Chapter 19:RDBG
RAUNIN DA BA A GANI
Meefat ink ✍️ writers
Bayan MC ya kammala gabatarda manyan baki sai ya dan murmusa ya kalli jama'ar dake cikin babban hall din “alhamdulilla, yanzu zamushiga babban bangaren taron the awards presentation” hall ya kaure da tafi MC yacigaba “kamar yadda kuka sani ba kowani dalibine ke samun damar hawa wannan stage dinba, ayau zamu karrama wadanda sukayi fice wadanda suka nuna cewa jajircewa, biyayya da kokari suna kai mutum ga nasara” sai yadan dakata “saboda haka muna rokon duk wanda aka kira sunansa yafito cikin nutsuwa kuma kowa ya karfafasu da tafi because every success deserves to be celebrated” adaidai time dinda yafara fadan hakan kowa yadaina abunda yakeyi har servers dindake ta zagaya wa suna serving MC yacigaba “please lets give a round of applause” hall ya kaure da tafi.
a VIP section jayne ya jingina da kujera yayi kasada murya yace “kaga students dinnan, wasu daga cikinsu zasu iya zama ma’aikata a companynmu nan da wasu shekaru” azan yagyada kai cikin nutsuwa yace “inhar sun cancanci zama ko daga wace jiya, kasa ko gida suke to tabbass zasu samu aiki da zasu tallafawa na kasa dasu"murmushi jay yayi sannan yace “that's why nake yinka my man”.
MC yabude wani envelope nafarko yace “our first award… The faculty of engineering" akayi tafi “award ne da ake bawa dalibinda ya kirkire abinda zai anfani al’umma congratulations to Mr Ibrahim musa” wani saurayi yamike daga bangaren engineering abokansa suka saka ihu “Ib, Ib, Ib,Ib,” aiko sai aka saka dariya MC yayi murmushi sannan yace “to present this award may i respectfully invite… THE HONOURABLE COMMISSIONER FOR SCIENCE AND TECHNOLOGY” ai sai hall ya kaure da tafi, commissioner yahau kan stage ya karbi plaque yayi musabaha da Ibrahim ya mikamasa certificate ai sai naga flashes ko taina ana daukar su ahoto sai commissioner yacire envelope daga aljihunsa yace “young man keep brightening” hall yayi shuru na dan wani lokaci sai MC ya tambaya cikeda faraa “sir can we know what it is?” commissioner yayi murmushi yace “two thousand US dollars” nan take hall ya kaure da ihu da tafi Ibrahim ya rasa abin cewa murya na rawa yace “thanks so much sir Allah yasaka da alkhairi”. MC yacigaba sai hall yayi tsitt “our next recipient… Faculty of Agriculture” da haka aka cigabada bada award wasu manyan suna bada scholarships wasu internships wasu kuma suna alkawarin samun aiki bayan sun gama karatu.
Ruhainace ke kallon komai cikin mamaki dan wannan ne karan farko na halartanta taron a makarantar “ban taba ganin taro irin wannan ba fina” tafada ma fina cikin rada, murmushi fina tayi tace “nima” sai meenat tayi caraf tace “yanzu na fahimci dalilin da yasa ake cewa wannan shine babban taro a Universityn gabadaya ”. Agefe guda azan ne yasake juyawa bangaren su ruhy akaro na ba adadi dan so yake yaga fuskar yarinyar da kyau, sai yaji jay na mgn kasa kasa, da idan kagansu bazaka taba gane cewa mgn sukeba wannan solonsune tun suna yara “wani lokacin certificate kadai baya wadatarda ma tashi, opportunity… shine yakesa rayuwa tasauya” gyada kai azan yayi yace “hakane shiyasa nakeso mu kara internship dinmu daga shekara mai zuwa” sai Jay yace “kara wa kuma” “eh ba iya hamsin ba inaso mu dauki akalla 150 ko fiyeda haka”