PAGE 21---30
by @swrites22
MAHER
sai 11pm ya dawo part dinsu ya wuce wanda ya kasance shi da Ayman ne masu mallakin part din a parlour ya sameshi yana ta dube duben littattafai irin nasu na lawyoyi a kujera ya zube yana fidda pistol din da ke bayan wandonsa ya aje akan center table , "kadawo bros Ayman yace yana dagowa , " Bari kawai tun dazu naso dawowa sai kuma mukaje wani investigation kuma har yanzun da nake fada ma ban kammala binciken ba, " wanna aikin anya baya ma yawa kuwa Maher kaje nan kaje can , hmmm kawai yace Ayman kuma ya cigaba da fadin dazu yarinyar uncle ishaq sunzo, " uncle ishaq dai wanda yarasu ? eh dazu sukazo da auntyn ta Kana fita suna shigowa ko itace wata marar kunya mai shade, " dariya ayman yayi dukda baisan me ya hadosu ba amma ya bashi dariya yace kwarai itace amma fa kasan miye bruh yarinyar tana da abin al ajabi da daure Kai bakaga yadda tayiwa grandfa Abdul hameed ba da aunty amarya abin ya dauremin Kai sosai sai kace wasu abokan gabarta Maher daya nutsu yana sauraron sa yace mai tayi tho? kasan dokar gidan nan dama idan dai kaje part din manya to akasa zaka zauna sai Kaine ma da kake karya dokar to ita ma halinku daya yadda baka shiri da aunty amarya itama haka amma kusan nata yayi worst saboda bakaji yadda ta dinga maida masu magana ba bata da tsoro ko kadan.......... nan ya kwashe duk abinda ya faru ya zayyane masa shuru yayi can kuma yace baka tunanin akwai wata a kasa kuwa Ayman nifa inaga haka kawai baza tayi musu haka ba ko dan girmansa a matsayin sa na kanin kakanta , "Nima gsky nayi tunanin hakan amma tunda munyi exchanging numbers sannu a hankali zansan komai kuma tunda ita ta fara neman number na ma kaga kamar tana da magana dani Kenan , mikewa Maher yayi yana daukan bindigar sa yace kamin sending number din ta ta, " ohk yace kawai.
Abangaren aunty amarya da Abdul hameed kuwa mahreen tana fita itama husna ta tashi Dan taje tasa number da mahreen ta rubuta Mata nan tayi Musu Saida safe ta shige , Abdul hameed ne ya juyo Yana fuskantar ta fiddausi munfa kashe maciji ne amma bamu sare kansa ba wani murmushi tayi haba Alhaji muka Kawar da manyanta ma bare ita karamar kwaro karka damu zan sa a kawar mana da ita kawai dan karta kawo mana matsala muji da wa annan biyun ma na wajen Khalid da suka zame mana karfan kafa, husna ta manta da Jakarta a parlourn hakan yasa ta juyo domin dauka taji abinda ya girgiza tunaninta da sauri ta boye bayan labule tareda saurin danna recording Abdul Hamid ne ya cigaba da magana taya hakan zata kasance fiddausi kashe wanna yarinyar fa a yanzu ba karamin aiki bane dan daganin ta tsagera ce batada tsoro nisai nake ganin ma kamar ta gano wani abun , "haba mana Kai kuwa karkabar kanka ya kulle mana Ka barmin komai a hannuna kamanta wace ce ni kenan na dade fa ina doraka a hanya tun wancan lokacin damuka yiwa shi Mari gayi kurciya muka sa akayiwa Khaled allurar poison kuma a karshe Ka Kai shi ishaq din da iyalansa barza u saboda gudun matsala yanzu kuma wanna yar karamar kwaron ce zatasa Ka firgita ai kawai itama binsu zatayi kuma suma wanna Maher din da ayman indai aka kasa daga minsu daga kasarnan to Suma kawai kashesu zansa ayi kaga sarauta dai dole hannun Ka zata dawo wata dariya yasaki shegiya fiddausi akwai brain fa saisa nake sonki kina daurani Kan hanya , husna da tayi Saving din recording dinta wayarta tayi Kara da sauri suka juyo waye anan abdul hameed ya tambaya Yana mikewa haba Alhaji kafiya tsoro fa wayatace tayi Kara kagan ta can ta fada tana nuna masa wayarta dake charge kusa da curtain dinda husna ta buya ajiyar zuciya ya sauke Yana kallon ta ni mamaki nake yadda Ka iya kashe har mutum uku ahakan da wanna shegen tsoron kamar farar kura , baza ki gane bane fa, " amma kasan dai bawanda zai shigo idan ba kiransu nay iba husna kuma ta shiga bacci dan haka Ka kwantar da hankalinka fa .
