MAHREEN

PAGE 61----70

by @swrites22

Yana shiga headquartern su da miss rabi ah ya fara cin Karo bayan ta gaishe shi kuma sai ta bishi office , saida suka zauna yace ya akayi ne? umm sir dama mahreen fa bata shigowa aiki Kan lokaci kuma kuma tafiya take kafin a tashi , " waya fada maki ? umm dama dama katseta yayi da tayi report ai karki damu idan kina da wata magana ki fadi ? a a babu sir dama na dauka baka sani ba ne sai da ya dan dakata ya dube ta kasa tayi da kanta girgiza Kai yayi kawai ya hado wasu takardu ya miqa Mata da fadin kije ki karasa wanna aikin , ohk tace tana karba ta fita .

Kogin tunanin mahreen ya fada sosai yake jinta a zuciyarsa na farko tausayinta yake ji na biyu kuma ta sadaukar da ranta saboda shi da badan ita ba da yanzu shine a gadon asibiti Ko kuma ma ba wanna zancen ake ba table dinta ya kalla yana tuna rigimar da suke kullum idan tazo murmushi yayi kawai sannan ya tashi ya fita dan zuwa ganin yaran da yasa aka dauko daga Aiden palace.

Sai rana Ayman yazo dubata (saboda Saida safe ya sani a lokacin daya kirata Kan maganar case din tsohon nan) nan yace anya kuwa gobe zaki iya shiga court din nan inaga kawai a nema masa wani sai a biyashi da ace bani da wani case din daidai time din dani zantsaya masa tun farko ma whl , "don't mind Ayman in sha allah zanje , "tho amma bakida lpy ai , karka damu zan iya.

Imran kuwa har dare bai sake zuwa dubata ba kuma tana ji shi yakawo nawal kuma shi yazo ya dauki aunty ummi da dare bayan tafiyarsu sana ta Kira sun dade suna waya sannan sukai sallama.

Sai 11 :46 pm Maher ya shigo a reception ya ga nawal tana waya karasawa dakin yayi husna ya samu Akan kujera tayi tagumi har bata san ya shigo ba idonsa yakai Kan mahreen da take ta danne danne awaya da hannun ta mai drip din karasawa yayi ya jawo kujera ya zauna sai a lokacin suka farga da shigowar sa husna ce tayi masa sannu da zuwa ya amsa Mata da kulawa, tashi tayi ta shige toilet juyowa yayi ga mahreen madam Mai ake tayi ne haka ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ajje wayar could you please discharge me , why ? "because I'm feeling alright, but you know they haven't removed the thread from ur hand right, " I know I will come back when they schedule the removal okay, but why do u insist ? cuz I have a case tomorrow in the higher court and I must attend . Then, how will we handle husna ? you know it's risky to let her return home , " I know she will stay with aunty ummi until we complete our investigation , alryt not bad, last night I listened to everything on the memory card, " then when will take them to court since we have all the necessary evidence , yea but I will visit them tomorrow night, I wanna go with you dan satar kallon ta yayi sai kuma yace okay , "what did you tell aunty ummi when she asked what happened to me ? I told them that there was a problem on the road you crossed and a bullet accidentally hit Ur hand when they fired their guns , " hmmmm alhamdulillah thank you so much , " why are you thanking me, "cuz she didn't know anything she doesn't know I'm working as a dss , "then why don't you tell her , she wouldn't agree .

Dakin ne ya dau shuru na wani lokaci can kuma tace are you a doctor , yes and you are working as DSS officer how is that possible , " like how you manage your both roles ya bata amsa daidai lokacin da husna ta fito idonta yayi ja da alama kuka tayi wayarta ta ciro a chargy ta koma kujera ta zauna nawal ce ta shigo itama sannu da zuwa tai masa sannan ta nemi guri kusa da husna ta zauna dakin ne ya sake daukan shuru har saida drip dinta ya Kare sannan ya tashi ya cire da fadin kwanta kiyi bacci dan hararar sa tayi sai kuma ta kwanta din, samun chargy ta fada tana Mika masa wayarta kamar bazai karba ba sai kuma ya karba ya makala sannan ya musu sallama ya fita.

