MAHREEN

PAGE 81---90

by @swrites22

PALACE

Bayan sun shiga sun mika gaisuwa Ayman yace wa waziri suna da magana da maimartaba , sallamar mutanan fadar akayi sannan yace dasu sarki na sauraren Ku bayani suka fara masa tare da kunna masu duk wasu audio. Sarki mai adalci da tawakali ya girgiza da jin abinda kaninsa ya aikata masa uwa daya uba daya akan Mulki ya nakasta masa ya ya da duk duniya bashi da wa anda yake kalla yaji dadi saisu cike da bakin ciki yace wa Maher Allah yakaisu ranar zaman kotun.

Duk wasu evidence daya kamata Ayman da mahreen su tanada sun hada domin so suke ranar da aka hau kotu a yanke hukunci kawai duk wasu maganganun sirrin da Abdul hameed yayi a waya mahreen ta tantancesu, sun bawa Abdul hameed damar daukan lauya haka kuwa akayi yayi wa lauyansa magana tare da masa bayani cewa karya ne shi bai aikata duk abinda suka ceba, ko da mahaifiyar Maher taji labari ta girgiza dama ta dade tana zargin furar da jakadiya ta dama ranar amma kasancewar batada hujja yasa tayi shuru kuma jin halin da ake ciki akan hargitsin da Abdul hameed ya kawo a masarauta yasa bata gayawa su Maher improvement dinda aka samu akan rashin lafiyar mahaifinsu ba , dan likitoci sunyi aiki sun qone ragowar gubar dake jikinsa sannan suka bada tabbacin zai kai one zuwa two weeks kafin ya farka amma suna da hope idan ya farka zai tashi lafiya.

Abangaren Imran kuwa daddysa da aunty ummi ya samu kan cewa sun daidaita da mahreen akan zasuyi aure shine yazo ya sanar masu ganin yadda suke sai basu bukaci jin ta bakin ta ba Inda daddynsa yace abari idan aka gama case din nan sai suje har wajen maimartaba suyi magana cikin farin ciki ya tashi ya tafi da fadin Allah yakaimu.

COURT

Cike take makil tako ina ka juya mutane ne waziri shiya wakilci Mai martaba can cikin lauyoyi na hango Ayman da mahreen suna ta hada takaddu rigistra ne ya Mike ya Kira shari ar su mahreen sannan yamikawa judges din su uku dake high table file din , judge din na tsakiya shi yace ina lauyan masu Kara Ayman da mahreen ne suka Mike sannan akace ina lauyan mai kare wanda ake Kara lauyan Abdul hameed ne ya Mike daidai lokacin da aka shigo dasu Abdul hameed da aunty amarya da chiroma da jakadiya Maher ne da yaransa guda biyu abayansu waje ya nema ya zauna , nan aka fara karanto laifin da ake zargin Abdul hameed dashi karyata wa yayi da cewa sharri ake masa shi bazai yi haka ba judge ne yace to ku kunji ya musa shin kuna da hujja mahreen ce ta Mike ina da ita hujja ya me girma me shari'a takawa tayi gaban Abdul hameed audion sa ta bude masa saida ya gama ji sannan ta karasa ta mikawa registra shi kuma ya kunnawa judges din duk suka saurara tukun aka kunna masu hotonsa tare da su chiroma da matarsa kuka ya fashe dashi da cewa na amince na aikata whl amma sharrin shaidan ne kuma da sharrin Matata ya fada Yana pointing aunty amarya ita ta jefani a bala'i , alhaji sharri zaka mun ni fa bansan komai ba muhawara ce ta barke a tsakaninsu har saida kotu ta tsawatar masu, kansu chiroma da jakadiya aka koma ba musu suka amsa yaran da suka tura ranar domin kashe su husna tare da yaran da suke tare da Abdul hameed a ranar daya kashe iyayen mahreen tambayoyi aka masu suka amsa lauyan Wanda ake kara ko kanada ja akan hujjojin da kuma bayanan da lauyoyin masu Kara suka bayyana cike da sanyi jiki yace bani da ya Mai girma mai shari a.

