Babi na tara
by @dijensy
9
Jidda ce zaune gefen gadon ƙafa ɗaya kan ɗaya tunda ta samu aka kawo mata wayarta shikenan ba dama sai ta wuni kan wayarta tana danne danne hatta power bank ɗinta ta sa su Abdallah sun kawo mata sabida haka bat da matsalar charge sai ta kai sha ɗaya tana latse latse ,yau Hassan yana off baza shi aiki ba sai dai akwai tahfiz kamar koyaushe da safe ya gama wankin banɗakin ya na share musu ɗakin tana jin sa yana sharar bata ko ɗago ta kallesa ba ta ɗage ƙafarta ya share dede inda take ta mayar ta sauke ta gefen ido take harararsa kafin ta sauke wayar kan cimyarta tayi folding hannu “Anjima zan fita”Ta furta kai tsaye tana jiran ya ɗago ya kalleta ya amsata kamar ko yaushe fuskarsa da walwala ya ɗago ya gama haɗe sharar waje ɗaya dukda ma ba yawa amma sai ya ƙalƙale ko ina yake bari.
“Unguwa za a je Jidda ,ko gida?”Ya tambaya a tausashe.
“Supermarket”.Ta amsa.
Murmushi yayi yace “Toh ko zamu je tare?”
Baki ta taɓe “Na san hanya idan zaka barni kawai ka faɗa min idan kuma zuwan ne baka so ka sanar min na cire rai”Ta faɗa tana tashi ta nufi sif rai a ɓace ya bita da kallo “Ko kaɗan ni bazan hana ki ba duk inda kike so zan barki Jidda ,amma ina gida ki faɗa min me kike so kinga na hutashe ki”.Cewar Hassan ta juyo sai kuma tayi murmushin gatse “Sai a ƙara jan wasu kwanakin da zamu koma sabon gida kenan ,da kuɗina zan sayayyar da nake so”.Shiru yayi kamar yana juya maganar yace “Allah ya kaimu da ƙarfe nawa?”
“Sha ɗaya”.Ta amsa ya jinjina kai “Tohm ba matsala”.
Hassan tsintsiya da abin sharar ya mayar maajinsu kafin ya dawo ya shiga wanka ya fito yana shiryawa ,dubu biyu ya ajje mata kuɗin mota ya mata Allah ya kiyaye yasan kafin ya dawo daga makarantar ta fita Jidda ko godiya ya fita ta kwashe kuɗin tana cusawa a jakarta ƙarfe tara da rabi ta yi wanka ta shirya cikin baƙar abaya goma ta gama shirinta ta ɗan zauna jiran da rabi tana game saƙon shi ta shigo ta ja tsaki tana buɗewa ‘Kada a mance da adduar fita daga gida Allahumma barik’Ta gama karancewa ta fice tunda tayi waya ya samu ta bashi numberta ba ranar da zata wuce bai turo mata da saƙo ba na addua da hadisai rututu da ta buɗe zata ja tsaki wataran ma bata buɗewa.
Anty Ruƙayya tana tsakar gida ta ga fitowar Jiddan tana jawo ƙofar ɗakin “Ina kwana”Ta gaishe da Anty Ruƙayya ta amsa kwana buyu ta ga dama tana fara gaisheta ba kamar da ba da sai ita ke kulata.