Da safe da wuri ta shirya tayiwa husna bayanin komai Dan haka idan su aunty ummi sukazo tare zasu wuce ita kuma tayi da Ayman zaiso ya dauketa .

9am tana cika suna karasowa harda Imran bayan an gaggaisa bata bi takan cin maganin da Imran yake tayi ba tace aunty ummi tana son ganinta janta tayi suka fita daga dakin sannan tayi mata bayanin komai da kuma nasarar gano su datayi ta dalilin husna sannan ta dora da inaso ta buya agidanki har sai mun gama bincike, keda wa zakuyi binciken nan mahreen nifa ina tsoro, " ni da doctor Maher ne aunty ummi tunda shima abun ya shafesu ajiyar zuciya ta sauke bazan hanaki ba amma ki Kula da kanki sosai, " Insha Allah auntyna ta fada tana dan murmushi, tou yanzu da kika shirya ina zaki ? an sallame mu fa sannan ina da wani case ne a court kimin addu a aunty yaune zan fara shiga court , "Amma bakya ganin har yanzu baki warware ba kofa dinkin hannun ki baa cire ba, " karki damu aunty ummi bana son zaman asibitin daga baya na dawo acire inaso mu gama duk abinda zamuyi da sauri domin maka azzaluman nan a court , shikenan to muje kiyi breakfast ko.

Saida tayi breakfast sannan suka dan zauna ana hira suna hada kayan da suke a asibitin don tafiya Imran ne ya hau kusa da ita akan gadon ya zauna Lilly nifa inada magana dake , "karka damu bros bari in danyi less busy , " amma kinsan daganan gida zamuyi ko ? yea nasani amma yanzu kasan court zani ba gida ba, " wa zai kaiki kafin tayi magana Maher ya shigo kaman jiya haka suka gaisa ciki kuwa harda mahreen da tace masa morning hannun sa yasa a goshi alamar sara Mata ba tare da yayi magana ba dan kallo daya ya musu itada Imran din ya kauda Kai cike da jin haushin Imran din wanda yarasa dalilin hakan , wrist watch dinsa ya kalla ba tare daya kalleta ba yace tashi mutafi inkin gama, "ina jiran Ayman nefa shi yace zai kaini cikin jin haushin ta itama da kuma kokarin controlling kansa ganin ya hana bacin ransa bayyana yace idan yakaiki wa zai daukoki to shi ya wuce in zaki tafi to in kuma bazaki tafi ba ki zauna yana gama fadar haka yayi waje.

Imran ne ya juyo wajenta wai maisa yake maki magana ne sai kace wata yarsa ko kuma wadda yake da iko da ita kallonsa tayi taga kaman adan zafafe shima yake maganar, "to kai ma yanzu fadan zakamin ko Me? sauka tayi sannan tayi wa aunty ummi sallama tayi waje, number sa takira Yana dagawa tace Kana ina ? ki fito mana ya fada yana kashe wayar .

Shuru ne ya ratsa motar har suka kusa karasa wa tace kafadawa granny ina hospital ? nop na dai cemata kina gidan aunty ummi shuru suka sakeyi har suka karasa tana kokarin fita yace idan kin gama kifito ina jiranki okay tace sannan tayi ciki.

Cikin nasara suka samu alkali ya yanke hukunci saboda kwarara hujjojin data bayyana shari'ar kusan shekara hudu an kasa kawo karshenta sai yanzu, mutumin ne ya biyota Yana mata godia bakomai kawai tace. Kana kallon fuskarta kasan tana farin ciki dukda bata bayyana ba a Inda ya sauketa anan ta sameshi ya kwantar da kujerar baya shiga tayi ta zauna fuskarsa ta zubawa Ido ta daukama bacci yake , re u done ya tambaya kamar bayaso still idonsa a rufe kanta ta juya tana kallon waje tace eh gyarawa yayi ya kunna motar suka fara tafiya ahankali take bashi labarin yadda shari ar takasance murmushi yayi kinyi kokari sosai Allah yakara hazaka murmushin itama tayi sannan tace ameen har suka karasa gidan aunty ummi dukkansu wani yanayi sukeji na daban har basuso suka karaso ba , bude kofar tayi sannan ta jiyo thank you for the care I truly appreciate , get ready by 8pm , okay sir ta fada tare da rufe kofar ta fita .