Tun a mota ta lura Imran sai wani cin magani yake shareshi tayi suna zuwa gida tayi wa aunty ummi sai da safe ta shige daki , bayan ta gama komai ta juya ta kalli nawal dake ta baccinta hankali kwance safa da marwa tafara dan neman mafita har saida ta kamo bakin zaren Amma dole tana da bukatar Karin bincike akai kuma hakan baza ta kasance ba dole saita koma masarauta kuma tajawo husna jikinta dan ta hakan ne zata samu wasu sirrikan Abdul hameed din dan taga kamar yafi san wanna aunty amaryar Ayman ne yafado mata arai shima zai Mata amfani kallon agogon dakin tayi 2:16am gashi gobe zata fara aiki a headquartern su a wanna dare bata samu bacci ba saida tayi sallah asuba tukun bacci ya dauketa 7am daidai alarm dinda tasa yafara ringing tare suka tashi da nawal dayake itama tana service ne a govt secondary school , agurgurje tayi wanka tafito shiryawa tayi cikin jeans black sai t shirt wata jacket ta dauko ash tasauka har Kan guiwarta belt din jacket din ta daura sannan ta gyara gashinta tayi rolling da black veil ta dauki spec dinta da P cap kamar kullum tafita a dinning ta samesu gaba daya harda babansu nawal good morning everyone ta fada tana hada tea saida suka gama breakfast nawal tai musu sallama ta wuce shima baban nasu sallama yayi ya wuce aiki dama shi managern banki ne da wuri yake fita aunty ummi ce ta dauko car keys guda uku ta Mika mata this is for who aunty ummi ? " this is ur inheritance your father left three cars he purchased when you returned to Nigeria , there's also a house in Australia where you lived , I didn't take any action without your input and regarding the money he left in RBA Australia I had Imran transfer it into my account, and the home you lived in before he passed away is still intact, since you are starting work today I decided to hand over the car keys to you as you will need them they are all parked outside , makullin mota daya ta dauka sannan ta juya Imran let's go har ta Kai kofa ta sake juyowa aunty ummi just kept everything with you ohk, gyada Mata Kai tayi wishing you all the best of luck , bye bye ta fada tana yin waje Imran ne yayi wa mahaifiyar tasa sallama ya bi bayanta shiga tasa motar yayi itama ta shiga ta ta suka dau hanya office dinta yafara kaita komai yamata yadda takeso hakan yasa suka wuce headquarter din direct office din sir jibril barau suka wuce dan shine babba awajen suna shiga bayan sun gaisa yace Imran zai iya tafiya itakuma zasuje ayi testing dinta haka yamata sallama ya wuce saida ya wuce sannan sir jibril yace what's your name ma ? mahreen ishaq abdallah, " ke jikar Mai martaba ce ko girgiza Kai tayi yace cousin dinki ma anan headquarter din yake Yana da kokari sosai , cousin dina ta maimaita yes Maher Khalid abdallah taji ya fada ashe a fili tayi maganar bata che masa komaiba Inda sabo ya saba da haka tunda Maher ma haka yake masa wani lokacin in ta motso dukda shine shugaban sa amma haka yake hakuri , mikewa yayi yace let's go jakarta kawai ta dauka tabi shi abaya bayan ta kafa P cap dinta ta rufe rabin fuskarta dashi har suka karasa wajen babba ne cike yake da bindigu da bullets da kuma sauran kayan aiki irin nasu karasawa sukayi wajen wata mata matashiya budurwa daga gani kasan fulani ce gaba da baya rubuce rubuce take tayi gaban table din na kalla miss rabi ah Kabir musa aujara nagani a rubuce mikewa tayi ta sara masa magana yai mata gani nayi ta tashi takarasa wani table din tayiwa wani magana sannan tafita , sir jibril ne ya karaso Inda ta jingina da bango tana danna waya sorry na aika a kirashi ne shi yake tantancewa da bada percentage sannan musan in da zamu ajjeki dagowa tayi ta kalleshi tana dan taunar lips dinta na kasa sannan ta girgiza masa Kai a zuciyarsa kuwa cewa yayi yau Allah ya hadani da miskilar yarinya shigowar Mr Maher da miss rabi ah ne yasa sir jibril barin mahreen ya karasa wajen su Maher ne ya sara masa bayani yafara masa ta gefen Ido yake kallonta ita da tace wa Ayman barrister ce me ya kawota headquarter su ta DSS