“Fita zaki ,Allah ya tsare sai kin dawo”.Jidda ta amsa da ameen kafin ta fita.Har ta isa titi tana jan tsaki komai na unguwar haushi yake bata ta tsari ɗan sahu har supermarket.Jidda siyayya tayo fal duk abinda ranta yake so sai da ta siye ta kashe sama da dubu sabain ɗari da ɗaya ne ya rage account nata daman shine ta taɓa ta komo gida da fagon kaya daga titi tasa almajiri ya shigo mata da kayan ta bashi ɗari biyar ya tafi.A cikin kayan chocolate da ta siyo ta ɗibarwa su Amal ta kira Usman ta bashi ya tafi ta dawo ɗakin tana babbaje kayanta harda abin maƙala kayan shampoo na banɗaki da fankar hannu mai charge sai fitila da sauran kayan amfani na mata da kayan ciye ciye ta warware ta ajje su a muhallinsu ta fita kitchen ta ɗakko plate da spoon ta dawo ɗaki ta haɗa cornflake ta sha tana gamawa ta haye gado tana cigaba da danna wayarta daga baya ta ajje wayar bacci yana yin gaba da ita ba ita ta tashi ba sai wajen uku saura ta shiga banɗaki tana yin uzuri ta dauro alwala ta fito ta gabatar da zuhr tana kan dadduma Hassan ya shigo ya kalleta so ɗaya yana sauke idanunsa ga dukkan alamu sai yanzu tayi azahar.Bata cemasa komai ba ta tashi ta ninke abun sallar ta ɗora kan gado don yunwa take ji kuma tasan zai ɗauke ta zauna tana jawo tray da ke gefe tana buɗe warmer abincin ta ga alale ta mayar ta rufe tana tashi ta ɓata fuska “Mai ya faru?”Ya tambaya ganin ta bar abincin “Bana ci”.Ta amsa tana zama kan gadon daga gefe.
“Mai kike so sai a siyo miki?”Ya tambaya.
“Ko ma indomie ce”.Ta amsa don daman ɗazu ta ji shaawarta abi ɗaya ya hana ta siyo ɗanya bazata shiga ta dafa ba kuma bazata iya zuwa ta ce Anty Ruƙayya ta dafa ba amma ba don hakan ba da ta siyo.Hassan azumi yake na alhamis amma haka ya tashi ya fita inda ake sayar da indomie kanshi da nisa akwai a kusa amma yasan ba lalle ta ji daɗinta ba sai da ya je inda ake ɗan packaging me kyau ya siyo mata ya dawo Jidda ta sa hannu ta karɓe a cikin takaway ɗin ta cinye ta tass ta kora da 5alive na roba da ta siyo.
“Nan da sati ɗaya zamu tare a sabon gidanmu”.Ta ji ya furta ta kallesa “Da waɗannan kayan zamu koma?”Ta tambaya tana kallon sif ɗin ɗakin ya girgiza mata kai ba tare da ya ce komai ba Jidda bata kuma ɗora wani abun ba fatan ta Allah yasa ta tarar da gidan empty wallahi daga bakin ƙofa zata koma gidansu ta sawa Umma kuka ta faɗa musu ita bazata kwanta a danshi ba…
*****
Jidda a iya sati ɗayannan kafin si tare ta yi kaca kaca da ragowar kuɗaɗen account ɗinta duk abinda ta gani online na ciye ciye sai ta saya ga subscription na data sai da tayi ƙarƙaf ,ragowar chanjinta ta ciro a jaka tana fitowa tsakar gida Usman na tsakar gida homework yake Amal na gefe ta tashesa “Zo ,ka siyo min awara irin ta rannan da ka siyo kada ka daɗe kaji?”
Tasowa yayi ya rufe littafin ya karbi kuɗin ta koma ɗaki ya fita ko minti biyar ba ai ba sai gashi ya dawo kayan sa duk ya baɗe da ƙasa yana goge ido a sanyaye Jidda ta fito taji Amal na tambayarsa mai ya faru “Almajiran layin baya ne suka kwace min kuɗin”.Ya amsa yana hawaye Jidda ta bisa da ido yadda ta kwallafaa awararnan?
“Kai wa ya aikeka kulasu baka da karfin faɗa dasu?yanzu kuɗina fa?”
“Yana hannunsu”Ya amsa yana shessheka Jidda ta giɗa kai “Ya maka kyau”Ta faɗa tana komawa ciki Anty Ruƙayya ta kira Amal tana tambayarta ta zayyane mata komai ta kira Usman ta rarrashesa ta ce ya je ya bata haƙuri.Jidda da shigarta ɗaki ta ɗauki wayarta ta kira Hassan yana wajen aiki ya ga kiranta da mamaki bata taɓa kiransa ko shi ya kira sai ta ga dama zata ɗaga shi ma da kiran yawanci aakan tambayar mai zai taho dashi ne.Sallama yayi cikakkiya Jidda ta juya idanu alamar gajiyawa da shaaninsa komai na shi a ladafce a addinance ,ta amsa kafin ta fara magana “Na aiki Usman ya siyo min abu yara sun kwace kuɗin ka turo min wasu”.Ta faɗa kai tsaye shiru Hassan yayi na ɗan sakan kafin yace”Mai ne abin da zai siyo makin zan iya siyoshi nima ?yanzu zan tashi”.