Imran ta samu a parlour da alama zaman jiranta yake karasowa tayi ta zauna tana fadin oh allah na nagaji kallonta yayi dama I'm just waiting for you , I can see she ai then what's up ? fadamin gsky abinda ya faru har aka harbeki ? shin shi doctor Maher din zai ma karyane Hala ajiyar zuciya ya sauke yana kallon hanya sannan yace nayi tunanin ko garin aikine ? nop ! sai kuma tace do you know what labarin abinda husna ta fada Mata ta bashi ta Kara da cewa kuma in sha allah everything has come to an end number Abdul hameed ta binciko awayarta tun ranar da husna tasa mata bata Kara bi ta kanta ba sai yanzu wanna number inason kaje kasa abincikomin duk wani list na calls dinda ke shige da fice da text messages zan baka letter cewar daga headquarter dinmu ne Ka wakilceni saboda abubuwan dake gabana dayawa bazan samu time ba kaji ko jinjina Kai yayi kamar wani danta yace an gama madam sai kuma yace to alhamdulillah tunda gashi burinki ya kusa cika sai kuma me next ? babu komai tace tana maida hankali kan wayarta, sai ki ajje wanna aikin kiyi aure kallonsa tayi wani aikin Kenan daga ciki ? aikin zaryar nan mana , "zanyi aure Amma ba yanzu ba , "to maisa ba yanzu ba mai kike Jira you are going to be 23yrs fa haba , "nayi tsufa Kenan ? nop ni ba abinda nake nufi ba kenan ai idan ma ba fada kikayi ba ba wanda zaice kinkai 23ye din , " then what's ur problem imran ta fada tana maida wayarta jaka ta zuba masa eyes gyara zama yayi sannan yace mahreen kinsan tunda kuka dawo nan na daura Ido akanki naji na sami Mata nayi kokarin bayyana maki kuma wanna abun ya faru ganin kin shiga rudu yasa na jinkirta daga baya kuma kika tado da tafiyar nan dan haka yanzu lokaci yayi dazan bayyana maki domin Nima na gaji da boye boye ajjiyar zuciya ta sauke Imran ba irin namijin da zaaki bane kuma ya bata muhimmiyar gudun mawar da baza ta iya mantawa da ita ba amma batajin tana masa son aure dan haka tace karka damu Imran zanyi tunani akai kaman zaiyi kuka yace wani tunani kuma murmushi ta masa gaggawa daga shaidan ne jinkiri kuma alheri ne Imran tunda nace kaban time kadan Kara hakuri mana tana fada ta mike ta wuce daki.

8pm daidai ta gama shirin ta yau atampa tasa dinkin skirt da riga Wanda yayi mutukar shiga da surarta bata daura dankwali ba sai mayafi data yafa kawai tadau jakarta ta fito a parlour ta samu Imran da daddynsa suna kallo wayarta ce tayi Kara tana dauka yace ina waje fa dakin aunty ummi taje tai Mata sallama sannan ta dawo parlourn tace wa daddyn zataje masaurauta amma ba Kwana zatayi ba adawo lpy yai Mata Imran ne yace Lilly dare baiyi ba kuwa ? don't mind Maher na waje Maher ya maimaita da mamaki ganin ta canja shigarta kuma tace tare da Maher zasu fita shin masarautar zasuje ko kuma wani wajen shima cewa daddyn sa yayi Yana zuwa sanna ya dauki dan makulli ya bi bayanta.

