PAGE 41----50
by @swrites22
Tana tashi ta shirya drivern part din granny tasa ya dauko mata motarta yau chamber su zata fara zuwa cikin shigar ta ta kullum amma yau an samu arziqin daura kimono a kai ringing din wayarta ne ya dame ta dagawa tayi hello husna daga dayan bangaren husna da jiya batayi bacci ba ta sauke ajiyar zuciyar mahreen kina lpy alhamdulillah , Dan Allah if u won't mind ina son ganinki , " nima ina son ganinki amma sai na dawo zan kiraki okay take care sallama sukayi duk abinda take bukata ta hada sannan ta wuce chamber su .
Ayman ne ya sameta a can shi da wani tsoho wanda aka cuceshi kuma ake masa barazana da rayuwarsa kusan shekara hudu suke ta faman shari'a da mutanan wanda suka kasance yan uba ne gareshi har duk abinda yake dashi ya Kare har takai bashi da halin daukan lawyer a yanzu gashi kuma ya sake shigar da Kara , kallonsu ayman din tayi nifa bana minor case irin wanna mutumin ne yace yarinya ki taimaka min dan girman allah da ma aikinsa , "ohk shikenan cigaba da bayanin Ka inaji saida suka gama Mata bayani sannan tace yaushe ne hawa court din Ayman ne yace jibi wani court ne ? higher court, what time? 9:00am, Ohk karka damu zan tsaya ganin na kwato ma hakkinka in sha allah, nagode yar nan Allah ya miki Albarka yasa ki gama da duniya lpy ameen tace sannan suka Mata sallama suka tafi.
Wayarta da tun dazu take haske ta dauka hello kina ina ? office di na ta bashi amsa a takaice jim Maher yayi baza kizo aiki bane ko yaya? later tace sannan ta kashe wayar duk bayanan case din daya bata ta hada sannan ta kulle office din ta fita.
Tana shiga gaban table dinsa ta karasa noon tace kawai, " sai yanzu kikaga daman zuwa, a dan gajiye tace this is not your concern , I have plenty to handle gashi duk wani information dazaka bukata suna ciki file din wani abu mai kama da memory ta dauko a jakarta ta mika masa saida ya gama dubawa ya dago yana kallonta kafin yayi magana wayar ta tayi Kara amsawa tayi da fadin let's meet in Marshad delight kawai tace ta kashe wayar dagowa tayi idon ta ya shige cikin sexy eyes din sa da yake jifanta da wani narkakken kallon da ya riqe idonta kamar magnet shine ya fara dauke nasa da fadin you try, mikewa tayi yace ina zuwa kuma ? Ba tare data kalleshi ba tace I told u I have plenty to handle if I finish before 5 I will be back ta karashe tana ficewa, wayarsa dake haske ya dauka hello! ohk inaga mu hadu kawai a aiden palace by 4 , Ohk hakan ma yayi naji ance ta daya bangaren sannan ya kashe.
Tana fita Inda tace wa husna zasu hadu ta nufa acan ta sameta sanye da niqab a fuskarta karasawa tayi suka zauna bayan sun gaisa husna ce tayi jim sai kuma tace mahreen bazan yafewa kaina ba idan wani abu ya sameki dukda nasan nima a yanzu rayuwa ta tana cikin hadari k........nan takwashe duk abinda tasani ta fada Mata sañnan ta dora da fadin da safe na samu mama da Baba na nuna masu duk nasan sirrin su kuma idan har sukayi yunkurin kasheki zan tona masu asiri kuma inada evidence ta hanyar recording din duk abinda suke aikatawa yanzu kuma kafin na fito naji mama na waya da thugs dinta tace kosu san yadda zasuyi su samu abinda nayi recording secret dinsu ko kuma su kasheni K.a k..awai amma.a ka.rsu ba.r alamar dazaa gane itaaa.ce. ta karashe tana mai fashewa da kuka wanna wace irin rayuwace akan san abun duniya da sarauta zata iya sawa a hallaka yar ta kwaya daya ni harna fara kokwanto anya kuwa mama ce ta haifan ganin kowani lokaci zasu iya kawomin hari kuma bansan ya Shirin nasu zai kasance ba yasa na matsa maki mu hadu a waje ga wanna memory din nayi copyn komai kije kisa zakiji komai, nisawa tayi duk jikinta ya mata wani irin nauyi wanna wace irin rayuwa muke ciki ne kiyi hakuri husna Amma bazan bari ki koma gida ke kadai ba ame kikazo ? silalewa nayi na fito ban dauki mota ba saboda Kar a ankara nafito daga idon da zatayi taga wani daga can karshe kuma da alama su yake dauka awaya ganin sun hada Ido yasa ya mike da sauri zai bar wajen itama da sauri ta tashi ta bishi tana cewa husna ina zuwa tana fita yana shiga mota number motar ta kalla kawai ta shaida itace wadda aka bita da ita jiya da sauri ta karasa tace wa husna ta tashi da sauri .