“Awara ta dubu ɗaya”Ta amsa ta katse kiran ya bi wayar da kallo Jidda da tsarabe tsarabe akwai abinci gida amma yanzu ko abinda take so akai sai ta haɗa da wani abun aljihunsa yayi mugun ƙasa baya so yayi ƙarƙaf kafin a biyasa ,daman ragowar kuɗaɗen hidimar transport na tashin da zasi ne da cefane abinda za su buƙata yau da gobe kafin albashinsa ya sauka.Jidda na sauke wayar ta ga Usman a bakin ƙofar “Mene?”Ta tambaya sama sama muryarsa na rawa yace “Kiyi hakuri Anty”.Jidda guntun tsaki tayi “Ni wuce ka fita kar raina ya ɓaci Usman ya fita.
Har ya tashi yana shawara haka ya ƙure ya saya mata ta dubu ɗayan da ta buƙata ya dawo gida.Jidda tana ganin shi ya shigo da sallama ta miƙe tana amsawa ƙasa ƙasa ya tako ciki yana ajje mata kan tebir ta sa hannu ta ɗauka da zafinta Jidda ta tashi ta fita ta ɗakko plate ta komo ɗaki ta juyeta ciki ta fara ci.A tunaninsa bazata iya cinyewa ba amma cikin mintina ta tada ita yayi murmushi Jidda ta fisa ci nesa ba kusa ba.Yau bai je makarantar dare ba gida ya zauna ta ga yana haɗa musu kayansu ta miƙe ƙafa ko a jikinta daman ta ayyana zai yi ɗin.”Wanne zan bar miki na sakawa gobe?”Ya tambaya ta ɗago idanunta ta ɗan kalli akwatin kayan da yatsa ta masa nuni da wata doguwar rigar atamparta ya ciro mata ya ajje gefe kayan yau da ta cire ya kai toilet ya wanke mata ya zagaya ya shanya ya dawo ɗakin komai sai da ya kimtsa shi goma da arbain ta ajje wayar ba charge power ɗin ma ta shanye saura 20 ta jona tana shiga banɗaki da fitila ta haɗa ruwan ɗumi ta tuɓe kaya tana maƙalesu kan abin shower bata san ko ta ina ba kawai ta ji saukan abu kamar ƙadangare sanda ta hmaƙale kayan ya ɗare mata hannu ta kwala wani uban ihu ya hauro mata baya tana jin ƙafafunsa fitilar ta wurgar gefe ta faɗi ta fashe Hassan ya fara shirin yin shinfiɗa ya saki bargon da lalibe ta buɗe ƙofar banɗakin a guje ta fito Hassan ya ɗauka ruwan zafi ta zuba a jiki daga inda yake tsaye ta faɗa jikinshi wata karkarwa da take na fitar hankali tana karkaɓe jiki Jidda ta mance ma a halin da take a zindir ɗinta ta kankamesa tana yi kamar zata shige jikinsa Hassan ya ma rasa yacca zai don wani irin ruƙo da rungumar da ta masa numfashi kawai yake “Bayana bayana”.Ta ke kwala ihu.
“Jidda ba komai”.Ya furta yana rubbing bayanta “Ƙadangare”Ta ke furtawa gabadaya ba a hayyacinta take ba “Ya gudu babu shi”.Ya faɗa a tausashe take jin muryar a kunnenta yana jin yadda zuciyarta take bugawa sun jima a haka kafin numfashinta ya fara daidaituwa hankalinta ya fara komowa jikinta tsahon minti biyar yanzu ta farga a yadda ta ke idan ta juyo zai ga komai kuma tasan ba za su dawwama a haka ba “Babu ƙadangare Jidda Allah ya gudu fa”.Hassan ɗin ya faɗa.