kotun ce tayi shuru na wasu dakika sannan Mai shari'a yace according to Section 319 of the Nigerian Criminal Code . Subject to the provisions of this section of this Code, any person who commits the offence of murder shall be sentenced to death dan haka kotu ta yankewa Abdul hameed Umar Jamil hukunci kisa ta hanyar harbi da bindiga sakamakon rashin wahalar da shari a da baiyi ba kotu ce tayi tsit sannan judge yaci gaba da magana kotu kuma ta yankewa fiddausi auwal magaji hukuncin zaman gidan Kaso na tsawon shekara goma tare da horo Mai tsanani sannan kotu ta yankewa jakadiya daurin rai da rai sakamakon yunkurin kisan Kai datayi ta hanyar saka wa uban gidanta guba a abinsha sannan an yankewa chiroma shekaru bakwai gidan yari tareda Tarar 500,000 nan kotu ta dau hayaniya ,asaurara masu shari'a suka fada sannan aka koma Kan yaran nasu shekaru bibbiyu aka yanke masu tare da Tarar dubu dari dari sannan masu shari ah suka buga guduma duk mikewa akayi har saida suka fita sannan mutane aka fara maida zance mahreen ce takarasa wajen husna dake kuka ta dago ta rungume itama hawayen taji suna neman zubo Mata saboda tuno da mahaifanta da tayi aunty ummi ce ta karaso ta hada su duka ta rungume hakika husna kinyi sadaukarwa Kuma ubangiji shi zai maki sakayya da mafificin alheri hakika zan rikeki kamar yadda zan rike nawal kinji ahaka duk suka firfita waje .

fitowa akayi zaa tafi dasu Abdul hameed husna ta karasa wajensu "Baba kayafe min hakika banyi hakan dan na tsane ku bane idon Abdul hameed cike da hawaye yace baki min komai ba husna kuma na yafe maki domin taimako na kikayi dan nasan idan naje lahira azabar sai tafi haka gwanda amin anan duniya kuma nayi nadama ina fatan Allah ya karbi tuba na Allah yamiki Albarka yabaki miji nagarih wanda zai Kula dake inaso ki rokarmin yaya gafara ya yafemin kinji yana gama fadi aka tasa keyarsa mama tace tana riko kafadun aunty amarya juyowa tayi mama kiyafemin murmushi tayi ba komai husna Allah ya yafe mana mama fishi kike dani Dan Allah mama kiyi hakuri kiyafemin kema, ko daya ba fishi nake ba dama ko ba yanzu ba asirin mu sai ya to nu domin rana dubu ta barawo rana daya tak ta mai Kaya dan haka Allah ya miki Albarka ki Kula da kanki kirike sauran yayunki da hannu bibbiyu sannan ki dauki matar babanki lamya kamar ita ta haifeki kinji nasan bata da matsala zata Kula dake itama wucewa akayi da ita aunty ummi ce ta jata sannan suka shishiga mota direct masarauta suka wuce , ranar cikin jimami aka yita sai dare suka komo gida.

TWO WEEKS LATER

Imran ne ya matsawa mahreen cewa taje ta ajje aikinta na DSS tunda burinta ya cika kuma ga magana har taje gaban mai martaba gashi ba a wani ja auran ba aka saka wata uku masu zuwa , "bazan ce zan ajje aikin nan yanzu ba gsky Imran, "to sai yaushe ne dear inaga dama iya waadin dakika dauka daga burin nan naki ya cika zaki ajje mesa yanzu kike son canjawa murmushi tayi karka damu Imran nama alqawari kafin auren zan ajje aikin, " ni fa dear ya kamata a canja min sunan nan , " ummm karka damu akwai lokaci ta fada can kasan zuciyar ta kuwa batajin wani son Imran kawai dai tasan ya Mata halacci kuma bashi da wani aibu amma ita tarasa me sa batajin sa a zuciyarta ta , kanta ta daga sama tana kallon yadda iskar hadarin farkon damina ke kadawa karar text ne ya shigo wayarta dubawa tayi Maher ne yace kina ina ne sunshine sunan ta sake maimaitawa sunshine reply ta masa da gida , inaso inzo in ganki a fakaice ta kalli Imran dayake danna waya shima tuna abinda ya faru tayi rannan hakan yasa ta tura masa Kai Kana ina ? love garden, ohk wait for me there, hopefully there's no problem, yea kawai ya tura Mata kallon Imran tayi sannan tace inaso naje naga granny na dan kwana biyu ban leqa ba kamar zaice suje ya kaita sai kuma dai yace adawo lpy take care , okay tace sannan ta koma ciki after dress ta dora sannan ta fito, da map tayi amfani dan zuwa Inda ya fada matan. tana fita ta kirashi kwatanta mata Inda yake yayi tana karasowa ta zauna , murmushi ya mata ai na dauka baza kizo ba gira daya ta daga maisa tho zanqi zuwa, " umm to nagode ya jikin abba ta tambaya da sauki alhamdulillah shuru sukayi na dan wani lokaci sannan yace mahreen naam tace tana bashi full attention dinta saida ya nisa sannan yace mahreen kina so na , shuru tayi kamar me tunani kafin tace kaman ya bangane ba, I mean kina so na zaki aureni , "whl har yanzu ban bangane Inda Ka dosa ba Maher wace irin magana kake ne , wani zazzafan numfashi ya fezar mahreen ina sonki kuma ina so in aureki mu rayu cikin aminci , "ni kuma bana sanka Maher ban taba ma kallon irin san da kake magana akai ba ina sonka a matsayinka na cousin dina kuma jini na , karya kike mahreen kina so na ya fada Yana Mikewa, itama mikewa tayi nace ma bana san ka Imran nake so kuma Shi zan aur.... Bata karasa ba ya bige mata baki karya kike mahreen kalli cikin idona kice min bakya so na baza ki aureni ba sannan me sa kika taremin bullet ranar nan in har da gaske bakya son nawa meysa baki bari bullet ya sameni ba kinga mahreen karki cuci wanna zuciyar data cika da begenki ki nutsu muyi magana ta fahimta ki bar wani zancen imran karkice ko dan kina zaune gidan su baza ki iya cewa bakya sansa ba , "wai Kam ko Ka kurman ce ne Maher nace ma Imran nake so kuma Shi zan aura nan da three months kasan dai bakyau nema cikin nema ko kuma kasan magana har taje gaban manya ya kakeso Ka hargitsa min tunani ne, "ko daya mahreen kin kasa banbance SO DA KAUNA kinason Imran amma ni zuciyar ki take kauna ga hakan a idonki me sa zaki karyata me sa zaki hana zuciyar ki abinda take kauna haba mahreen ki bar wanna wasan dan baki san yadda nake ji bane da baki fada min wanna maganar ba dan Allah in wasa kike ki bari zuciyata zata iya bugawa hañnun ta yakamo ya dora daidai saitin zuciyar sa mahreen please kitaimaki wanna zuciyar hannun ta ta kwace ta rufe bakinta dashi duka hawaye suka fara ambaliya a fuskar ta da sauri ta juya gudu gudu sauri sauri ta hada ta fice ko ganin gabanta sosai batayi haka ta karasa mota ta fige ta a guje sai gida bata shiga ciki ba saita zagaya baya saida taci kukan data rasa na miye sannan ta wanke fuskarta a tap ta shiga gida lokacin an fara Kiraye Kirayen sallar magrip.