Tunda ta fito ya zuba Mata Ido wani kyau yaga tayi masa kodan ta canja shiga ne yau data san yadda kayan Hausa suke karbarta data ajje wanna shigar tata ta yahudu da nasara tana karasawa ya bude mata kofa ta shiga idonsa akan Imran daya ke tsaye kofar parlourn jan motar yayi suka fice ba wanda yace da dan uwansa komai a maimakon taga yayi hanyar masarauta sai taga yayi wata hanyar daban batayi magana ba sai tsintar muryarsa tayi Yana cewa waye shi ,wa kenan Wanda nake ganinku a asibiti tare ya fada kamar bayaso, oh wai Imran kake nufi shine babban Dan aunty ummi he's so kind ba shida problem dan kallota yayi sannan ya maida kansa titi meysa yake bibiyar ki to , bibiyata kuma like how ? kalli mirrorn gefanki cikin mamaki take kallon motar tabbas motar Imran ce kallosa tayi ya akayi kasan shine kallonta yayi ya dauke Kai ba tare da yace komai ba daidai nan wani security ya bude gate din wani gida shiga yayi da motar yayi parking , inane nan ? in mun shiga kya gani ya fada Yana ficewa itama fita tayi ba tare da tsoro ba tabi bayansa wasu thug boys ta gani a parlourn da alama abige suke suna ganin su suka fara boye kayan shaye shayen su suna Kiran sai oga Allah yakara lpy bai wani kulasu ba ya Mika masu hannu alamar subashi wani abu key dayan su ya Mika masa sannan yayi gaba itama binsa tayi suna zuwa ya bude dakin wani dan dattijon mutum ne ya bayyana duk an masa jina jina tana ganin sa ta gane shine na hoton data gani tare da su aunty amarya kofar ya rufe bayan ta shiga sannan ya karasa gabansa kujera ya janyo da kafarsa sannan ya nuna Mata da hannu alamar ta zauna karasawa yayi gaban chiroma daya girgiza da ganinsa kaganeni ya tambaya Muhammad ma-maher maika keyi anan murmushin gefen baki yayi na zo ne kafadamin yadda akayi kasawa abbana poison a abinci cikin firgici yace a a whl bani bane bansan da zancen nan ba ohk baka daku ba Kenan barin kirasu a a dan Allah tsaya zan fada whl zan fada ma gsky juyawa yayi wajen mahreen da hannu yamata sign data danna recording sannan ya fara tambayar sa meysa kasawa abbana poison a abinci whl bani bane Muhammad nima sani akayi waye ya saka? alhaji Abdul hameed ne da matarsa ina zaman zamana sukazo suka cusa min raayin daba nawa ba kuma ya bani kudade masu tsoka da cewa idan na aikata zai bani fiye dasu shi yabani poison da cewa na kaiwa jakadiya ta zuba a abincin alhaji Khaled tareda bata kudi Mai yawa a furar dayakesha duk dare wadda takasance ita take damawa anan tasa masa saidai kash a daren bai wani sha sosai ba saisa bata kasheshi ba saidai illar datayi masa wanda har yanzu Bai dawo hayyacinsa ba sunso mutuwa yayi Amma jin babbar illar data masa yasa sukace ya Zama minor bazai yi wani tasiri ba kuma whl nayi nadama ya fada yana rushewa da kuka, hotonsu shida Abdul hameed da aunty amarya ya bude awayarsa ya nuna masa sannan yace kasan dai wanna hoton bana da bane meya Kara hadaku kuma duk kuka tsallake ko ina kuka shige har dakinsa cikin rudewa yace a a -a a whl kamar daga sama yaji tsawar Maher zaka fadamin ne ko yaya ? dan Allah Kayi hakuri ohk baza kafada ba Kenan zan fada zan fada karkayi gigin yimin karya domin haka na barazana ga rayuwarka ya fada Yana daga masa rigarsa Inda ya hango bindiga soke jikinsa ne ya dau rawa, kirana sukayi akan sunaso akawar da maimartaba Inda sukeso na jawo waziri cikinsu saboda waziri shine na kusa da maimartaba tunda aka nadashi tare suke shi yake bashi shawara anan nake chemusu waziri baze bada hadin kaiba saidai su nemi wata hanyar shine sukace idan har banbi umarninsu ba na kawo masu cikas to sai sun tona min asiri awajen waziri , wani asiri Kenan ? cikin kuka yace wata tsohuwar alaqata ce da amaryar waziri , Kenan da Kai akaje aka kashe uncle da iyalansa ? whl Allah kaji na rantse ma Muhammad bansan komai akan hakan ba sai daga baya da nake tuntubarsa da zance shine yake cemin shine kuma idan nayi gigin fadawa wani abakacin raina, shiwa Kenan Ka tuntuba? alhaji abdul hameed juyawa yayi wajen mahreen data dora kafa daya Kan daya ta zuba masu Ido da hannu ya nuna masa tayi saving record din, hakan tayi sannan ta mike ganin shima yayi hanyar waje , tare suka fita karbar duk wani Abu da aka kamo chiroma dashi yayi sannan sukayi waje suka shiga mota suka wuce masarauta still Imran na biye dasu Inda ita kuma ta kule da hakan karfa yaga dan yace Yana sonta yayi amfani da haka yaga kamar har tazama matar sa ne da zai dinga wani binta duk Inda zataje dole ma ta shata masa layi.