“Ka rufe idonka”.Ta buƙata ya murmusa “Na rufe”Ya furta yana rintse idanunsa dukda haka bata yarda ba ta ɗago tana kallon iya haɓarsa da sajensa daga ƙasa ƙasa hannunta na dama ta kwance daga rungumar da ta masa tana rufe masa idanunsa tana kallonshi murmushi yake ya kasa rufe bakinsa tana kallon fararen haƙoransa fuskarta tsyi kicin kicin ta ke kallonsa a hankali ta ke sakin ɗaya hannun ta riƙe mishi hannu ɗaya na dama kamar kana wa makaho jagora suka tako bakin gadon blanket da yake shirin shinfiɗawa ta ɗauko tana yafe masa kansa “Ka da ka buɗe sai na ce ka buɗe”Ta buƙata tana turo baki ya jinjina kai ta saurin buɗe akwatinta ta ciro kayan baccinta ta saka don ta yafe wankan sai da ta gama ta yaye masa blanket ɗin Hassan ya sauke idanunsa kanta “Kuma bazan kwana ɗakinnan ba wallahi”Ta faɗa yana kallo ta nufi ƙofar ta fice Hassan yayi dariya kamar ba itace ta ke kurma ihu ba ɗazu har tsiwar ta dawo.Fita yayi ya bita waje tsakar gidan daga bakin ƙofa murya ƙasa ƙasa “A ina to zaki kwana?“
“Ko ma ina amma banda ɗakinnan”.Ta amsa tana turɓuna fuska ya murmusa ya kasa ce mata komai domin wannan abun da take yafi komai kashe masa jiki.
“Jirani”.Ya faɗa yana shiga ɗakin ya fara dube duben ƙadangare banɗakin ya fara zuwa ya duba yana haska fitila ya juyo ya duba bayan ƙofa sai ga ƙadangare ya manne bayan ƙofar har ma yayi baƙi Hassan ya fita ya ɗakko tsimma ya dawo banɗakin ya kamoshi gam ya fito Jidda tuni ta nufi can ƙofar ɗakin Anty Ruƙayya sai da ta ga Hassan ya dawo ta komo bakin ɗakin “Na ciresa”.Ya furta.
“Da akwai wani?”
“Babu shikaɗai ne daman”.Ya amsata.
“Tohm ka fara shiga”Ta faɗa Hassan ya yi murmushi ya shiga sannan Jidda ta bi bayansa ,Anty Ruƙayya batasan mai yake faruwa ba ihu dai ta ji kuma har ranta bata kawo ihun da ya shafi abu makamancin haka bane wani tunani can ta tafi ta ƙarasawa yaranta addua dukkansu sunyi bacci ta dawo kusa da Shafiha ta kwanta tana sakin murmushi ita kaɗai ihun Jidda ta ke tunawa tana cewa ‘Bayana bayana’ da wannan Anty Ruƙayya ta kwanta.
Jidda sai zazzare ido take haka ta haura kan gadon tana kallon Hassan yayi shinfiɗa ya gama addua ya kwanta sam hankalinta ya ƙi kwanciya “Jidda kiyi addua kwanciyar kinji”Ta ji muryarsa Shiru ta masa tana rufe ido ƙadangaren take gani kawai a idonta ta miƙe zaune ta rarrafa daga kan gadon tana leƙa Hassan a ƙasa ya juya baya tana shawara daga ƙarshe dai ta buɗe baki tace “Ka dawo saman tsoro nake ji”.Jidda bata iya bacci ba sai da Hassan ya dawo kan gadon ta shiga daga ciki ta kwanta ya na kallonta ta runtse ido ta makalkale jikinta sai ta bashi tausayi matuƙa ya kasa ɗauke idanunsa daga kanta “Na miki addua?”Ya tambaya ta giɗa kai idanunta a rufe ,Hassan sai da ya mata adduoi ya tofa mata jiki bai kwanta ba yana zaune sai da ya tabbatar bacci ya ɗauketa sannan ya kwanta…..
On Arewapen
Share
Like
Comment❤️❤️