TWO DAYS LATER

zuciyoyin nan biyu sun shiga wani hali especially Maher daya tabbatar mahreen na neman yi masa nisa tunda gashi ya tabbatar nan da wata ukun ne aurenta duk ya rame ya fita hayyacinsa , sai kuma ya samu Kira daga Ammi cewa su zo tana nemansu da gaggawa cikin tashi hankali yake tambayar ta ko wani abune ya faru ba komai ku de kuzo kawai cikin wani tararrabin ya sake fadawa ba bata lokaci ya sanar da Ayman suka shirya tafiya tare da sanarwa grandparents nasu zasuje duba mahaifinsu ne .

Suna zaune bayan an gama masu screening ya dauko wayarsa yana so ya kirata kuma me ma zaice mata da haka dai ya yanke shawarar kiranta har sau biyu bata dagaba sai ana ukun ne ta daga hello!, inaji tace, cikin dacin rai da kuma dacin maganar da zai fada ya lumshe idon sa dama na bugo ne na tayaki murna Allah ya sanya alheri zanyi tafiya watakil kuma kafin na dawo kinyi aure Allah ya baku zaman lpy yana gama fada ya katse wayar yana dafe kirjin sa da yakeji kamar zuciyar sa zata fito, abangaren mahreen ma hakan ce ta kasance wani Abu taji ya tokare Mata makoshi so take tayi kuka ta kasa pillow ta kankame tana runtse Ido tare da sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya.

Abun da suka Tarar a Egypt shiya kusan shafe rabin bakin cikin da Maher ya taho dashi abbansu suka samu zaune manira na gefensa tana basa labari Ammi kuma tana hada masa shayi sunyi farin ciki sosai ganin abbansu ya tashi daga paralysis kuma yana magana saidai takawar ne har yanzu batayi karfi ba sati biyu da zuwansu aka sallame su daga asibitin gidansu dake nan Egypt suka koma .

yanzu ma zaune yake shi da abbansa yana matsa masa kafafunsa manira da Ammi kuma suna kitchen Ayman kuma ya fita , abba ne ya dafa kansa son miye matsalar murmushin karfin hali yayi ba komai abba mai ka gani ? Maher karka boyemin damuwarka ko da banida lpy ina gadon asibiti mun saba sharing komai tare dukda baka fadamin marar dadi amma komai zakayi ko kayi saika labarta min dan haka kafadamin abinda yake damunka nisawa yayi sannan yace abba Dama....... Zayyane masa komai yayi dan jim abban yayi sannan yace karka damu Maher idan mahreen matar kace bata da miji sai Kai idan kuma ba matar Ka bace to Ka qaddara dama haka Allah ya tsara girgiza masa Kai kawai yayi ba tare daya sake cewa komai ba.

wata biyu sukayi sannan suka shirya dira Nigeria domin yiwa mutane bazata dan dama basu fadawa kowa tashin abban ba ,kwana kwana Maher ya fara dan baya son dawowa Nigeria yanzu amma abbansa ya kasa ya tsare tare zasu dawo hakan Kuwa akayi abba ya tuso keyarsu suka dawo manira cike da farin ciki take dan ita batasan Nigeria ba tun tana 1 year aka tafi da ita Egypt.

