HARAMTACCIYAR GADA

1

by @hafnancy

HARAMTACCIYAR GADA.

*{Haɗuwar rayuka da ƙaddara ta tattara wuri guda.*🔥💔}

NA

HAFSAT MUSTAPHA ('Yar Mutan Naija).

SADAUKARWA GA UWARƊAKI NA: HAJIYA ZAINAB AHMAD (HAJIYA MAMA). AMINCIN  ALLAH DA NI'IMOMINSA SU TABBATA A GAREKI UWATA.

Ban kirkiri wannan littafin da nufin tozarta wani ko wata ba. Na rubuta shi ne domin na samar da natsuwa a zukatan masu karatu.

LITTAFIN NAN HAKKIN MALLAKA NA HAFSAT MUSTAPHA NE, BAN YARDA WANI YA JUYA MIN SHI, KO YA YI AMFANI DA WANI ƁANGARE NA LABARIN BA. SANNAN BAN YARDA A ƊORA A WATA KAFA TA MEDIA BA TARE DA NEMAN IZINA BA.

Bismillahir Rahmanir Raheem.....

BOOK 1

PAGE 1.

KADUNA/NIGERIA.

SUNDAY: 3PM

"Wallahi ba zai yiwu ba! ba zai taɓa yuwuwa ba! idan na yarda, ashe ni ɗin sha-ka-tafi- ne haihuwar saratu ɗan asara."

Ya furta cikin jin zafin rashin mutuncin da aka gurza masa. Sai daya fesar da zazzafar huci kan ya ci gaba da magana zuciyarsa na bala'in ƙuna "'Yar iska! Haihuwar gaba da fatiha! Na rantse ba ki isa ki ci kuɗina a banza kuma ban samu biyan bukata ba. Ke har kin isa ki min wayau? 'Yar kwalta fa? da bata ga wata sana'a mai daraja ba sai ta tsayuwa a bakin titi ana jiran masu kuɗin gari domin su ƙwaƙula su bar wa saura."

Wata mai suna 'Yar Gala ta ɗaga murya ta ce"Sai fa kayi da gaske ko kuma ta yi awon gaba da kuɗinka. Gaka nan zabgege da kai kamar mai wayau amma har ka iya bari 'yar kucakar yarinya da bakinta bai gama ƙarnin nono ba tasa hannu ta ƙwaci kuɗi a hannunka ta sokesu cikin rigar mama. Yanzu ko kunya baka ji ba? kana kallo baka ɗau mataki ba, zaka fito nan ka tsaya kikam a tsakiyar mata kamar iccen dabino kana ɗaga mana murya. Mu ne kake so mu shiga mu ƙwato maka kuɗin ko ɗanne maka ita kake so ayi?"

"Ke!! Sa idonki cikin nawa."

Ya furta zuciyarsa na ci gaba da tafarfasa. Sai daya tabbatar da ta harmutsa idanunta cikin nashi sannan ya ce" Dan uwarki ban ce ki shiga cikin maganar nan ba don ban ga kowa ba in ba ita ba a gidan nan. Kuma wallahi sai nayi abin mamaki da zai sa ku gane haukar tawa bata banza bace."

Ya faɗa da ƙarfi yana kallon inda take zaune cikin wasu mata mazauna gidan, sun fito shan iska ana hira da shewa.

Tun da Ghali ya fito daga ɗakin wacce take ƙoƙarin cin kuɗinsa ya fara musu hauka a tsakar gida babu wanda ya bi ta kansa sai 'Yar Gala da bata iya gani tayi shiru.

'Yar Gala ta dube shi ta banka masa harara kamar idanunta za su faɗo ta ce" To, sai kayi mu gani."

Ta ja baki tayi shiru don ta fara ɗan tsorata da yanayinsa.

Kada kai ya yi yana faɗi cikin ɗaga murya yadda ya san wacce taci amanarsa zata iya jiyo shi"Idan fakewa kike da cutar mutane. To billahil lazi la ila ha illa huwa ko dai ki fitomun da dubu hamsin ɗina, ko kuma ki bani abin da nake kwaɗayi don a zauna lafiya. Idan kuma kika nuna tirjiya zaki jawo zuciya tasa in ƙona wannan gidan matan gabaki ɗaya kowa ma ya hallaka in yaso ma haɗu gaban Allah ayi yacce za ayi kawai."

