MAHREEN

PAGE 31----40

by @swrites22

Agaban table din ta tsaya tana karewa office din kallo saida ya danyi rubuce rubucensa sannan ya dago a tsaye ya ganta kamar an dasa ta phone dinta take bubbugawa akan lip dinta tana kallon wani wuri have a sit ya fada bata motsa ba ki zauna ya sake fada still bata motsa ba kansa ya dafe ya zuba mata Ido kamar ba zaiyi magana ba yace mahreeen kamar bayaso dagowa tayi idonsu cikin na juna why are you trying to give me a headache , "mee! hararar ta yayi sannan yace akwai wata ne bayan ke sau nawa ina maki magana kinyi shuru sorry I don't think you are talking to me Cox u haven't mention my name zuba mata Ido yayi dan ji yayi kamar ya maketa saboda haushi adan tsawace yace nace ki zauna ko kika min tsaye a Ka bata rai tayi ba a min tsawa Maher really ya fada yana juyi akan kujerar sa I'm your superior here not ur cousin you don't have the right to address me informally kujera taja ta zauna ba tare datace komai ba shuru office din yayi na dan wani lokaci sannan yace your name batare data kalleshi ba tace mahreen ishaq abdallah sunan ya maimaita har saida ta dago suka hada Ido ta dauke kanta meya kawoki nan , kallon Ka raina min hankali ta watsa masa kafin tace aiki , "ke ba law kika karanta ba meye hadinki da hukumar DSS ba tare data tambayeshi ya akayi yasan ita lawyer bace ta bashi amsa da I earned both my first degree in law and my masters degree in defence and security studies, how old are you ? This question is not relevant here ta fada tana daure fuska kamar wadda aka aikowa da mutuwa , tabe baki yayi tare da dage kafada irin I don't care din nan sannan yace wancan shine part dinki a office din nan and wancan toilet ne yana gaba fada ta mike zata fara tafiya cikin fada fada yace did I ask u to go I haven't finished juyowa tayi cikin masifa itama I have told you before don't shout at me I'm not your daughter although I will work under you, that doesn't give you the right to control me , I also want to remind you that I'm not going to work here permanently hope you Gerrit Ido cikin Ido suke kallon juna idonsa ya maida Kan hannun ta data matse spec dinta sosai kamar zata balle shi saboda masifa sannan ya sake dubanta juyawa tayi tafara tafiya yace mahreen kamar baza ta tsaya ba sai kuma dai ta tsaya ba tare data juyo ba tace lemme be. shuru yayi yana nazarin yarinyar there's something peculiar about her I need to know more about her.

Tana fita taciro p cap dinta ajaka ta saka sannan tayi waje can wani waje data ga da kujeru karkashin wata bishiya nan ta karasa ta zauna ,duniyar tunani ta fada dole ta nemi mafita indai haka aikin nan yake dole tafara aiwatar da aikinta tun wuri ta rabu da wanna jarabar dan baza ta zauna mutum yana bat umarni ba kamar ubanta saida taji zuciyar ta tayi sanyi sannan ta tashi ta koma yaji shigowarta amma bai dago ba wucewa tayi Inda yace part dinta ne ta zauna kafarta ta dora kan table din sannan tafito da wayarta Kiran husna tayi suka gaisa ahankali take maganar har suka gama , dagowa yayi ya zuba Mata Ido kafar yabi da kallo kamar bata taka kasa sannan ya maida kallon sa gareta dole yasan komai da wurwuri domin take taken yayi yawa to me ma yakawota nan kuma mai take taqama dashi da har take irin wanna abubuwan, sarauta wata zuciyar taba shi amsa to ai shima jikan sarkin ne meysa sai ita yasan idan yace kiranta zaiyi wata sabuwar rigimar ce shi kuma baya son surutu da yawa pistol ya dauko sabuwa a drawer office din ya hada mata komai ya cikata da bullet sannan ya nufi table dinta a kujerar gaban table din ya zauna ya dora bindigar Kan table din dagowa tayi taga kafarta yake kallo saukewa tayi tana cigaba da abinda take dauki yace yana mata nuni da bindigar dan tura kujerar baya tayi sannan ta bude locker dake gaban table dinda kafa dan yatsa tasa ta dago bindigar ta wurga cikin locker din hmmm ya sauke wata boyayyar ajiyar zuciyar sannan yace ba anan nace ki ajje taba ki dauka ki tafi da ita gida taki ce amma kiyi taking care, okay tace kawai a ina kikayi karatu wanne daga ciki tabashi amsa both Australia and Russia why did u assume you wouldn't work here permanently ? Cox that's not my ambition , " and why do you choose it right now ? this is my personal plan and it's none of your concern baice komai ba yayi shuru can kuma yace there's a case I'd like your help with , come over when you are ready to hear the details ya fada Yana tashi ya koma Kan table dinsa saida tadau wasu lokuta ya ma dauka baza tazo ba sannan ta tashi ta karasa bayani ya fara mata sosai ta nutsu take sauraran sa har ya gama bayanin sannan ya mika mata file din mikewa tayi ina fatan kin fahimta yea and I will go through the information again good ya fada ita kuma ta wuce.