Mahreen mahreen kina ina mahreen ce tafito daga daki har wani yar rama tayi naam aunty ummi, kije kicewa su husna su shirya anjima zamuje sannu da zuwan kanin mahaifinki , sun dawo ne ? eh kuma ance ya warke ma, Allah ya Kara lpy tace tana komawa ciki jiki a sanyaye duk ta zama wata iri .

Bayan magrip suka shirya nawal ce ta kalli mahreen tab yau dai inajin zaai ruwa da kankara yau kece zaki fita da hijabi mahreen bata kulata ba tayi waje, a parlourn grandmother dinsu duk suka samesu har Mai martaba mahreen da Imran sune abaya tunda suka shigo idonsa na kansu Amma sai yayi kamar wayarsa yake dannawa gaishe gaishe aka fara abban su Maher ne yace zo nan daughter zo ki zauna nan kusa dani Kan mahreen akasa ta karasa ta zauna satar kallon Maher tayi taga ya kauda Kai can kuma ya mike ya fice a zuwan zai amsa waya Mai martaba ne ya bukaci abar mahreen anan ta kwana Imran kamar ya hadiyi zuciya saboda shi ganinsa dan ta hadu da Maher ne Amma ba yadda zaiyi dole haka ya dauki aunty ummi suka tafi domin husna ma cewa tayi zata zauna itama nawal tace za akawosu gobe tare aikuwa raba dare sukayi suna hira da manira dan ma ita mahreen din tana da damuwa saisa duk a takure take .

Washe gari tana tashi ta duba time 5:09pm ta gani ganin dakin bakowa yasa ta mike dama tana fashin sallah wanka ta shiga ta fito ta shirya sannan ta fita parlour shima shuru sai hadimai ne daketa hidima suna ganinta suka zube suna kwasar gaisuwa hannu kawai ta daga masu ta shiga kitchen ta zuba juice a cup sannan tafita garden ta kofar baya Maher ta gani zaune ya zubawa waje daya Ido duk yayi rama jikin ta ne ya karayin sanyi harta karasa taja kujera ta zauna tare da cewa good evening sau daya ya kalleta ya dauke Kai Yana kokarin tashi Maher ta Kira sunansa slowly tsayawa yayi shi bai tafi ba shi bai juyo ba sai kuma tarasa mai zatace tafiya ya fara har ya fice daga wajen cup din juice din ta daga ta buga da bango zuciyar na wani irin zafi wayarta ce tayi Kara ko dubawa batayi ba ganin an ki de na Kiran yasa ta daga ba tare data duba sunan ba cikin masifa tace wai waye ne yake damuna Imran kuwa a zuciyarsa cewa yayi nasan zaa ri na ba tana tare da wanna yaron ba watakil ma ya hure Mata kunne ina waje ku fito kawai ya fada kashe wayar tayi ba tare data amsa ba ta tashi ta koma ciki. a dakin ta samesu sun dawo nawal ce tace mahreen ya Imran yazo yana waje yana jiranmu bata tanka mataba ta dauki hijab ta makala sannan tayi waje what's wrong with her manira ta tambayi nawal I don't know too ta fada da mamaki meya bata mata rai haka kuma daga ina take da wanna tunanin suka fito granny da fitowarta parlour Kenan suka Mata sallama nawal maiya samu yar uwar taku naga ta fito kamar zata tashi sama , whl mu ma haka ta shigo mana mun barta tana bacci mukaje part din Ammi shine dawowar mu muka Tarar bata nan sai kuma gashi nan ta shigo ranta abace , Allah ya kyauta Ku gaida mamanta ku ita kuma wanna ina zata ta tambaya tana nuna manira husna ce tace wai part din Ammi zata koma tunda mu tafiya zamuyi , au kaura zaku mun duka Kenan to ai ni duk Wanda yaci tuwo dani miya ya sha zaa zo a sameni ne duk dariya sukayi har manira da bata san Mai grannyn ta fada ba sannan suka fice a mota suka samesu sallama suka yiwa manira ta wuce part dinsu su kuma suka shiga mota.