Jin kalamansa na ƙarshe yasa sauran ƙwailaye da gogaggun 'yan matan gidan yin wuff! suka fiffito tsakar makeken gidan a inda su kayi arangama da mutumin da ke son ganin bayansu a dalilin mutum ɗaya tak!

Shi dai ba matashi ba balle kace da sauran hankali, akalla ya doshi shekaru arba'in da dori.

"Me nake gani kamar hula a cikin gidan nan?"

Furucin da Shugabarsu mai suna Jidda ta fara furtawa kenan lokacin da idonta ya sauka kan Ghali da ke tsaye kamar mayunwacin Zaki.

Kasancewar daga bacci ta taso yasa ta murza ido domin ta tabbatar da abin da idanunta ke gaya mata.

Wani tsawa ta daka ranta a mugun ɓace ta ce"Waya jawo hula cikin gidan nan?"

Tambaya ta watso da idanunta cikin nasa babu alamun tsoro a tare da ita. Hakan ya ƙara ba wa Ghali mamaki don yanayin tsayuwarta da action ɗinta ya tabbatar masa da lallai ita mai baza capacity ne a gidan.

Bata jira jin ta bakin kowa ba don shakkarta ake. Ta ce tana kallon kwayar idonsa"Malam! ya zaka shigo mana gida kana hauka kamar gwaggon biri? har da cin alwashin ƙona mafakar da muka dogara da ita damu a ciki? shin nan ɗin ya maka kama ne da gidan ubale? Na tabbata dai gwanjo ba sabon abu bane a wurinka. Ko ba wannan da aka hana maka ba, kana iya samunsa a wani waje. Gwanjo na ko'ina domin wani sawa ɗaya zai mata sannan ya watsar wani ya taya."

Shiru ta yi tana jiran jin ta bakinsa amma ya kasa tofa koda kalma ɗaya saboda tsananin mamakin hausar data dunƙula, da mai gane fassararsa sai wanda ya san duniya.

"To, a kan wani dalili zaka cika mana gida da hayaniya saboda kuɗinka na siyan kayan makulashe?"

Shiru babu amsa don jikinsa ne ya mutu da irin cin mutuncin data masa.

Waigawa tayi ga yan'uwanta cikin buɗa ido ta ce" Zan yi tambaya For the last time, wacece ta jawo mana hula gida? Kuma da rana gantsal haka? Ku faɗa min ko wata shegiyar ce ta ɗebo mana jaraba cikin gida har yake barazana da rayukanmu duka?"

"Ina tunanin Saffy ce don tunda ta shigo gidan nan ta karya doka na kawo maza amma haka dai kullum ake rabuwa baram-baram. Sai ta yi dabarunta yadda kuɗaɗe zasu shiga hannunta sannan ta musu tozarcin da zai sa su hanzarta barin gidan nan babu shiri."

Jin haka yasa Ghali saurin taran numfashinta bayan ya haɗiye wani kakkauran yawu na takaici.

''Au! dama ashe ba kaina ne farau ba? Kenan akwai waƴanda ta cutar kafin ni? to wallahi ku rubuta ku ajiye nine ƙarau kuma.."

Cike da Zafi Jidda ta katseshi "Kai dallah malam yi mana shiru , ko an gaya maka haukar taka ce zata iya magance matsalar da kake ciki?"

Juyawa tayi tana duban sauran 'yan'uwan nata tace''Wacece Saffy? an yi sabuwa ne a gidan bayan tafiyata?"

Kasancewar jiya ta dawo daga Ingila tare da Alhajinta. Kuma akalla sun kwashi wata uku a can shiyasa bata da labarin Saffy wacce dududu bata cike wata biyu da shigowa gidan ba.

Wata tace''Eh ga dakinta can "

Ta furta tana nuna wani single room.

''Wacce shegiyar ce acikinku ta kawo mana matsala gida ? in tasan bata shirya zama ba menene na shigowa ?"

Jidda ta furta idanunta akan dakin, Fuskarta dauke da bacin rai tsantsa.

''Sady Done ce ta kawota."

Aka bata amsa a taƙaice.

Tace"Ina Sadyn take?"

"Bata gari"

"Ku min magana da yarinyar maza ina son ganinta."

Ta bada Umarni, har wata mai suna Beeba ta nufi ɗakin, ko mai ta tuna kuma sai kawai tace"Dakata! bari in sameta da kaina."

