PAGE 51---60
by @swrites22
Daidai kanta ya tsaya yana kallon fuskarta da tayi fayau drip din ya kalla sannan ya dago daya hannun wadda aka nade da Bandage ya hada da nasa ya zuba mata Ido har husna ta karaso dan nesa ta tsaya , karaso yace yana zare hannun sa daga nata sannan ya juyo wajen husna muje office muyi magana sai ki dawo ya fada yana fita binsa tayi har suka shiga office dinsa sannan ya zauna itama ya nuna mata wajen zama.
Meya faru daku? tsaf ta fada masa komai takara da cewa idan ya samu lokaci ya saka zaiji komai cikin jimami ya dauki waya security guda biyu ya bukaci suzo sannan yace mata ta zauna a dakin mahreen karta fita ko ina wayar mahreen dake jakarta ce take ta Kara daukowa tayi taga missed call din aunty ummi ne kusan hudu saina Imran biyu, Kiran ne ya sake shigowa , hannun ya Mika Mata wayar ta bashi amsawa yayi da sallama dan Allah ina mai wayar ? tana hospital tazo wucewa ne rikici ya ritsa da ita har aka harbeta a hannu ya samu kansa da fadawa aunty ummi din, Innalillahi wa Inna ilaihir Raju un wani hospital din sunan asibitin ya fada mata sannan ya tashi yana mikawa husna wayar dakin suka koma shi da husnan har saida securities din daya Kira sukazo sannan ya cewa husna kinji abinda nace maki ai kuma karkiyi zancen da kowa ko dalilin daya sa har muka zo nan sannan ki kirasu kice su taho Mata da Kaya yana gama fadar haka yayi waje.
masaurauta ya nufa ya shige part dinsu ba kowa hakan yasa ya shige dakinsa memory ya ciro sannan ya karasa karshen dakin labule ya yaye sannan ya Danna wasu numbobi dakin sirrin sa ne ya bayyana kamar wani office shiga yayi ya zauna tare da jawo system din ya kunna ganin ba chargy sosai ya sashi maqala chargy sannan ya saka memory din ya fice kofar ta rufe da kanta kayan jikinsa ya rage sannan ya fada toilet ya sakar wa kansa ruwa ko da ya fito kitchen ya shiga ya hada tea domin shi cewa yayi baya san wani bayi ko masu hidima saboda bayason hayani da yawan magana marar dalili sama ya koma direct dakin sirrin sa ya koma sosai ya nutsu yanajin abinda ke cikin memory kafin ya gamaji tuni jijiyoyin kansa sunyi rau rau he can't believe this baba Abdul hameed shine sanadin rashin lapiyar mahaifinsa wajen hoto ya shiga Abdul hameed da aunty amarya sai chiroma sune suka bayyana zooming din hoton chiroma yayi lalle da akace makashinka yana tare da Kai bai yadda ba sai yanzu chiroma daya kasance na jikin abbansa tun a wancan lokacin kenan ma dashi aka hada baki aka sawa abbansa guba yaci rufe system din yayi yana dafe kansa dake barazanar rabewa biyu Wanda ba tantama migraine dinsa ne ya motso tashi yayi ya fita daga dakin sirrin ya koma dakinsa locker dinsa ya bude ya dako wani magani guda biyu ya jefa a bakin sa sannan ya jingina da wardrobe ya dage kansa sama komai ya tsaya masa chak daren ranar ko bacci barawo bai iya sace shi ba .
Aunty ummi da nawal da Imran wanda hankalin sa yafi na kowa tashi jin abinda aunty ummi tace ya faru da mahreen din dan shi yasan kawai sun boye ne amma watakil aiki suka fita aka harbeta dole ne idan ta nutsu yasan nayi shi dama wanna aiki ba sansa yake ba kwata kwata bai dace da ya mace ba a haka sukaje suka dubata da yake securities dinda Maher ya ajje basa cikin uniform saisa su aunty ummi basu lura dasu ba suka shiga, nawal da husna suka bari awajen ta sannan suka tafi da cewa inta farka nawal takira su .
kadan kadan nawal da husna ke hira saboda rashin sabo dan ma nawal akwai dan surutu har dare ya raba nawal ta hau doguwar kujerar dake wajen ta kwanta ita kuma husna ta dauro alwala ta shimfida dan kwalinta ta fara sallah har saida akayi asuba sannan taga mahreen ta fara motsawa tashi tayi ta karasa kusa da ita tana Kiran sunanta a hankali.
kadan kadan take bude idonta har ta bude su gaba daya akan husna kokarin mikewa take ta taimaka Mata ta zauna, sannu take ta mata daga Kai tayi ta kalli drip din da aka Kara sawa dazu hannun tasa ta cire sannan ta rufe wajen cannula din why do you remove it mahreen ? I'm going to take a shower , but dakin bari.... Shiii ta fada tana kokarin sauka kasa hannun ta fama ahhh ta fada tana rutse Ido kiyi ahankali fa saisa nace dakin bar wankan yanzu saboda Kar ki jiqa hannun karasa sauka tayi idonta akan nawal data farka tana kallonsu mahreen kin tashi sannu murmushi tayi who told you I'm in the hospital ? whl we have been trying to reach you but you weren't answering at the end someone picked up and told us you were in the hospital kallon husna tayi ita kuma tayi saurin fadin doctor Maher ne , doctor Maher ta maimaita ha a mai kuma ya hadashi da doctor shida yake hukumar DSS ikon allah sharewa tayi da fadin nawal kun kawomin kayane ? eh gasu can miko min husna ta fada tana wucewa toilet din .
