worry granny I will think about it stop crying tafada tana dan bubbuga bayanta saida tayi shuru sannan ta kalli Ayman daya zuba masu Ido Ayman wanna itace kanwar ku wadda aka kashe iyayenta da yayanta shekaru kusan uku kenan nasan ba lalle kunsan juna ba itace yar ishaq wan mahaifinka sunanta marin , mahreen ne ba marin ba, ke ni rabani wannan sunan bansan Inda iyayen ki suka samo suka makala maki ba suna sai kace daga duniyar aljanu duk dariya sukayi banda mahreen data murmusa kawai sun dade kafin tace su shiga su gaisa da iyalan abdul hameed kafin su wuce, tare da Ayman suka fita shi zai rakasu parts din iyalan abdul hameed part din uwargidan suka fara shiga ta karbesu hannu bibbiyu tana Kara yiwa mahreen gaisuwa har yayanta biyu wanda suka rage basuyi aure ba suka shigo suka gaggaisa tukun suka tashi zasu shiga part din aunty amarya da yake ba tazara sosai yasa a kafa suke tafiya kallo Imran tayi what's Abdul hameed's status in this house and who's he exactly ? he is your grandfather's brother he is the one praising your father's good characters when we were in the palace da sauri ta dago whatt you mean that man he is the brother of my grandfather are you okay Imran ? da mamaki yake kallon ta kafin yace yes he is what wrong with that girgiza Kai tayi cikin rudani tabbas dole ma ta dawo masarautar nan sake juyowa tayi both the part we came from and the one we are heading to are parts of his family's domain ? yeah yace daidai nan suka shiga part din aunty amarya a hakimce suka sameta bayi suna ta mata hidima wasu na yanka mata fruits wasu na Mata tausa karasawa sukayi suka zauna akasa suna gaisheta mahreen kuwa kujera ta haye ta fito da wayarta ta fara latse latse aunty amarya ce ta dago ta kalleta bayin ta sallama sannan tace ke agidanku baa koya maki gaisuwa bane ko kallonta batayi ba balle tasan tana magana keeeee ba magana nake maki ba aunty ummi ce tace mahreen dagowa tayi can't you hear her talking to you, who tace in I don't care tone aunty amarya mana where's she tafada kamar bata gantaba domin tun shigowar ta kallo daya tayiwa matar taji ta tsaneta kamar yadda ta tsani mijinta sabanin mamar su maijidda wato uwar gidan wadda itama a yanzu takejin tsanarta Jin cewa itama matar azzalimin nan ne wanda ya tarwatsa farin cikin ta.

mahreen aunty ummi takira sunanta cikin rashin jin dadin abinda tayi kallon aunty amarya tayi tace evening, "evening din uwarki nace eveni....... Shigowar Abdul hameed ya hana ta karasawa kusa da matarsa ya karasa ya zauna Yana fadin ashe kunshigo nan aunty ummi ce tayi murnushin karfin Hali da fadin eh whl , mahreen da zuciyarta ta taso jin ta zagi mommyn ta , cire spec din idonta tayi ta kalli wanda akace kanin kakanta kuma makashin iyayenta tace tell your wife to get back into her sense sannan ta kalli aunty amarya this is the first and last time you will disrespect one of my parents in front of me, " owooo you are showing me that u lack morals and respect, husna ce ta shigo ta gaishesu sannan ta zauna Baba baki mukayine eh e-h ya fada kamar adan rikice sannan ya nuna mahreen jikar Mai martaba ce kuma yar ishaq Wanda suka rasu shekaru biyu da rabi daya wuce , they died or were killed ta fada a dan tsawace tana binsa da kallo dan ta fara loosing control ,rikicewa yayi eh eh aka kashe su mantawa nayi amma ai dama lokacin su yayi dan daba haka ba baza su mutu ba cike da tausayi husna take kallonta ganin an maidata marainiyar karfi da yaji ko uba ka rasa ya zakaji balle kuma harda uwa da kuma ya yanta Allah sarki may Allah have mercy on their pure soul mahreen may Allah grant them jannah and expose all those involved in their killing, wata muguwar harara iyayen suke aika mata kamar zasu rufeta da duka duk abinda suke mahreen na lura dasu amma tayi kamar bata gani ba kallon husna tayi suka hada Ido alama tai mata da number ta itama sign ta mata na bari su tashi girgiza Kai mahreen tayi sannan ta mike ta karasa wani table karami da aka daura littattafai akai pen ta dauka ta rubuta number ta kananu a yar karamar paper ganin duk sun zuba mata Ido yasa ta yayyaga takardun saita barbaza su akan table din dagowa tayi ta dan wurgawa husna pen din paper data rubuta number ta dauka sannan ta karasa a fakaice ta wurga Mata takardar sannan ta kashe Mata Ido taya ta karbi pen dinta paper tasake yagowa ta koma Inda ta tashi ta zauna ta daura kafa daya Kan daya duk ita suka zubawa Ido wani rubutu tayi sannan ta Mike ta dauki bag dinta aunty ummi let's go, " ohk dama yanzu zamu wuce ta fada tana sauke ajiyar zuciya sallama suka masu mahreen ce taje gaban kujerar su aunty amarya wani kallo take jifansu dashi cike da tsana sannan ta sunkuya kamar zasu hada goshi da aunty amarya I will show you that I lack moral and respect ta fada tana wani kankance idanuwa sannan tafara tafiya ball tayi da mug dinda ke gaban kujerar tasu take ya tarwatse sake juyowa tayi ta kallesu sun zuba Mata Ido in shock kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta kalli mug din dayayi pieces sannan tayi waje anan tayi joining dinsu dan dama basu yi nisa ba Ayman ne yake janta da magana ba komai take amsa masa ba domin yanzu tana bukatar time tayi tunani akan wanna lamarin shiko Imran haushi ne yakama shi saida suka kusa mota ayman yace have you finished studying sister ? yea! which course ? criminal law tabashi amsa a takaice wow I am also a lawyer juyowa tayi daidai lokacin zata shiga mota mika masa wayarta tayi insert ur digits here karba yayi yasa mata sannan yayi flashing awayarsa ya mika mata nata wayar karba tayi ta rufe kofar suka wuce.

YOUNG WRITER

MAHREEN