Fitowa tayi cikin Shirin fita yace ina zaki ne love ? zanje na aje aikin ne kamar yanda na ma alqawari murmushi yayi cikin jin dadi to ko kefa my love adawo lpy take care of yourself for me wucewa tayi ba tare data sake magana ba.

tunda ta shiga office din ta hangoshi shida miss rabi ah suna magana ganin shigowarta yasa ya canja hirar daga ta aiki zuwa wata hirar daban itama miss rabi ah wanna damar tayi amfani da ita ta fara zuba masa labari murmushi kawai yake dukda bai Kai zuci ba, sosai taji zafin ganinsu a haka wanda har hakan ya kasa boyuwa a fuskarta karasawa tayi ba tare da tayi magana ba ta dora masa takardar akan table ta juya tsintar muryarsa tayi Yana fadin takardar miye ne wanna din? resignation letter ce , to ai bani keda alhakin karba ba sai kije wajen sir JB juyowa tayi cikin dacin rai ta warci takardar saida takusa bakin kofa yace wa miss rabi ah dear bita ki karbo takardar tashi tayi cikeda jin dadi ta bita dan karbo takardar a maimakon ta bata takardar saita hada harda IV bikin su tace gashi kya hada masa dashi sannan tabar wajen cikin sauri ta karasa ta shiga mota kifa kanta tayi akan steering tayi shuru ta rasa Mai yake Mata dadi saida tayi kusan five minutes tukun tasamu ta tada motar ta fita a harabar wajen.

Miss rabi ah tana komawa tace gashi wanna kuma tace abaka ta bashi IV din, file din dayake Mata magana akai dazu ya mika Mata zaki iya tafiya cike da farin ciki ta wuce dan yau ta samu fuska wajen Maher , IVn ya dauka Yana kallo yayyaga wa yayi sannan ya mike ya zuba a dustbin safa da marwa ya fara Idonsa cike da hawaye zuciyarsa tafara masa nauyi abubuwansa ya dauka ya bar office din.

YOUNG WRITER

MAHREEN

END 91-----100

Shirye shiryen biki ya kankama Inda ya rage saura kwana uku a daura aure da yake sai an fara daura aure tukun na ayi sauran event din yayin da amarya take kwance ba lafiya ko abincin kirki taki ci anyi anyi aje asibiti taki dole haka suka hakura suka zuba Mata Ido, Ammi taso ta dawo wajen ta har a gama bikin amma aunty ummi ta hana acewarta ai itama yartace ba sirika ba ganin maimartaba yasa baki yasa aunty ummi hakura da in an daura aure zata koma fada har sai an gama events din saita tare a gidanta.

A bangaren Maher kuwa tunda yaga shirye shiryen da ake a masarauta na bikin mahreen ya shiga daki ya kulle kansa ya kashe wayoyinsa anyi neman duniya an rasa shi sosai iyayensa suka shiga tashin hankali especially abba wanda yasan kwanan zancen wasa wasa har ranar daurin aure ba Maher ba labarin sa , Ayman ne ya shigo part din dan daukan wani abu a dakin Maher zuwa yayi ya jijjiga kofar a kulle Allah yasa suna raba spare key daukowa yayi ya gwada cikin sa'a ya bude can ya hango Maher karshen gado Yana fidda numfashi da kyar da sauri ya karasa Yana masa magana ganin baa cikin hayyacinsa yake ba yasa ya fice da sauri fada ya nufa acan ya samu mahaifinsa janshi yayi gefe ya fada masa abinda ke faruwa komawa yayi shima sannan ya sanar da maimartaba shi kuma suka tafi shida Ayman domin kaishi asibiti.

Abangaren mahreen tunda ta tashi yau da ciwon Kai da zazzabi mai zafi har suma take nawal ce tafita da gudu ta sanar da aunty ummi halin da ake ciki driver tasa nawal din takirata Mata don Kai mahreen asibiti sannan tabukaci sana da nawal din su tsaya da baki ita da husna kuma su kaita asibitin , ahanya take Kiran Imran take shaida masa shima cikin tashin hankali yace zai same su acan.

MASALLACIN FADA

2:00pm daidai bayan an idar da sallar jumma a aka fara sanar da an daura auren MAHER KHALED ABDALLAH da amaryarsa MAHREEN ISHAQ ABDALLAH Akan sadaki dubu Dari biyar sannan aka sanar da daurin auren IMRAN MUKTAR AYUB da amaryarsa MANIRA KHALED ABDALLAH Akan sadaki dubu dari biyu , duba na kai wajen Imran kwallar data tarun masa a Ido ya dauke Yana amsar gaisuwar mutanen da suke masa murna.

