CHAPTER 2
by @hafnancy
HARAMTACCIYAR GADA 2026
BOOK 1.
Page 2.
Samha 'ya ce ɗaya tilo ga Executive Chef Jalaluddeen Alkaleri (Yallabai) da Hajiya Nafeesa Mu'azzam. Shekarun haihuwar Samha ashirin da takwas a duniya. Matashiya ce amma mahaukatan kuɗaɗen data tara ne yasa ake Hajiya Sama, Hajiya kasa kamar za a shimfiɗe a gabanta.
Mahaifinta, da mutane suke kira da Yallabai mutumin Alkaleri ne amma kasuwanci ne ya kawo shi garin kaduna domin duk fadin Najeriya babu garin da yakeso kamar Kaduna aganinsa in aka cire Kano, shi ne gari na biyu da yafi daɗin kasuwanci da wayewa.
Hakan yasa bayan ya kare karatunsa a Bauchi State University, da kammala bautar kasarsa kawai ya tarkato zuwa Kaduna, sannan ya yi amfani da ɗan jallinsa dayake ta tarawa tunda dadewa ya buɗe karamin restaurant tare da taimakon abokinsa Nasir da suka yi karatu tare.
Nasir ne ya tsaya kan tsayin daka na tabbatar da cewa ya taimaki amininsa. Har gidan zama sai daya samo masa saboda iyayensa na da hali dayake mazauna garin Kaduna ne. Shi Nasir iyayensa sun ɗora shi kan sana'a ta siyar da kayan textiles da zai dogara da kansa. Hakan ya bashi kwarin gwiwan samo ma amininsa inda zai kafa restaurant tunda burinsa a rayuwa ya buɗe gidan abinci. Sannan Nasir yasa iyayensa suka tallafa masa da kuɗi ya kara jalli da shi.
Kamar da wasa Jalal ya fara kasuwancinsa kuma cikin kankanin lokaci Allah yasa wa sana'ar tasa albarka dan ba karamin ciniki yake ba. Kuku ne wanda ya amsa sunansa kuku, ya iya girki mai ɗanɗano da ake matukar jin daɗinsa. Dana zamani dana gargajiya babu wanda bai iya ba kasancewar ya taba shiga makarantar koyon girke-girke har na tsawon shekara ɗaya a can garin Bauchi lokacin yana karatu.
Sunan gidan abincinsa 'Alkaleri's Kitchen' da a kayi rijista a karkashin hukumar kula da harkokin kasuwanci. Sannan ya taka matsayin Executive Chef ne a dalilin gasanni da yake yawan shiga da kasashe daban-daban ke shiryawa kuma yake nasara.
Sannu a hankali ya soma buɗe branch har awasu garuruwa kamar Abuja da garin haihuwarsa Bauchi. Ya zuzzuba kwararrun kuku. Daga nan bai sake yin wani girki da kansa ba don ya zama oga baya zama. Ko a halin yanzu ma kasashe kusan biyu yake neman kafa branch kamar Dubai da kasar birtaniya shiyasa bai cika zama ba. Kasuwancinsa kawai yasa agaba bai tab'a tunanin aikin gwamnati ba don baya sha'awarsa.
Yana da shekaru ashirin da bakwai a duniya yayi kaurin suna na ban mamaki, da nan gida Najeriya har da kasashen waje. To, a lokacin da Nafeesa ta samu labarin irin arzik'in daya tara da irin ɗaukakar daya samu, shine ta dawo tana rokonsa don ya sota tun suna makaranta amma dake awancan lokacin bashi da arziki sai bata kalleshi ba.
Bayerabiya ce 'yar Kwara state amma a Katsina ta tashi gaban iyayenta dayake mazauna garin ne. Sai dai idan ba ance maka Bayerabu bane sai ka rantse hausawa ne saboda hausarsu na fita sosai. Karatu ya kai ta garin Bauchi, bayan ta kare ta koma gaban iyayenta amma daga jin Jalal ya samu ɗaukaka ta fara bibiyarsa.
Jalal bai wani ja mata aji ba don shi mutum ne da babu ruwansa, shiyasa ake yawan cutarsa don bai cika reacting akan abu ba sai ka kai shi makura. Ya san ɗaukakan takeso bashi ba amma bai damu ba ya aureta duk da ga yawan 'yan matan dake kawo masa hari, ganinsa matashin mai kudi ga kuma kyau da aji, hadda sugar mommies amma hakanan ya zabeta akansu ba don yana sonta har lokacin ba, sai don shi ma yana so yayi aure ya tara Zuri'a.
Bayan aurensu, a farko sun samu ɗan jinkirin haihuwa. Sai da aka kwashi shekaru kamar biyu zuwa uku sannan ta haifi 'yarta Mace. Tunda ta haifi Samha sai tayi tsarin iyali wai bata son ta cigaba da haife-haife kar ta tsofe don haihuwa ma baya cikin agenda ɗinta. Yana son haihuwa amma haka nan ya hakura ya kyaleta don shi mutum ne da baya son yana shiga hakk'in wani.