Saida tayi wanka tai brush ta shirya cikin skirt da riga English wear hijabin husna ta karba ta rama sallar magriba da Isha sannan tayi asuba ta koma gadon ta kwanta dan har yanzu jikinta ba karfi tunanin abubuwa dayawa take har doctor rukayya ta shigo da yake itace da night duty ya jiki tai mata sañnan tai mata yan tambayoyi ta maida mata drip din hannun ta sake dubawa nurse dinda take bayanta tace ta canja mata bandage din sannan ta juya wajen su nawal karta dau abu Mai nauyi da hannun saboda dinkin da akayi sannan ta musu sallama tafita, aunty ummi nawal takira ta hada ta da mahreen din taji muryar ta kamar yadda ta bukata idan har mahreen din tatashi.
9:00am daidai aunty ummi da Imran suka shigo da breakfast a hannunsu , bayan sun duba ta aunty ummi ta juya wajen su nawal sannan tace idan Imran zai wuce kije gida kiyi wanka yaso da rana saiki taho da lunch husna kema ya kamata kije gida ki huta ko, mahreen ce tace a a aunty ummi husna is not going anywhere , to ai mahreen She has to go home, take a bath, change her clothes and come back ko , "she will do it all here aunty ummi dai bata Kara cewa komai ba ta nemi guri ta zauna , Imran daya tsaya bangaren da mahreen take yace Lilly juyowa tayi suna kallon kallo ya akayi hakan ta faru ya fada kasa kasa yadda ita kadai zataji kafin tace wani Abu Maher ya shigo kamshin turaren sa na imperial majesty ne ya fara musu sallama yayi kyau cikin kananan kaya dark brown suit sai ta ciki light brown bai daura rigar suit din ba tana riqe a daya hannun sa daya hannun kuma waya ce riqe ya Kara ta a kunne da alama wata magana yake Mai mahimmanci gashin kansa da sajen kawai abin kallo ne saboda tsaruwar su da kuma kulawar da suke samu bayansa kuwa wani mutum ne rike da warmers din breakfast tun da ya bude kofar dakin hankali ya dawo kansa take kwarjinin sa ya cika wurin takun sa kuwa ba mace ba ko namiji dole ya kalla ya waiwaya domin ya san maza sun iso da hannun ya nunawa mutumin dake bayansa kan ya ajje basket din ya fita takaita wayar yayi sannan ya kashe fuskar ba yabo ba fallasa ya gaisa da aunty ummi sannan su husna suka gaisheshi Imran ne ya mika masa hannu sukai Musabaha sannan ya kalli mahreen da tunda ya shigo ta kasa dauke idon ta a kansa sai taga kamar ya canja mata ma hannun ta mai bandage ya kamo yana dubawa wani abu ne ya taso ya tokare Imran a wuya, "kinyi breakfast ya tambaya girgiza masa Kai tayi juyawa yayi wajen husna zuba mata tea da breakfast ya fada yana maida hankalin sa kan wayarsa har husna ta zubo tea ta fara mika masa karba yayi ya aje gefen ta sannan ya karbi plate din ya ajje, cup din tea ya dauko tea ya debo a spoon Yana firfitawa da bakinsa sannan ya mika mata kauda Kai tayi mahreen yakira sunan ta ahankali juyowa tayi cikin shagwabar da bata san tayi ba , " karbi nace ,ba musu ta bude bakin ya bata cikin wani irin tukuki daya tsayawa Imran a wuya ya tashi yayi waje binsa sukayi da Ido banda Maher da kawai feeding din mahreen yake kamar wata yarinyar goye har saida tace masa ya isa sannan ya mikawa husna cup da plate din ya Mika mata tissue.
Masu share share ne suka shigo hakan yasa su aunty ummi fita dakin ya rage daga mahreen sai Maher magani ya fiddo a aljihun sa ya balla ya mika Mata tare da dauko mata robar ruwa ya mutsa fuska tayi ni bana sha ohk do u prefer an injection shuru tayi tare da kurawa maganin Ido dauka yayi da hannun sa open your mouth kamar zatayi kuka tayi yadda yace a tsakiyar tongue dinta ya dora mata magani sannan ya dora mata ruwa a bakinta da sauri ta fara shan ruwan har tana kwarewa bubbuga bayanta yake a hankali harta yi shuru , "da akwai securities awaje saboda dole zasu bibiyeku keda husna, okay tace ,do u need something ? husna need clothes to change ohk ya fada sannan ya fice ita kuma ta kwanta , husna da aunty ummi kawai ya samu a waje dan Imran da nawal sun wuce , aunty ummi yai ma sallama da cewa zaije wani waje ya dawo sannan yace husna ta biyoshi , wasu yaran sa da yakira su biyu domin su canji wanda suka kwana yayiwa magana sannan yacewa husna kibisu zasu kaiki ki siyo duk abinda kike bukata to tace sannan ta bisu shi kuma ya shiga motarsa ya wuce.
YOUNG WRITER
MAHREEN