Abangaren majinyata kuwa da suke hospital Ayman ne ya shiga dakin da aka kwantar da Maher idon sa biyu amma idanunsa a rufe karasawa Ayman yayi Yana dariya angon mahreen sai a tashi cuta ta kau bude Ido yayi akan ayman dan neman Karin bayani ,videon ya masa playing awayarsa daidai lokacin da ake am batar an daura auren MAHER da MAHREEN ,Mai hakan yake nufi Ayman taya hakan ta faru murmushi yayi za kaji komai abakin Mai martaba Amma ba yanzu ba , "Ayman maisa zakuyiwa mahreen haka bani takeso ba Imran takeso ta fadamin da bakin ta shin wani irin kallo kukeso ta min mai son kansa ? dariya ayman ya saki da fadin ai duk jirgi daya ne ya kwasoku domin ita mahreen din ma yanzu haka tana cikin asibitin nan an kawoka da kadan itama aka kawota kuma I'm sure itama dalilin dayasa aka kawoka shi yasa aka kawota , " Ayman Kana nufin mahreen ma tana cikin irin halin danake ciki kwarai kuwa Maher ai..... Maganar sace ta tsaya ganin husna ta shigo da gudu tana kuka tana nuna masu hanyar waje menene Ayman ya tambaya mahreen ta bashi amsa ai kafin ta karasa bayanin Maher ya fisge Karin ruwan da ake masa sai ganinsa sukai abakin kofar da sauri husna takarasa fita ta nufi room dake opposite da nasu suka rufa Mata baya abinda ya faru kuwa shine farkawar ta Kenan husna tafara tsokanarta da an daura an daura ta Zama matar ... .bata Karasa ba numfashin mahreen yafara sama da kasa shine dalilin dayasa ta rikice ta fada dakin Maher .

Ko da suka shiga ta sake suma Ayman ne yafita da sauri Dan Kiran doctor, doctors biyu ne suka shigo cewa sukayi su fita Maher ne yace shi ba zai fita ba dakyar doctor rukayya ta samu ya fita Amma a kofar dakin ya tsaya .

Kusan 40 minutes suka fito dashi suka fara cin Karo doctor rukayya ce tace ta farka Amma munsa mata oxygen kafin numfashin nata ya daidaita yanketa yayi ya shige ciki gaban gadon ya karasa ya kamo hannun ta ya hada da nasa yace mahreen dagowa tayi ta zuba masa Ido kokarin cire oxygen din take ya riqe hannun rufe Ido tasakeyi hawaye na zuba ta gefen idonta mahreen open ur eyes and see me ni ne Maher dinki ur husband Ido tasake budewa sosai tana kallon sa yace yes I'm ur husband dani aka daura maki aure bada Imran ba su Ayman ne suka shigo shida husna ina wayarka Ayman Mika masa yayi ya bude videon sannan ya nuna mata sake lumshe idonta tayi Ayman ne yace husna taso kiga muyi waje .

Ganin numfashin ta ya fara daidaita yasa ya zare oxygen din sannan yatemaka Mata ta zauna sai a lokacin ya lura da yadda jini yake zuba ta wajen cannula dinda aka samasa cireta yayi gaba daya sannan ya karasa ya dauko tissue ya danne wajen karasawa yayi ya dale gadon da take zaune kanta ta dora Kan kafadar sa shi kuma Yana Mata magana a hankali shigowar su aunty ummi ,Ammii da abba yasa yai shuru kokarin raba jikinta da nashi take amma bai bada damar hakan ba murmushi irin nasu na manya abba yayi sannan ya dubi aunty ummi ai inajin kawai a sallamesu ko tunda naga sun samu sauki , "hakane barin ga doctor din.

Ana sallamarsu direct fada suka nufa Ko da suka koma Maher kafarsa kafar mahreen har saida Ammi ta korashi tukun ya fita , washe gari akayi sa lalle Sunday kuma aka shirya mother's eve Inda da antashi kuma angwaye zasu kwashi amaren su su tafi Maher a masaurauta zai fara zama kafin ya gyara gidansa.

Mai martaba ne ya aiko yana son ganin Maher da mahreen , Yana kokarin shiga dakin Ammi ta fito ina zuwa kuma tace dashi dan shafa kansa yayi Ammi dama Mai martaba ne yace yana son ganin mu kallonsa ta tsaya yi dan dariya yayi Ammi baki yarda dani bane Allah da gaske nake kuma ki kirashi kitambaya, naji to jeka, to Ammi ai tare yace muje , naji jeka zan turo ma ita juyawa yayi ya fita ita kuma ta koma dakin lace ta dauko Mata skirt da riga sai babban mayafi ki shirya yanzu mijinki Yana waje Yana jiranki Mai Martaba na neman Ku to tace sannan ammin ta koma wajen bakinta.