mota suka shiga tana yi tana kallon bayansu ganin ba Wanda yake binsu yasa ta sake komawa chamber su acan ta saka memoryn a system saida ta saurari komai sannan ta bude photo guda daya wanda ya kasance mutum uku ne a ciki Abdul hameed sai aunty amarya da chiroma jin ashe ba ita kadai sukayiwa illa ba harda mahaifin su ayman amma ita sunfi mata illa tunda kashe mata nata akayi idonta ne ya cika da kwalla wadda rabon da tayi wani Abu Mai kama da kuka tun data daga ta bar kasar kujerar ta juya sai kuma ta mike da sauri ta shige toilet.
sai kusan 5:45pm sannan suka fito daga chamber ta lura area wajen kamar akwai matsala ganin irin motar dai da ake bibiyarta da ita tayi parking a kusa da chamber ta yadda Kana fitowa idan Kayi left zaka gansu tsayawa ta danyi kadan da mota har husna nace mata lpy wani mutum taga yana waya kuma yana waige waige kamar bashi da gaskiya tsallaken titin kuma wani shoe Maker ta gani ya zubawa motarsu Ido da matsala tacewa husna tana me cire pin din veil din ta dan wani gumi taji ya karyo mata dukda sanyi AC motar , " matsala kuma maiya faru ? sun san kina tare da ni saisa suka turo wanda zasuyi monitoring din mu, " na shiga uku shikenan husna ta fada tana fashewa da wani marayan kuka , " calm down husna ta fada tana reverse ta canja hanya saidai ba tayi nisa ba taga mota har biyu suna binsu abaya.
Abangaren Maher 4pm tana yi ya karasa Aiden palace saida yayi reserving gaba daya wajen Sañnan ya jira mutanen suka gama fita ,wanda zasu hadu dashi ya jira sannan suka shiga tare saida ya gama bashi bayanan gaba daya umarni ya masa da hannu dayaje kawai tunani ya fada lalle dole mahreen ta shiga wani hali shi kansa da halin da mahaifinsa yake ciki da yadda rayuwarsu ta juya yakejin kamar duk duniya su kadai aka tsana ballanta na ita da aka kashe mata uwa a gabanta aka kashe mata uba a gabanta sannan aka kashe yayanta shima a gabanta wani irin tausayinta yaji yana ratsa duka jijiyoyin jikinsa daga waya yayi kamar zai kirata saiga kiranta ya shigo kallon Kiran ya tsaya yi cikin mamaki har ya katse sake shigowar wani kiran ya dawo dashi hankalin sa dagawa yayi yajiyo muryar ta a rude tana fadin hello Maher kanaji na saida ya lumshe idanun sa saboda yadda zuciyar sa ta buga da karfi kamar zata faso kirjin sa lip dinsa na kasa ya kamo ya tsotsa kadan sannan yace inaji, kana Inaaa? Aiden palace, ohk ta fada tana kashe wayar takarawa motar gudu map din motar take bi harta karasa Inda ya fada mata motocin dake binsu taga sun Karu wajen four gashi kuma duhun gabatowar magrip har ya fara, motar taso shigewa da ita ciki securities din suka hana da cewa ba wanda zai shiga saboda anyi reserving wurin jakarta ta dauka kawai tace wa husna let's go fita sukayi cikin zafin nama amma still sun hanasu shiga gefen rigarta ta daga bindiga ta bayyana sannan ta nuna musu ID din ta ba shiri suka basu hanya husna kam ba karamin tsorata tayi ba da ganin bindiga a jikin mahreen da dan gudu ta shiga tana jujjuyawa dan neman maher ganin ba kowa awajen .