1:30pm ya shiga yayi alwala sannan ya fita yayi sallah Inda ya barta nan ya sameta ke bakya sallah ne ya fada , Bani da hijabi saida ya harari kayan jikinta sannan ya zauna waya ya dauka yayi dan danne danne sannan ya ajje kusan 30 minutes miss rabi ah ta shigo sai falli take rike da wata leda a hannun ta gashi sir ta fada pointing mahreen yayi da hannu miqa Mata karasawa tayi tace gashi from where ta tambaya sir Maher kallon sa tayi taga hankalin sa ma baya kansu okay thanks tace ita kuma ta wuce tana hararar ta budewa tayi taga jilbab ne aciki black colour tashi tayi tayo alwala sannan ta dau pray mat dinda ta gani ta saka hijabin ta tada sallah koda ta idar saida tayi addu a wa iyayenta da ya yanta sannan ta mike come and take your lunch kallon table din tayi leda biyu ta gani iri daya I'm not starving , bai sake cemata Kala ba ta cire hijabin ta linke ta maida a ledar sannan ta linke pray mat din ma ta maida Inda ta dauko abubuwanta ta hada a jaka ta saka p cap dinta ta gado ta dauki key din motarta sannan ta dauki wanna file din daya bata tayi hanyar waje where are you going wrist watch dinta ta duba it's almost 3 , and so , " I'm going to my office , office ya nanata yana dagowa yeah I'm going to our chamber whom do you ask for permission maimakon ta amsa masa saita maida masa tambayar what's your closing time ? I'm the one asking the question here not you dan yatsina fuska tayi I'm leaving now set your questions aside I'm going with or without permission and that's final, " do u know our rules ? They are for those staying long term tana gama fadar haka tayi waje wayar sa ya jawo ya rubuta message ya tura Kira ne ya shigo wayar da dagawa yayi da fadin yeah ita tare da katse Kiran.

Tana fita chamber su ta nufa saida ta nutsu tabi baya nan dake cikin file din da ya bata daki daki sannan ta tsunduma kogin tunanin yadda zatayi gaskiya ta bayyana tabbas tasan Abdul hameed shine makashin iyayenta but a yanzu bata da evidence dole ta shiga jikin ya yansa dake gidan da haka ta yanke shawarar zuwa gida domin ta shirya ta koma masarauta tana samun baya nan data keso zata bar can din .

Aunty ummi ta nuna rashin amincewarta da komawar mahreen can din amma dole dole ta tada bori akan sai taje haka ta barta amma da sharadin ba gaba daya ta koma ba murmushi tayi kawai tare da girgiza mata Kai Imran ya shiga rudani saboda barin mahreen gidansu badan komai ba sai dan shishshige matan da ayman yake yi amma ba yadda zaiyi ya san tunda tace sai taje sai taje din haka ta har hada duk abinda ta san zata bukata sannan ta nemi aunty ummi tai mata transfer wasu kudade a acc dinta.

Komawarta masarauta kamar a kunnen Abdul hameed aunty amarya kuwa cewa tayi abu yazo da sauki husna ta shiga rudani sosai baza ta sake bari akashe mahreen ba saboda tasan itama Allah saiya kamata da laifin boyewa datayi tunda har da saninta.