Nufar dakin tayi aka bita da kallo har shi Ghalin da bakinsa ya mutu nashi sai ido yana kallon ikon Allah. Sai a yanzu yake jin wani uban kunya ya lulluɓeshi ganin idanun duka matan gidan akansa yake, daga mai watsa mishi harara sai mai zuba ashariya.

Tana nan zaune agefen madaidaicin katifarta duk ta takure kanta wuri daya, kanta akasa sai tsiyayar hawaye take, tunda Jidda ta fara balli atsakar gidan gabanta ya shiga aikin faɗiwa.

Bata taɓa ganinta ba amma haka kawai taji bata sha'awar ma haɗa idanu da ita.

''Ina shegiyar take ne kina ji ana magana kinyi zamanki a ɗaka don kin rainani ko kuwa faɗa miki matsayina a gidan mata ne ba ayi ba? To ki sani ni ce shugabar duk wata 'yar high a cikin gidan nan."

Bakinta ne ya mutu asa'ilin da ƙwayar idanunta suka harmutse cikin na wacce aka ambato da Saffy, jin wani tsananin faduwar gaba tayi wanda tunda uwarta ta haifeta bata taɓa jin irinsa ba.

SAFIYYA... ta furta da karyayyen murya gami da saurin nufar inda take da mataccen jiki saɓanin da data shigo da zafinta.

Wacce aka kira da Safiyya ta miƙe akiɗime tana kallon Jidda. Har ta mutu bazata taɓa manta da wannan fuskar ba.

Ita ma da karyayyen muryar tace''Yaya Jidda kece ? me kikeyi anan ɗin?"

"A'a Safiyya kece dai zan tambaya ko mai ya kawoki gidan mata ? Me kika zo yi ƙanwata? Ke ce Saffyn da ake magana akai ?''

Da hanzari ta nufeta ta rungumeta gami da fashewa da kuka tana faɗin"Yaya Jidda ashe zan sake saki a ido ? tsawon shekarun nan ashe kina gidan mata bamu sani ba ? Tabbas ni ce Saffyn data kawo muku matsala gida."

Runtse idanu tayi tana jin yadda kukan ƙanwar tata ke dukan zuciyarta.

"Ina Abie da sheɗaniyar matarsa ?"

Bayan tayi tambayar sai kuma ta girgiza kai ta ce ɗauke da murmushin takaici"Kodayake bai kamata nayi tambaya kan uban da ya yi sanadin shiga ta duniya ba."

Cikin rashin jin daɗi Saffy ta ce"Kowa na lafiya kuma nima gudowa nayi bayan na samu labarin tarin alkhairin gidan mata. Sai dai daga zuwana na gano cewa zaka ji daɗin zama amma kuɗin haraji shi ne matsalar."

Hawaye ya wanke mata fuska. Girgiza kai Jidda ta shiga yi ita ma hawaye masu Zafi na saukar mata saman kunci tace "A'a k'anwata zaman gidan nan bai dace dake ba, ki koma gida kawai Allah na tare dake. Ki bari ni dana fara wannan rayuwar in ci gaba amma bazan so ace 'yar'uwata da nake jinta a raina ace ita ma ta hau kan gadar da nake kai ba, please Safiyya ki koma gida."

"Yaya wallahi bazan iya ba! bazan tab'a bari ki sake kufcemun ba. Daga yanzu inaso in kasance tare dake har ƙarshen numfashina."

Ta furta hakan da iya gaskiyarta tana sakin kuka me tsuma zuciya.

Jidda tace" Safiyya, wallahi banso ace Allah zai sake ƙaddara haduwarmu in buɗe ido in ganki kan gadar da nake daka tsallen biri a kai ba. Yanzu nufinki kema irin tsallen dana keyi shi kika zo yi kuma a biyaki?"

Girgiza kai tayi tana"Har fa rikici ake da ke kan gwanjo. Wallahi naso ace in sake haduwa dake kina matsayin matar aure amma ba a gidan mata ba ƙanwata."

kuka yaci mugun ƙarfinta jikinta har rawa yake......

"Ni fa kudina nake jira in kama gabana amma naga kema kin shige baki fito ba kodai had'a baki ku kayi ne ban sani ba ?"