Ya dauki son duniya ya dorawa Samha kasancewarta 'ya daya tilo daya mallaka arayuwarsa. Haka Samha ta taso cikin kulawar iyayenta amma daddyn nata akodayaushe kokarin dorata akan hanya madaidaiya yake, ita momminta ne ke sangartata.
A Poland tayi karatunta kuma acan ne ta hadu da Haseeb Aliyu Gamawa wanda ya yi bala'in tafiya da imaninta. Shi ma mahaifinsa ba laifi yana da dan rufin asirinsa, kuma kafin ya bar duniya sai daya tabbatar da Haseeb ya samu wajen zama a asibitin ido na nan garin Kadunar, dayake ya karanci abin da ya shafi ido ne.
Dama Ilimi ne yazo karawa shine suka hadu da ita Samhar kuma sai ya kasance gari daya suke, nan da nan soyayya ta kullu tsakaninsu.
Da kammala karatunta babu b'ata lokaci aka yi musu aure. tunda ta dawo ita ma kamar mahafinta ta nuna bata ra'ayin aikin gwamnati shine mahaifinta Yallabai ya bata makuden kudade akan ta fara sana'a, baya so ta dogara da mijinta.
Ita ma Haj. Nafeesa ya sha bata jalli kan ta fara sana'a amma sai ta cinye kudin. Wai sam bata kaunar wahalar dakai, ta fi son kawai ya dauko kudi ya bata ta biya bukatun kanta. Ta zama cima-zaune.
A duk sanda ta fadi hakan girgiza kai kawai yake yi, wato aganinta shine mai aikin banza, don tana ganin cewa shi mai arzik'i ne shiyasa bazata yi wahalar neman na kanta ba. Allah ya gani wallahi bai auri irin macen da yake so wacce rayuwarsu tazo daya ba, aurensa da Nafeesa rubutaccen al'amari ne kawai. Baya da ra'ayin ajiye mace fiye da daya shiyasa bai yi tunanin kara aure ba.
Lokacin da Samha ta nuna bata ra'ayin aikin gwamnati. Ya nuna mata jin daɗinsa kuma ya bata goyon baya sai dai, tana gaya masa gidan mata zata kafa ya nuna rashin amincewarsa saboda tsarinta bai gamsar da shi ba.
Tsari ne na bada mafaka a kyauta, sai kuma wadata su da kayan abinci daidai ƙarfinta duk wata. Amma haraji shi ne kuɗin da zata fanshi dukiyar da take bararwa a kansu.
To, wannan tsarin ne sam bai gamsar da Yallabai ba, don yana ganin harajin nan zai sa 'ya'yan mutane shiga wani hali. Daga shi har Haseeb basu yi na'am da wannan kasuwancin ba, amma Haj. Nafeesa da aminiyarta Haj. Haire su keso ta kafa wannan gidan matan ba don suna son ta samu ci gaba ba, sai don cimma burin da ke ransu wanda ko Samha ma basu sanar mata ba.
Ganin Haseeb da Yallabai na neman kawo musu gaddama yasa Haj. Nafeesa da Haire shiga malamai suka sa aka rufe bakin duk wanda zai iya kawo matsala bayan kafuwar wannan gidan.
Yallabai bai sake daga murya akan kafuwar gidan mata ba. Ya zura musu idanu amma a ransa ya ce
''Duk abin da ya biyo baya kuyi kuka da kanku"
A halin yanzu GIDAN MATA yana da shekaru biyar zuwa shidda da kafuwarsa.
JIDDATULKHAIR KABIR ita ce 'ya mace ta Farko data fara rayuwa acikin wannan gidan hakan yasa Samha ta bata dukkanin yardanta. Ta sakar mata ragamar komai na kula da gidan wanda tasa wa suna GIDAN MATA saboda fita zargin jama'a.
Kudad'e ne kawai Samha ke gani, cikin ƙanƙanin lokaci ta zama Hajiya a idanun matan gidan. Akwai matan da sun bata shekaru amma girman da take da shi a idonsu yasa suke binta sau da ƙafa.
Bata da Lokaci shiyasa Jidda ke kula da gidan, hakan yasa ba kasafai suke ganinta ba sai lokaci zuwa lokaci.
Wani al'amarin da zai matukar baku mamak'i shine tun ba'a je ko'ina ba Allah ya fara saukarwa Samha da mahaifiyarta aya tun duniya. Wato mahaifinta Chef Jalal yana mu'amala ta sirri da Jidda ba tare da saninsu ba.
MAFARIN HAƊUWARSA DA JIDDA.
Akwai ranar da Jiddan taje gidan abincinsa na Abuja road tare da wani saurayinta don ita rayuwarta mai aji take yi. Idan ta tsaya da mutum daya ta riƙe shi kenan har sai idan shine yaci amanarta ya gujeta, to shine zata laluɓi wani.