A kofar part din aunty amarya sukayi parking sannan suka shiga ita dashi kawai suka samu a parlourn da alama wata magana suke Mai mahimmanci karasawa sukayi suka zauna cikin fara'a suka tarbesu wanda har hakan yabasu mamaki suka kalli juna mahreen ce tace ina husna aunty amarya ce ta cafe da cewa husna tayi tafiya taje zamfara wajen yayata bari akawo maku abinci ta fada tana tashi tayi ciki , Maher yajikin mahaifin naka ? yaji sauki gobe ma zasu dawo saisa nazo na fada ma ko zakuje taryoshi , adan rikice yace wai wadin kagane wani mahaifin naka nake magana kuwa ? yes nagane ba abban Muhammad Maher da Ayman da manira ba gobe zai dawo ai gumi ne ya fara tsatsafo masa tako ina sai ya Mike sai ya zauna Maher ne ya dora da cewa ya dai lapiya murmushin karfin Hali yayi Kai Amma naji dadi Allah yakawosu ashe har yasamu sauki bamu sani ba saidai kawai ace mana zai dawo ko awajen su waziri banjiba , "ai ba lalle kaji ba suprise muka muku , e..eh eh hakane ya fada still har yanzu baya nutsuwarsa kallon mahreen yayi alamar jinjinawa tai masa tana murmushi daidai karasowar aunty amarya da hadimai data dorawa abinci iri iri a tray tare dasu fruits da jugs aka ajje akan centre table sannan suka wuce ita kuma ta zauna tana murmushi bismillah ga abinci kuci mahreen ce ta Mike ta karasa gaban table din Apple guda daya ta dauka tana jujjuyawa a hannun ta sannan ta taka gaban gujerar Abdul hameed ta Mika masa apple din , gashi baba bismillah da sauri aunty amarya tace ha a Mene haka kuma mahreen wanna ai na kune ba nasa ba maisa zaici abincinku a a baza ayi haka ba murmushi tayi sannan tace saboda kinsa guba a ciki ko ? haba mahreen wanna wace irin magana ce takawa ta sake gaban table din sannan ta dauki cup ta tsiyayo juice takarasa wajen ta karbi kisha , ni ai bana shan irin wanna lemon mahreen, ummm wato muma ta uncle Khaled kikeso ki mana Kenan , wa wani Khaled din kuma mai muka masa dan girgiza Kai tayi sannan tayi baya ta ajje cup din a table ta juyo wajen Maher da gira tai masa alamar suje sannan ta dauki jakarta, mikewa shima yayi sannan ya kalle su an riga da an bari dan Kada ya girma wutsiyar rakumi kuma ta riga tayi nesa da kasa bar ganin allura kankanuwa ce karfe ce aduk lokacin da Mage ke waje bera baya Wasa yana da Kyau a rika Sara ana duban baki gatari qotar zata iya gocewa tasamu Mai saran kuma abinda dama ta jure hagun baza ta jure ba abinda ya Baka dariya yau gobe shi zai saka ka kuka yana gama fada haka yayi waje mahreen ta Mara masa Baya , cikin shock suke kallon kallo da matsala fa alhaji wai maike faruwa ne tabbas asirin mu na dab da tonuwa fiddausi dama na gaya Miki ai, ni nasan ba Wanda zai je famu wanna matsalar in ba husna ba ace Ka haifi da acikinka sannan yafi karfinka to wai tana ina ne ? an cemin suna tare da wanna mahreen din, amma fa kinaji yanzu take tambaya ina husna, to abin ya daure min Kai gashi layinta a kashe amma ni inada tabbacin duk yadda akayi dasa hannunta to yanzu miye mafita gashi ance gobe Khaled zai dawo wai ya warke , wani Khaled din tafada tana mikewa Khaled dai dakika sani dan maimartaba safa da marwa ta fara dan neman mafita.

YOUNG WRITER

MAHREEN