Haka suka ji Ghali ya furta daga can tsakar gidan, nan take duk suka dawo hayyacinsu, Jidda tace"Ina kuɗaɗensa ? bani in mayar masa ban son matsala. Kin san bazaki bari ya amfana da jikinki ba to meyasa kika karbi kudinsa ? ki kiyaye naji ance kina samun matsala irin haka kuma daga yau kar in sake ganin kin gayyato rijalu cikin gidan nan domin an kafa doka na hanasu shigowa sai dai ka fita ka haɗu dasu a wani wuri. Zan sa tsatssauran doka tunda naga babu wanda ya ɗauki abun serious. Idan kika sake kawo wani kuka yi rigima ina mai tabbatar miki zaki samu matsala da Uwar ɗakinmu Samha.

Runtse idanu tayi wasu siraran hawaye suka gangaro mata tace"Naji insha Allahu Zan kiyaye! amma kiyi hakuri yaya bazan iya bashi wannan kudin ba don watan nan ne yakamata in fara bawa uwarɗaki Kudin haraji "

"Karki damu zaki ban akawunt nombanki idan lokaci ya gabato zan biya miki. Wannan kuɗin dai ki kawo in mayar masa mu samu mu kashe case d'in nan "

Bata musa mata ba, tasa hannu cikin rigar mamanta ta ciro kudin ta damƙa mata.

Har ta juya zata fita, Saffy tayi saurin damk'o hannunta, da rawar murya tace"Yaya Jidda yaushe zan sake saki a ido ? don ga dukkan alamu kina da wuyar gani kuma ni bana so ki sake guje min. Ke kadai ce kawai ta sauramun aduniyata, Yayata please..."

Sosai jikin Jidda yayi bala'in sanyi, ita kanta zata so ace ta kasance da yar'uwar tata har karshen numfashinta amma abu ne mai wahala sabida irin rayuwar da suka tsinci kansu ciki, wanda ba a son ransu bane suka wayi gari acikin wannan gidan.

"Insha Allahu zanyi ƙoƙarin kasancewa a kusa dake amma ban miki alƙawarin ganina a kodayaushe ba. Sannan ina so ki ɓoye dangantakar dake tsakanina dake, ki rufe wannan sirrin bana son wani ya san cewa ke ɗin yar'uwata ce, kinji ko? ki kiyaye."

Gyad'a mata kai kawai tayi amma ko kadan bata so hakan ba, daga haka ta fice bayan ta karbi akawunt nombanta da lambar wayarta.

Ta sallami Ghali tare da masa gargadi da babban murya akan karta sake ganin kafarsa awannan gidan.

Komawa bangarenta tayi wanda ita da mataimakiyarta Salamatu da suke kira SALA ne kaɗai suka mallaki safe contain kasancewar su aka ba shugabanci. Duk sauran a single rooms suke da banɗakuna a waje. Wasu ɗakunan, mata kamar biyu zuwa uku ne a ciki amma ɗakin da Saffy take, ita ce farkon shiga kuma har yanzu bata kai ga samun abokiyar zama ba.

Matasa mata ne daga 18years amma ba a karban wacce ta haura 40. Shekaru na ɗaya daga cikin tsarin  da Samha take dubawa kafin ta karɓi duk wata 'ya mace da take da bukatar zama a gidan nata.

Afkawa tayi cikin Tunanin irin sabuwar rayuwar da zasu shimfiɗa da k'anwar tata amatsayinsu na mazauna gidan mata. Ga Ya ga kanwa babu mai k'wabon wani acikinsu.

UWARƊAKI- SAMHA.

Samha ce hakimce saman kujera akatafaren falonta tayi shiga ta alfarma sai baza kamshi take, bubu na lace ne ajikinta ruwan kore wanda yakara haska fatarta kasancewar ita d'in mai farar fata ce kuma tana ɗan karawa dana kanti.

Gefenta aminiyarta ce Hadiza, itama cikin shiga ta alfarma.

Fira suke tabawa sama sama don Samha tafi bada hankali ne akan system d'in dake gabanta, sai latsansa take cike da kwarewa.

Can wayarta tayi kara ta daga,

"whaatt?"

Shine abin da ya soma fitowa daga bakinta.

Can tace"Gaskiya ya zama dole in dau mataki kafin yarinyar nan tazo ta zame min matsala, ina Jidda? ita wani matakin ta ɗauka ? don a iya sanina itace yakamata ta fara daukar mataki, sai idan abun yafi karfinta shine ni zansa hannu."