sir JB ne yakatse masa zancen zucin dayake ta hanyar cewa yanzu sai muje ko da hannu yayi wa miss rabi ah magana cewa tai mata magana su shigo gaba sukayi shida sir JB tare da dayan ma aikacin muje ko miss rabi ah tace dagowa tayi ta kalleta sannan ta sauke kafarta daya daga jikin bangon ta bita duk sun zubo masu Ido bata kalli kowaba saida ta iso kusa dasu tasa hannun ta daga p cap din kadan yadda zata iya kallonsu sosai table din da aka wargaza pistol ya nuna Mata da hannu tafiya tafara kamar bazata taka kasa ba ta karasa duk sun zuba mata Ido jin idonsu na damunta yasa ta maida P cap dinta kamar yadda take dazun pistol din tafara hadawa cikin kwarewa a lokaci kankani ta hada ta tasa bullet sannan ta dan buga ta a table din ta ajje sosai su sir JB suka jinjina mata tabirgesu yadda take hada komai da zafin nama amma kuma a nutse saida yagama rubutun dayake ya dago bindigar yabi da Ido pen din ya buga a lip dinsa kadan kafin ya tabe baki da fadin muje wajan harbi biyosu tayi muryarsa ta tsinta wakika barwa bindigar batabi takan maganarsa ba dan batama dauka da ita yake ban cikin dan jin haushi ya juyo kusan Karo sukayi taja baya cewa nayi ki koma ki dauko bindigar ko dagowa tayi sukayi 4 eyes sorry I don't think dani kake tafada tana komawa dan dauko bindigar bayanta yabi da kallo Yana mamakin ta tunda ta shigo sai yanzu yaji maganarta saida yajira ta karaso sannan ya fara tafiya acan suka samesu karasawa yayi wajen miss rabi ah kije ki nuna Mata Inda zata harba sannan yazuba Mata Ido still wayar take dannawa daya hannun kuma tana dan juya bindigar muje can zaki harba tafiya tafara batare data dago ba, dakin dago Kin maida hankali saboda ki fuskanci abinda zan nuna maki still bata dago ba tace just go on kasa kasa miss rabi ah ta harare ta sannan tace acikin wancan black dot din akeso ki harba three chance ne dake kawai wayar ta kashe ta turata aljihun bayan wandonta sannan ta dan karkatar da p cap din gefe ta saita bindigar batare da jin wani dar ba ta rufe idon ta tasaki bullet din tafin dataji sir JB da dayan mutumin nayi ne yasa ta bude eyes dinta sannan tajuyo tana kallon su sir JB ne yace gsky nadade banga yarinya mai kwazo irinki wadda ta kware sosai ba Masha Allah gsky zaa ja dake juyawa yayi wajen Maher Wanda shima mamakinta ya kara cikashi amma ya boye sai murmushi kawai dayayi kagama rubutawa ne Maher yes sir yace Yana mika masa file din karba yayi yadan duba sannan yace ina ganin she will work under your office as your assistant girgiza masa Kai yayi sannan yace kinyi kokari cousin dinki maher zai nuna maki office dinda zaki zauna gyada masa kai kawai tayi dan itafa baso take yana wani nanata cousin dinnan ba wuccewa sir JB yayi miss rabi ah ma cikin dan jin haushi tayi waje dan komawa wajen zamanta ita taso samun matsayin mahreen saboda shiga jikin Maher amma percentage dinta bai kai ba dayan abokin aikin na sune yace natayaki murna dan murmushi tayi sann tace tnk u shima waje yayi wajen yarage daga ita sai Maher saida yagama kare Mata kallo up and down tanajin yadda eyes dinsa ke yawo ajikinta har saida ta dago suka hada Ido dauke kansa yayi kamar baisan da ita ba ya zaro wayar sa yayi wani katse latse sannan yace biyoni kamar bada ita yake ba har yakai kofa ya juyo yaga tana yadda take mahreeen ya fada cikin jin haushi yarinyar nan tanason samun ciwon Kai dagowa tayi tace yes muje yace binsa tayi suka fita rage tafiya yayi har saida ta karaso ki daga kafa malama aikin mu bana masu iyayi bane in kinsan baza ki iya ba sai zauna matsayin ki ki nemi aikin daya dace da mace ita dai bata ce masa komai ba , ba haka maheer ya so ba don so yayi ya sake jin maganar ta amma ganin bata tanka masa ba sai shima yaja bakin sa ya tsuke har suka shiga office na farko mutum hudune awajen mace daya maza uku mikewa sukayi suna sarawa Maher din da Kai kawai yake amsa masu office na biyu suka shiga babba ne office din kuma zaman mutum biyune table dinsa ne na farko sai na karshe empty .
YOUNG WRITER
MAHREEN