HASASHEN SOYAYYA COMPLETE

Hs 59

by @legendspen

(59)

Ba a jima ba, sai ga wata nurse ta fito tana murmushi, ɗauke da wata kyakkyawar jaririya da aka naɗe a cikin farin kyalle. "Masha Allah, an sami mace kyakkyawa. Jaririya tana cikin ƙoshin lafiya."
Senate ya miƙe ya karɓi 'yarsa. Tana kuka, amma ganinsa ya sanya ta yin shiru kamar ta san kowaye shi. Ya sunbaci goshinta, hawaye yana zuba a fuskarsa. "Masha Allah... kyakkyawa ce kamar mahaifiyarta."
Amma murnar tasa ba ta dore ba lokacin da ya ga nurse ɗin ta koma ciki da gudu ba tare da ta ce masa komai game da halin da Bhatool take ciki ba. Ya kalli Umma, sai ya ga ita ma fuskarta ta sauya.
"Nurse! Bhatool fa? Inna mahaifiyarta?" Senate ya kwala kira, amma ba wanda ya saurare sa.

Daga cikin ɗakin, sai aka fara jin sautin injina da gaggawar likitoci. Senate ya ji wani irin sanyi ya ziyarci ƙafafunsa, ya kalli 'yarsa dake hannunsa, ya ji wani irin tsoro ya ziyarci zuciyarsa, tsoron cewa wannan jaririyar ita ce kyautar da Bhatool ta bar masa kafin ta tafi.

Bayan kusan mintuna ashirin da haihuwa, likitan ya fito yana goge gumi, ya kalli Senate cikin wani yanayi na tausayawa. "Alhaji, tana son ganinka. Amma don Allah ka daure, karka nuna mata damuwarka."
Senate ya mika wa Umma jaririyar, ya shiga dakin jikinsa a sandarare. Ya iske Bhatool kwance, fuskarta ta yi fari sol, numfashinta yana fita da kyar, amma idanunta suna nemansa. Ya karasa kusa da ita, ya kama hannunta wanda ya riga ya fara yin sanyi.
"Bhatool... gashi nan kin tashi lafiya, kin kawo mana kyauta," ya fada yana kokarin hadiye kukan dake taso masa.
Bhatool ta yi wani raunannen murmushi, ta kalli Senate cikin ido. "Usman... lokaci na ya kusa... ina jin sa a jikina. Ina son ka sani cewa ina sonka sosai, na yafe maka komai..."

"A'a Bhatool, karki ce haka, zaki tashi, zaki warke mu raini 'yarmu tare," Senate ya fada yana kuka, hawayensa suna digawa a kan hannun Bhatool.
Bhatool ta girgiza kanta a hankali. "A'a Usman... ka saurare ni. Ina son ka kula mini da 'yata... Ka bawa Umma ko Abdul su rike mini ita, nasan za su so ta yadda nake so. Ka gaya wa Yaya Karima ina son ta, na gode da kula da ni da kuka yi... na gode da gatan da kuka nuna mini."
Ta danyi shiru tana neman numfashi, sannan ta ci gaba. "Ka gaya wa Abdul ina son shi sosai, ina masa fatan alheri a rayuwarsa da sabon aurenshi. Kowa ya yafe mini..."
"Bhatool kiyi hakuri don Allah, zaki warke, muna bukatar ki," Senate ya fada yana kukan dake cin rai, ya kankame hannunta tamkar hakan zai hana ranta fita.
Bhatool ta kara matse hannunsa da sauran karfin dake jikinta. "Usman... karka damu. Na tafi ina mai farin cikin cewa na bar maka gurbin da zai dinga tunatar da kai ni. Ka kira sunan Allah a kunne na..."
A lokacin ne Umma da Abdul suka shigo dakin. Abdul ya iske kanwarsa a wannan halin, ya durkushe a gefen gadon yana kuka. Bhatool ta kalli Abdul, ta yi masa wani kallo na karshe dake nuna tsantsar soyayya da fatan alheri.
Dakin ya cika da kuka, yayin da Senate ya fara karanto mata kalmar Shahada a kunne, muryarsa tana daukewa saboda zafin rai. Bhatool ta bi shi, tana motsa bakinta a hankali, idanunta suka fara lumshewa yayin da wani irin sanyi ya ziyarci dakin.

"La'ilaha illallahu..."
Wannan ita ce kalmar ƙarshe da ta fita daga bakin Bhatool, tare da wani sanyayyan numfashi wanda ya fita bai sake dawowa ba. Hannunta dake maƙale da na Senate ya saki, idanunta suka lumshe tamkar mai bacci, fuskarta kuma ta bayyana wani irin haske.

"Bhatool?" Senate ya kira sunanta, muryarsa tana rawa. "Bhatool don Allah ki buɗe idonki. Gashi 'yarki tana kuka tana nemanki!"
Shiru! Babu amsa.
Abdul wanda yake duƙe a gefen gadon, ya ɗaga hannun ƙanwarsa ya ji shi tamkar auduga, babu sauran dumi. Wani irin ihu mai ban tausayi Abdul ya fasa, ya ɗora hannunsa a ka. "Bhatool! Don Allah karki tafi ki bar mu! Wayyo ƙanwata!"
Daidai nan, Yaya Karima ta faɗo ɗakin a guje, tana iske wannan yanayin, ta saki wani uban kuka ta zube a ƙasa tana kiran sunan Allah. "Bhatool! Yanzu duk gatan da muka yi miki ashe na bankwana ne? Ashe dukan wahalar da kika sha a baya kika jure, ashe domin ki tafi ne yanzu?"