Tunda tafito yazuba mata eyes sau daya ta kalleshi tayi kasa da kanta harta karaso bude Mata motar yayi saida ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ya tada motar suka bar part din shuru ne ya ratsa motar har suka karasa fada kokarin bude kofa take yace a a madam tsaya mana bude wa yayi ya fito sannan ya zagaya ya bude Mata rankwafowa yayi ya gyara Mata veil din sannan ya mika Mata hannun sa kallon sa tayi yayi murmushi hannun nata ta daura saman nasa sannan ta fito tare suka jera cikin fada , fadawa nata Mika masu gaisuwa acan suka samu abba sai manira da Imran da alama su ake jira, karasawa sukayi suka gaishe da maimartaba sannan suka gaishe da abba Musabaha sukayi shi da Imran sannan yakoma ya zauna kusa da mahreen data sunkuyar dakai kasa abba ne yafara magana kamar haka nasan Kai Maher da mahreen da kuma ke manira zakuyi mamaki da yadda kukaji abun wato abun daya faru shine ana baifi saura awa biyar a daura auren ba wanna yaro dan Albarka ya fada Yana nuna Imran yazo nan fada ya bukaci yin magana dani da Mai Martaba duk da a lokacin ni ina cikin kidima halin dakai Maher kake ciki gashi kuma Kana kokarin rasata gaba daya hakan nazo nan fada muka zauna abun daya fara fada shine ya bar maka mahreen nan muka tambayeshi dalili yake ce mana a lokacin mahreen tana asibiti kuma rashin lafiyar saboda Kaine kamar yadda kaima kake asibiti ta dalilinta dan haka shi ya sadaukar da soyayyar dayakewa mahreen saboda farin cikinta sosai naji dadin hakan Wanda har yasa nace in har bazai takura ba na bashi auran yata manira bai min musu ba ya amince da Allah yasa hakan shi yafi alheri nan na samu mama Fulani da amminku na fada masu Amma na nemi a boye maki ke manira har sai na fada maki da kaina to kunji dalilin , Maher ne ya Mike ya karasa wajen Imran ya rungume shi nagode Dan uwa nagode da sadaukar war dakamin Allah yakara zuminci murmushi yayi shima bakomai dan uwa kuma sirikina shima murmushin yayi kafin Mai martaba yayi gyaran murya duk nutsuwa sukayi nasiha ya musu sosai sannan ya basu umarnin tashi Imran ne ya musu sallama ya fita abba ne yace manira ta tashi ta bishi cike da kunya ta Mike ta bishi juyowa yayi wajen Maher naji Ayman yace ka nemi visa zaku tashi a satin nan eh abba in sha allah, to Masha Allah Amma inaso kasani a nan masarauta zaka zauna nasa an gyara ma part guda naji amminka tana cewa wai kace daka gyara gidanka zaka koma to ban aminceba kansa akasa yace to abba yadda kace haka zaayi , to Allah yamuku Albarka da ameen suka amsa sannan suka tashi suka fito.

Juyowa yayi jin kukanta da baya ya dawo sunshine kukan na miye kuma oh nagane tsohuwar soyayyar ce ta motsa ko ya fada yana juyawa dan cigaba da tafiya a dan fusace ta baya yaji ta rungumoshi I'm so sorry ba abinda kake tunani bane ta fada cikin kukan juyowa yayi yace is okay daina kukan to yaja hannun ta dan ganin Ido yayi yawa a wajen .

8:00pm

Manira da mahreen na hango cikin wata alkyabba ta alfarma yan bikine suke ta shige da fice awajen hall din nawal naga ta fito a motar ganin Imran ya doso su magana sukayi Naga ya karasa ta gefen manira ya fito da ita wasu ganin motoci ne guda hudu suka Shigo filin ta farko Ayman ne da husna suka fito sauran kuma abokan Maher ne wanda rabin su Ayman ne ya gayya to su, Ayman dinne ya zagayo motar da Maher yake yace bros inaga fa kaikadai ake Jira ,sun karasone ya tambaya eh inajin ma mahreen dince kawai a motar take jiranka fitowa yayi ya fara takawa zuwa motar ya rankwafa ya kamo hannayenta duka dagowa tayi suka hada Ido gira ya dage Mata gira fitowa tayi kafarta ce ta dan gurde tayi baya zata fadi ya tarota ta fada kirjinsa rikeshi tayi gam dan ta tsorata har saida ya dagota hular alkyabbar ya daga my sunshine you look so gorgeous amma Mai kwalliyar tayi kuskure ka dan tissue ya zaro a aljihunsa ya kamo habarta jan bakin da aka samata maroon ya gogeshi tas bata fuska tayi sorry baby kinfi kyau a haka maida mata hular yayi sannan ya kama hannun ta suka gara tafiya nan shima Imran yafito da manira daga motarsa , amaren ne suka fara shiga Inda husna ta tsaya gefen mahreen nawal ta tsaya gefen manira dama ba wasu friends bane dasu saida suka shige tukun Suma angwayen da friends dinsu suka jera suka wuce , anci an sha anyi games tsakanin amare da angwaye sai wajen 12:30 aka tashi angwaye suka dauki amaren su suka wuce.