Tab'e baki mai gulma tayi kan tace

"Wallahi uwarɗaki babu matakin data ɗauka, gani muke ma kamar lallamin yarinyar tayi sannan ta karbo kudi ta maida masa kuma daga haka bata sake cewa komai akai ba shiyasa naga dacewar na kiraki na fad'a miki halin da ake ciki tun wuri kafin muzo muna cizon d'an yatsa "

Ajiyar zuciya me zafi ta sauke sannan tace,

"Shikenan nagode kwarai yanzu zan buga warning acikin group chat da kaina don kar inzo in dau mataki aga laifina."

Cike da farin ciki mai gulman tace" To, Uwarɗaki amma dan Allah karki nuna kamar nina gaya miki "

"A'a kar ki samu damuwa zan yi komai a ilimance ne."

Ta datse call d'in tana cigaba da masifa, Hadiza na mata magana ma ko sauraronta taki, ta kunna data ta hau whatsApp, group chat nasu mai suna GIDAN MATA ta shiga tayi dropping message kamar haka bayan tayi sallama.

"Abin da ya faru ayau a GIDAN MATA ya shiga kunnena! kuma ba tun yau nake da labarin hakan ba amma na zuba idanu ne kawai ina kallo atunanina zata canza amma gani nayi abun dad'a gaba yake yi. Har yanzu ban sata a ido ba kuma bana bukatar saninta. Sady done ki ja mata kunni in har tasan bata shirya zaman gidana ba ta tashi taban wuri kafin nadau mataki! Jidda ina da labarin kina gari tun jiya, don haka kiyiwa tufkar hanci dan muddin ta sake na shigo cikin zancen nan wallahi na rantse da Allah saina wulakantata! bazai yiwu in bata daki kyauta ta zauna babu ko kwabon da zata biya ba, nawa kawai a dinga kawomun kuɗin haraji duk bayan wata biyu. Last month na ɗaga mata kafa tunda shigarta kenan kuma duk wacce ta shigo gidana a watan farko na kan ɗaga mata kafa. Wannan watan za ta fara bayar da kuɗin haraji kuma idan ta kawo min matsala da biya sai na bata mamaki.

Ku gayamin idan ta ci gaba da bada matsala taya kuke ganin zata iya biyan bukatun kanta har kuma ta dinga biyan kuɗin haraji ? to na rantse da Allah ku gaya mata ta kiyayi haduwata da ita! in har tasan bata shirya ba tabar min gida don bada kudinta na gina wannan gidan ba! sannan kafin na kafa shi ban nemi shawara daga wurinta ko wurin mai dattin hula ba. Jidda na sake fad'a ki dau mataki ko in dauka, har kan maganar shigar masu hula gidana. It has to stop don bana so a lalata min suna......A huta lafiya.

Kafin kace meye wannan, tuni kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa, dama akwai masu jin haushin Saffy har da masu kiranta da slow poison.

"Wallahi Uwarɗaki ki dau mataki, akan me yarinya karama zata jawo akonemu gaba daya tun bamu tuba mun kama Allah ba "

"Uwarɗaki ko ni in tayaki yin waje da ita ne ?"

"Hajjaju ayi mata hakuri bi'izinillahi zamu canzata don ga dukkan alamu bata waye ba."

Reply's ɗin da suke ta bata kenan.

Jikinta ne ya ɗauki rawa sosai bayan ta karanta. Hawaye masu dumi suka wanke mata fuska, sai salati kawai take tayi da kuma nadamar shigowa gida kamar wannan. Amma kuma idan ta tuna daga inda ta fito, sai taji kawai gwara mata wannan rayuwar akan na gidansu.

Itama Jiddan ta gani, girgiza kai kawai tayi dan tasan duk inda aka fi biyu to tabbas za'a samu munafukai aciki.

"Noted Uwata."

Shi ne reply data bata, kuma nata ne kawai Samha tayi reply, bata kula sauran ba hakan kuma ya kara kufular dasu dan sosai suke son cusa kai gareta amma ita tafi ji da Jidda domin ita ce alkhairinta ta farko da kowa sai ya biyota.