TWO WEEKS LATER

Mahreen ce ta dawo daga aiki tana garden sai Ayman dake gefenta yana bata labarin wani case da suke shari'a a kai husna ta shigo wurin taji dadin zuwanta sosai dama jira take ta gama da wani abu tukun ta neme ta sai kuma gata kallon Ayman tayi da fadin Ayman excuse me please Ohk yace yana tashi ya basu wuri gaisawa sukayi husna ce tace mahreen mai sa kika dawo masarautar nan ? Ai gwara dana dawo ba gani cikin family na ba ko ya kikaga ta fada tana nazartar yanayin husnan, amma ni ina ga gidan aunty ummi yafi masarautar nan dadi kinga sai ki dinga kawo mana ziyara , " bakwa maraba da dawowa ta Kenan ? a a whl ko daya , to maisa kikace haka ? kawai saboda naga masarautar ba wani dadi bane da ita gashi zakiyi kadaici , " to ba ga ku ba murmushin yaqe husna tayi bata sake cewa komai ba sai mahreen da tace ni dama I want to ask you for your dad number inaso nazo muyi dinner ta musamman da kakana , "ba -ba baba wai ta fada cikin rawar murya tsayawa tayi tana kallon ta ganin yadda tarikice eh mana da problem ne ? no babu komai mika mata wayarta tayi tasa mata sai kuma ta tashi tai Mata sallama saidai kuma takasa tafiya sai tayi gaba saita dawo baya ita dai mahreen ta zuba mata Ido har ta fice girgiza Kai tayi tabbas husna ta san wani abu amma maysa tace tabar gidan haka taita tufka tana warwarewa har akayi magrip ta tashi ta shiga saida tayi sallar Isha sannan ta tashi ta shirya domin fara aiwatar da aikin da Maher ya wakilta ta akai cikin shigarta ta kullum cikin kananan Kaya tasa p cap tareda face mask ta dauki duk abun bukatarta ta jefa a jaka sannan ta fita granny tasamu da hadiman ta barka da hutawa tai mata sannan tayi hanyar waje kiranta tayi marin juyowa tayi , amma kinsan nan gidan sarauta ne ko irin wanna shiga bai kamata ba kina jikar sarki inata so nai maki magana ina mantawa amma hakan bai dace ba, in sha allah zan gyara ta fada tana yin waje motarta ta shiga tana kokarin tada wa text ya shigo wayar ta da wata bakuwar number good luck take care of yourself kaman ya Kenan waye ke bibiyarta ? Ya akayi aka san zata ? number ta dannawa Kira dauka akayi amma ba ayi magana ba hakan ya darsa mata shakku Kenan akwai mai bibiyar rayuwar ta tunda har akasan zata fita kuma aiki zata je yi bude kofar motar tayi da niyyar fasa fitar a yau din wani text dinne ya sake shigowa just go don't worry I'm sure you are curious about who I am but time will reveal that, number tabi da kallo special number ne komawa tayi kamar yadda ya rubuto amma ta kasa tafiya zuciyar ta na cikin fargaba can kuma ta tada motar ta fita sai dai kuma tunda ta fita ta lura da masu binta abaya zuciyar tace ta bata akwai Wanda yake son cutar da ita kuma hankalin ta yafi bata wanda ya turo Mata text ne ya akayi tabi abinda suka rubuto meysa bata fasa fitar ba duka ta kaiwa steering tare da take motar a 360 nan suma suka Kara wuta amma sun kasa kamota harta karasa restaurant din da zataje wayarta ce tayi Kara number husna ta gani dauka tayi cikin muryar kuka tafara hello hello mahreen kina jina yes husna what's going on why are you crying ? "where are you right now husna ta tambaya sunan wani restaurant ta fada daban a maimakon wanda take mahreen stay where u re , your life is in danger they are hunting for you , " who are they? There's no time just do as I say we will discuss later , ohk tace tunanin ta duk ya curkude tarasa Inda ma zata kamo wayar husna yasa zaren data kamo zamewa kwata kwata ta rasa waza ta alakanta da hakan ajje wayar tayi sannan tazaro wata a jakarta , Kira tayi da ita banji me akace mata ba naji tace ohk sannan takashe wani abu ta fito dashi a jakar ta makala a wanna wayar sannan ta dauki Jakar ta ta fito wurin wani table da wani mutum ke zaune ta nufa magana suke kasa kasa dana kasa jin me suke cewa saida mutumin ya gama sañnan tafito da wani abu a leda ta mika masa tashi yayi ya tafi wayar data boye akasan table din ta fito da ita tadanna wani abu sannan ta jefata jaka , wata yar paper ta dauko tayi dan rubutu sannan ta tashi tare da nufar wani service daya dauko tray da wasu sukayi order zai kawo masu kamar bata sani ba ta Kara waya a kunne bangajeshi tayi tray hannun sa ne ya fadi Wanda ya jawo kusan rabin hankalin mutanan wajen p cap dinta ta sake gyarawa sannan ta durkusa kusa da service dinda ya fara masifa yana tattare kayan magana tai masa a hankali sannan ta wurga masa takardar a fakaice mikewa tayi kamar gaske tana bashi hakuri kudi tafito dashi a hand bag dinta ta Mika masa sannan tafita mota ta shiga tana sauke ajiyar zuciya maganar husna ce ta dawo Mata a kai Kiran Imran tayi bugu daya ya daga Lilly how far Kana ina ta tambaya ansa Mata yayi jin yana kusa da restaurant din yasa tace ya karaso kamar zaice mai taje yi restaurant da daren nan sai kuma yayi shuru 10 minutes tsakani ya karaso Kara gyara parking din motarta tayi sannan ta dauki komai nata ta fito motarsa ta shige da fadin muje , " Inaaa ? ya tambaya Yana kallon ta da mamaki , masarauta, motar taki fa ? don't worry I will send someone to pick it up in the morning Kiran husna ne yasake shigowa bata daga ba ta tura Mata text I'm safe don't worry suna fita taga motar data biyota dazu number motar ta dauke sannan ta dauko karamin jotter a jaka ta rubuta what brings you here tonight ? my work tace a takaice, mahreen your work takes too much of your time, you should be with your family at this hour, this job doesn't deserve someone as valuable as you daga masa hannu tayi is okay Imran bai Kara cemata komai ba har suka karasa masarauta ya sauke ta a kofar part din granny tnk u bruh good night my warmest regards to aunty ummi and nawal in sha allah tomorrow I will pay a visit to them murmushi yasakar Mata sannan yace good night sweet dreams we will expect you girgiza masa Kai tayi sannan ta wuce.

YOUNG WRITER

MAHREEN