Suna Shiga part dinsu ta zame hannunta ta zauna a parlour dakinta ya nuna Mata sañnan ya wuce tashi tayi ta shiga nan taga akwatuna guda 24 da alama na lefe ne kayan jikinta kawai tarage ta watsa ruwa ta fada gado.

kwana biyu tsakani ya shigo dakin zaune take akan gado tana faman latsa waya wata karamar vest ce a jikinta sai wando Wanda da kadan ya wuce guiwarta kallo daya ya Mata ya kauda Kai tun ranar da suka dawo daga dinner sai yau suka sake haduwa bakin gadon ya zauna good afternoon tace kasa kasa murnushi yayi noon my sunshine dama zuwa nayi nafada maki ki shirya kayanki anjima zamuyi tafiya flight din 9 zamubi idan an idar da sallar laasar zamuje kiyiwa aunty ummi sallama, Tom Allah ya kaimu ameen yace ya Mike ya fita . 3:30 ta tashi ta Shiga wanka hadawa tayi da alwalar sallar laasar doguwar Riga tasa da hijab tayi salla sannan ta cire rigar tayi shafe shafenta akwatinta na gida Wanda jiya su nawal suka kawo Mata ta bude atampa ta dauka dinkin doguwar Riga tasa sannan ta gyara kanta mayafi ta dauko da jaka da takalmi ta ajje gefe ganin har yanzu Bai shigo ba yasa taja akwatunan lefenta ta Fara hada abubuwan bukatarta Wanda zasuyi tafiya dasu tana gama shiryawa yana shigowa cikin farar shadda da alkyabba Baka hannun sa rike da wata alkyabbar irin tasa black Amma ta Mata ce sorry nayi delay ko karbi kisa zamu Fara biyawa fada sannan zamuje part din Ammi da kuma wajen granny da nace saimun dawo Amma Naga yanzun zai fi kawai ,mayafinta ta dauka tayi rolling tare da karbar Alkyabbar tana Dan yatsina fuska Jin nauyin ta murmushi yayi Nima basan Sawa nakeba nauyi takemin a jiki ,ganin ba daidai tasa ba yasa ya gyara Mata sañnan ya Riko hannun ta suka fito bude musu gidan Baya akayi Saida tafara shiga ya rufe sannan yazagaya ya Shiga shima fada suka Fara zuwa tun daga bakin kofa ake Mika masu gaisuwa har suka Shiga cike fadar take da mutane hakan yasa ya Kara Jan hular alkyabbar Dan rufe fuskarta sosai Saida suka Mika gaisuwa wajen sarki sannan suka gaishe da waziri Basu Dade ba suka fito sashin granny suka biya Saida suka taba Yan wasanni na Kaka da jikokinta sannan sukayi part din Ammi Wanda sai kusan magrip suka samu suka fito a gidan aunty ummi ya ajje ta yace zaije masallaci yayi salla idan ya dawo zai kirata, a lokacin daya kirata kuwa kamar zatayi kuka haka ta tashi ta fito bayan aunty ummi tasake Mata nasiha Mai ratsa jiki , jiki a sanyaye tafito suka tafi, suna komawa gida kayansu suka dauka sukayi airport a Dubai suka yada zango satinsu biyu suka wuce umrah sannan suka yada zango a paris (france) apartment guda ya kama masu Zama suke Mai cike da farin ciki da walwala.

7 MONTHS LATER

Mahreen ce zaune Akan kujera Sanye take da mini skirt da half vest tayiwa gashin ta style ta daure Shi a gefe popcorn takeci hankali kwance duba nayi wajen Maher dayayi matashi da cinyar mahreen Yana karanta Mata wani novel Mai abun dariya sosai take jin dadin novel din Dan sai dariyarta take cike da nishadi Dan tsagaitawa tayi sannan tace moonlight wai yaushene tafiyar tamu ne naji Kayi shuru kasan idan bamu jeba Ammi da aunty ummi baza suji dadi ba tafada cikin shagwaba lakace Mata hanci yayi sunshine kinfiya rigima fa Nima da nafiso sai babyna ya bayyana kansa tukun yafada Yana shafo karamin cikinta da baifi three months ba, nidai a a ban yarda ba bikin Ayman fa da husna ga na nawal kuma gsky Bai kamata ba murmushi yayi Wasa nake maki har nayi booking flight a week dinda zaa Fara bikin zamuje saboda banaso kiyi nisa Dani Amma fa ko bikin nawal aka Fara saidai kije ki dawo Amma Banda kwana nifa nafijin dadin nan Dan haka nan zamu tattaro mudawo gaba daya koya kikace abinda kace haka zaayi my man tafada tana shafa kansa mikewa yayi sunshine I want to feel my baby's warmth ya fada Yana daukanta cilak sukayi daki.

TAMMAT BI HAMDULILLAH

anan na kawo karshen novel Dina Mai suna MAHREEN kuci gaba da bibiyar novels Dina domin fadakantar nishadantarwa da kuma ilmantarwa taku har kullum YOUNG WRITER .