tunda suka shigo yake kollonta sunan ta ya Kira ganin tana kokarin yin wani wurin ba tare data Lura dashi ba kamar ma baa hankalin ta take ba juyawa tayi tana ganinsa ta karasa tana da gudu tana haki mikewa yayi husna da tsoro yagama cikata sai kuka take, duk da shima ya dan shiga rudu da yanayin daya ganta amma dake gwarzon namiji ne take ya shanye a nutse ya shiga tambayar su menene ? Jakarta ta bude ta dauko memoryn data nannade awata takarda ta mika masa akwai matsala keep this memory with you, meysa ? harbi sukaji da sauri ya dauki memoryn yasa a wallet dinsa sannan yasa a aljihu su waye suka biyoku bullet aka harbo daidai sashin mahreen cikin zafin nama ya fisgota bullet din ya samu bango dagowa tayi taja hannun husna da gudu sukayi bayan wajen can wani lungu tace ta buya karta fito har sai ta dawo sannan ta fita tana dauko bindigar ta kafar wani ta hango ta kasa Maher daya karaso wajenta da sauri tace duk wanda Ka gani Ka harba amma bata yadda zai mutu ba tana gama fada ta kwanta kasa ta saita kafar mutumin ta harba Maher da tuni shima yabar wajen ihun da wanna wanda mahreen ta harba yasa sauran fitowa gadan gadan suka bude wuta fafatawa aka shigayi tsakanin su har sukai nasarar harbinsu gaba daya kafa da hannu .
A gajiye mahreen ta shiga sauke numfashi wani harsashin aka Kara harbowa saitin Maher da yake kokarin sawa bindigar sa bullet da wani irin gudu ta karasa gareshi tare da hankade shi da karfi bullet din kuma ya samu hannunta Kara ta saki daidai nan mutumin ya fito zai fice Maher da yaji ihun mahreen kamar an buga masa guduma a tsakiyar ka sakar masa harbi yayi take nan ya sameshi a ciki da sauri ya karasa wajen mahreen ya riko hannun ganin yadda jini ya wanketa nan take ciki hanzari ya miqar da ita yana kwala mata Kira a kunne ganin tana neman suma daukarta yayi ya dorata Kan kujera sannan ya dauko ruwa ya juye mata a fuska duk ya rude bude idonta tayi daya mata ja saboda azaba hus..na hu...snaa, tana ina ? hanyar data boyeta ta nuna masa sai yayi gaba sai ya dawo murmushi tai masa cike da karfin hali sannan ta maida kanta Kan table din yana zuwa ya hangota ta takure tana kuka muje muje kawai ya fada yana juyowa tabiyo bayanshi a sume suka sameta bai jira wata wata ba ya sureta yayi mota husna tabi bayansa da gudu tana kuka rike da jakarsu .
A Mota ya kira yaransa na wajen aiki cewa suje su dauko wadanda suka harba sumusu treatment amma su tsare su saiyazo, direct hospital dinda yake aiki ya nufa da ita bai jira ankawo wani gado ba ya dauketa a hannunsa yayi ciki da ita husna na binsu taimakon gaggawa aka fara bata kwata kwata ya kasa ta buka komai ganin hakan yasa sauran doctors din sukace yaje waje ya jira, fita yayi ya jingina da kofar dakin husna ce ta taso tana tambayar sa mai ya sameta baice mata komai ba ya kalli hannun sa da kayansa daya baci da jini toilet ya karasa ya wanke hannun nasa sannan ya dawo kofar dakin yana safa da marwa wani tashin hankali yake ciki wanda rabonsa da shiga irinsa har ya manta bazai jure wani abu yasa meta ba ta sanadiyyar sa ba wanda ya taba masa irin wanna sadaukarwar ta gwammaci ta mutu a kan shi wani abu ya sameshi wani irin sarawa kansa yayi har saida ya dafe shi why mahreen why why wani irin abu yaji tun daga kafarsa har tsakiyar kansa game da ita ajiyar zuciya ya sauke yana daidaita nutsuwar sa tare da bude dakin ya shige.
Saida akayi sallar Isha tukun ta farfado allurar bacci suka mata sañnan suka jona mata Karin ruwa suka fito ganin kallon da Maher din yake musu yasa doctor rukayya yin murmushi da fadin Kai doctor maher kai da kake farde mutane ma Ka dinke amma wanna duk Ka bi Ka rude cire bullet kawai kodai itace amaryar ta mu bai bi ta kan zance nata ba yace me ake ciki , munyi aiki an cire bullet din kamar yadda ka gani anyi saa ai bai fito ta barin hannun ba munyi mata dinki amma tana bukatar hutu sosai in sha allah ba wata matsala boyayyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya koma dakin , husna dake rakube kamar marainiya ta taso tana tambayar doctor rukayya abinda ta fadawa Maher Shi ta fada mata zan iya shiga husna ta tambaya eh amma ba ason hayaniya tana bukatar hutu to tace sannan ta tura kofar ta shiga.
YOUNG WRITER
MAHREEN