Kai tsaye ta tuntuɓi Saffy ta private suka fara chatting. Ta ce " Safiyya kibar gidan nan please bai dace dake ba "

Da sauri ta mata reply"Yaya, bana tunanin ko a mafarki zan sake bari muyi nesa da juna. Koda ban ganki anan ba zan rayu a cikinsa don rayuwar gidan nan ya fi min rayuwar gidanmu."

"Hmmm! Safiyya rayuwar nan bai dace da ke ba. Bana so ki shiga wani hali a kan kuɗin haraji don naga baki shirya zama cikinmu ba. "

"Ina so in kasance tare dake JIDDATULKHAIR... kece uwata! kece ubana! kuma yar'uwa daya kwal da nake ganin Allah ya bani."

kuka sosai Jidda ta fashe dashi tana tausayinsu duka, da rawar hannu ta mayar mata da reply" ki sameni gobe da safe misalin sha daya a Alkaleri's kitchen na karamin branch ai kin san wurin ko ? sai mu tattauna "

"Zan dai yi tambaya tunda ba ko'ina na sani ba, kuma zanzo insha Allah."

"Good yanzun idan kin tashi biyan kuɗin haraji, ki sanar min sai insa miki kuɗi cikin akawunt. Amma yanzu dai zan miki transfer na 100k da zaki kular min da kanki."

Cike da farin ciki ta hau mata godiya, ko sakwan 30 ba ayi ba taga alart d'in dubu darin ya shigo mata.

A take ta aika ma Jidda da sakon godiya zuciyarta cike fal da jin daɗi.

****

"Samha ni dai bazan gaji da miki nasiha ba! Allah ma yana gani amatsayina na aminiyarki ina baki shawara amma k'in daukawa ne kikai. sana'ar da kike yi sam bai halatta ba, haramtacce ne, ki rushe wannan gidan matan ki kama wata sana'a mana dan Allah wanda ya halasta. Ga nasa'o'i nan masu albarka iri iri wanda in ka tsai da gaskiya da amana sai kaga Allah ya bud'a maka. Wallahi ko daddawa kika dauka kina yawo dashi yafi wannan sana'ar da kikeyi. kin zuba yara a gida kina cutar dasu da wayau amma basu ganin haka sai kyautatawar da kike musu. Wata ma na tabbata ba karamin hali take shiga akan kudin harajin nan ba, nawa ta tara na kanta balle ta biya kudin wani haraji ? Allah Samha ki dawo kan hanya kar masifu suzo su sauka kanki daga baya kizo kina nadama."

Da sauri ta daga mata hannu ranta na suya ta cire farin gilashin idanunta ta ajje gefe, k'wayar idanun sun soma canza kala tsabar b'acin rai.

Ta ce"Look Hadiza! nasha gaya miki ke baki taka matsayin da har zaki zauna kina bani gurguwar shawararki ba. Ni na zabarwa kaina sana'a ba uban kowa ba wanda kuma yaga bazai iya jure gani ba to yafita daga rayuwata, tunda har nake da daurin gindin mahaifiyata da albarkarta to kar uban kowa yasa. Mahassadan banza kawai masu bak'in ciki da cigaban wani "

"lallai Samha ni nema nake miki bak'in ciki da haramtacciyar sana'ar da kike yi ? babu komai Allah ya taimaka "

"Ameeen, tashi kibar mun gida."

Murmushi kawai Hadiza keyi cike da mamakinta. Sai data miƙe ta ce"Samha, koda ba zaki ɗau maganata kiyi aiki da shi ba, zan sake faɗa ki bar wasa da rayuwar 'ya'yan mutane. Ina mai tabbatar miki, rana ɗaya za kiyi nadama. Rana ɗaya zaki nemi wuri domin ki ɓuya, ba zaki samu ba."

"Zaki bar gidana ko sai na baki mamaki?"

Ta furta cikin zafin rai.

Hadiza tana ji kuma tana gani ta korata daga gidan....

Haka kawai ta ji zuciyarta na son ganin saffy da ake magana akai....

Ajiyar zuciya ta sauke ajere kana ta faɗa cikin tsaleliyar motarta mai gadi ya buɗe mata ta fice. Tana so ta fara biyawa saloon a gyara mata kai, daga nan sai ta ziyarci gidan matan Samha domin aiwatar da kudirin da ke ranta.

NAGODE ALL🙏

#HaramtacciyarGada

#2026 Novel

#HAFNANCY📚✍️

***/***

NAGODE ALL❤️🙏