Asibitin ya ruɗe da kuke kuke. Masu jinya ma kansu sun kasa daurewa, domin kowa ya shaida yadda Bhatool ta yi gwagwarmaya da rayuwa. Senate kuwa, ya kasa kuka, ya kasa magana. Ya kafe gawar Bhatool da ido, yana tunawa da hirar da suka yi a falon Umma mako guda da ya wuce. Ya tuno alƙawarin da ya yi mata na cewa za su raini 'yarsu tare.
"Kin tafi kin bar ni da wannan nauyin, Bhatool," ya faɗa a cikin ransa, yayin da wani irin daci ya ziyarci maƙogwaronsa.
Umma kuwa, tana can a kusurwa, ta ƙanƙame jaririyar a ƙirjinta, hawayenta yana zuba a kan fuskar jaririyar. Jaririyar kuma ta fara kuka mai ƙarfi, tamkar tana kiran mahaifiyarta dake kwance shame-shame, wadda ba za ta sake amsa kiran kowa ba har abada.

Wannan rana ta kasance baƙar rana ga masoyan Senate da Bhatool. Mutuwar Bhatool ta zama wani babban darasi dake nuna cewa rayuwa ba ta da tabbas, kuma nadama takan zo ne a lokacin da gyara ba shi da amfani.

An fito da gawar Bhatool daga ɗakin haihuwa, aka naɗe ta a farin kyalle. Senate ya bi bayanta da kallo, yana jin tamkar ƙashin bayan rayuwarsa ne aka fitar da shi. Ya kalli Abdul dake kuka tamkar ransa zai fita, ya fahimci cewa wannan raunin ba na mutum ɗaya ba ne; rauni ne da zai dade yana raɗadi a zukatan kowa.

Labarin mutuwar Bhatool ya karaɗe garin Yobe tamkar wutar daji, musamman yadda kowa ya san wahalhalun da ta sha da kuma yadda yanzu take dab da samun natsuwa. Gidan Umma ya cika ya batse, mutane sun kasa gaskata abin da suke ji.

A gefe guda na falon, kawayen Bhatool na kusa da na nesa sun hallara, kowacce ka kalla fuskarta ta kumbura saboda kuka. Jannah dake kwance a kasa, kuka take yi tana kiran sunan Bhatool, tana tunawa da yadda suka yi biki kwanan nan. 

Amrah kuwa, wadda take jin nauyin abin da ta yi wa Bhatool a baya, kukan nadama da tausayi ne ya cika ta tana jin kamar ba ta sami isasshen lokacin da za ta nuna wa Bhatool soyayya ba kafin wannan ranar.

Haka Suhaima ma, kuka kawai take yi. Gaggo Larai, Furee, da Habi, duk sun shiga wani irin tashin hankali. Kowa yana tuna wata hira ko wata hidima da Bhatool ta yi musu. "Bhatool ba mace bace mai rikon mutum, mace ce mai hakuri," in ji Habi cikin shesshekar kuka. Shuru ya mamaye falon duk lokacin da aka kalli jaririyar dake hannun Umma, wadda kukan ta ya ki tsayawa tamkar tana kiran mahaifiyarta.
Karfe biyu na rana aka shirya janizar Bhatool. Kowa ya hallara a babban masallacin dake layinsu Bhatool. Abdul yana tsaye, kansa a kasa, hawaye yana zuba a fuskarsa ba kakkautawa. Ahmad ma yana can a gefe, zuciyarsa tana tafasa da tausayin wannan baiwar Allah da kuma kaddarar dake tattare da ita.
Senate kuwa, tun asuba rabon sa da magana. Yana tsaye kusa da gawar Bhatool lokacin da aka sauke ta don yin salla. Ya dube ta a cikin makara, an nada ta a cikin farin kyalle, fuskar nan ta ta mai kyau yanzu babu sauran numfashi. A nan ne Senate ya ji cewa lallai rayuwarsa ta sauya har abada.
"Allahu Akbar!" Muryar liman ta karaɗe ko ina. 
Bayan an gama salla, aka dauki gawar zuwa makabarta.  Nan fa kuka ya dawo sabo
Jannah da Amrah suna can daga ƙofar gidansu Bhatool, kukan su yana tashi yana ratsa zukatan mutane. Babu wanda bai yi kuka ba a wannan ranar, har wadanda basu san Bhatool ba sun ji radadin mutuwar tata. Haka aka wuce da ita maƙabarta Kowane taku da ake yi, Senate yana jin tamkar ana kara nisa da shi ne daga duniyar farin ciki. Aka tafi da ita cikin kuka da addu'o'i, aka sanya ta a cikin kabarinta.

Lokacin da aka fara zuba kasa, Senate ya kalli Abdul suka yi ido hudu, kowannensu ya juya kansa gefe yana kuka.
An gama jana'iza, mutane suka fara rarrabuwa, amma Senate ya ki tafiya. Ya tsaya a kan kabarin, yana kallon sabuwar kasar da aka zuba. "Bhatool, na yafe miki duniya da lahira. Kuma na karbi amanar 'yarki da kika bar mini. Insha Allah zan rayu ina tuna kowace hira tamu," ya fada cikin murya can kasa.

Wannan rana ta kasance babban bankwana. Kowa ya koma gida da tunani daya "Ina ma ace Senate ya sani tun farko, ina ma ace Anty ba ta shiga tsakaninsu ba." Amma kaddara ta riga fata.

Legendspen
***