Haidar shine maneminta na biyu kuma ba laifi yana kashe mata kudi, duk wani wanda zai zauna na 'yan mintina da Jidda dole ne ya ji ta kwanta masa arai saboda kyawun halinta. Matsalarta ɗaya tana bada wuta a gidan mata wannan yasa ake ganin kamar bata da sauki.
A ranar sai ya kasance Yallabai yazo ganin yadda kasuwancinsa ke tafiya a wannan branch d'in domin reshe biyu yake dashi a garin.
Tunda idanunsa suka kyalla ido kan Jidda yaji gabaki daya ya rasa natsuwarsa. Gashi babu halin zuwa kusa da ita tunda tare da wani take kuma bashi da tabbacin ko ma'aurata ne. Sai dai yanayinsu ya nuna kamar budurwa da saurayi ne.
Sai daya samu kamar 80% na assurance na cewa budurwa da saurayi ne sannan ya shiga cikin kwastamomi ya zauna domin jin dadin kallonta dakyau. Ma'aikatansa sai mamak'i suke tayi don da wuya kaga ya zauna cikin kwastamomi. Ba wai don yana da ganin kai bane, kawai ganin dama ne bai yi ba.
Har yau kuma muddin zai yi amfani da hannayensa ya yi girki sai an ji ɗanɗanonsa daban don girkinsa na musamman ne babu abunda Matarsa zata nuna masa sai dai shi ya nuna mata. Balle ma ba iya girkin ta iya ba, wasu lokutan ma tana kallo zai shiga kitchen ya had'a lafiyayyen girki kuma babu kunya ta zauna ta tande kwano tana zuba santi.
Wasa-wasa aka koma ganin Yallabai a wannan reshen gidan abincin. Ya jera kusan sati guda yana zuwa musu akai-akai wanda abu ne mawuyaci ka gansa kullum, sai gashi Jidda tasa ya mayar da wurin kamar gidansa don kawai ya kara haɗ uwa da ita tunda babban yaronsa Aliyu ya bashi tabbacin tana yawon zuwa siyan abinci. Wasu lokutan a nan take siya ta zauna ta ci, a yayin da wani sa'in tana takeaway ne.
Ya ɗau alk'awarin duk randa ya ganta koda tare da wani ne ba zai yi kasa agwiwa ba zai sallame wannan da makud'en kudi sannan ya maye mata gurbinsa, haka nan kawai ya ji yana son ta zamo tasa shi kadai.
Cikin ikon Allah kuwa akwana na goma sha daya sai gashi ta sake dawowa tare da wannan saurayin nata Haidar don duk duniya babu gidan abincin da takeso kuma take jindadin ɗanɗanonsa kamar Alkaleri's Kitchen. Babban yaron Yallabai na ganinta bai tsaya ɓata lokaci ba ya kira shi awaya tunda assignment ne da aka bashi cewa duk ranar da Allah ya kaddara ta zo gidan abincin ye neme shi a waya.
Bai ɓata lokaci ba ya garzayo gidan abincin. Duk da sosai ya cika da farin cikin ganinta amma ya yi takaicin sake ganin nata tare da shi wannan saurayin.
Bai yi kasa a gwiwa ba tunda ya dau alk'awarin ganin ya maye gurbin wanda take tare da shi. Haka ya nufi inda suke, daddad'ar kamshin turarensa ne ya soma bugar hancinsu kan sallamar ma ta biyo baya. Zuba masa idanu sukayi bayan sun amsa sallamarsa, sosai ya musu k'warjini kuma tabbas sun shaidashi don shi d'in sananne ne.
Bai jira sun masa tayin zama ba yaja kujera gami da dora kafa daya kan daya, cover shoes ɗinsa sun sha tsadadden polish sai walkiya suke. Gaba daya ya gama daukan hankalin waje sai kallon inda suke ake.
"Ku yi hakuri na nemi wuri na zauna tun baku bani izinin hakan ba " yayi k'ok'arin kau da shirun daya dan ratsa atsakaninsu...
"Baka da matsala Yallabai ai girmanka ne ! amma ina fatar ba wani laifi mukayi ba ko ? don zamanka acikinmu ya nuna sam bata lafiya bace "
murmushi yayi ya fesar da iska idanunsa akan Jidda wacce tunda ya zauna awurin ta dibirbirce.
Ya ce"Ga wacce ta yi min laifin nan ?" Ya furta yana nunata da 'yar yatsa.
Waro idanu tayi cike da tsoro take fadin,
"Ni kuma ? me na maka ?"
"kin sace mun Zuciya "
Cike da mamaki suke kallonsa, har Haidar ya bude baki zai yi magana, Yallabai yayi saurin daga masa hannu"Ba cece kuce ya kawo ni nan ba don ba girmana bane, ko ba'a fada mun ba nasan budurwarka ce. Zan mallaka maka makud'en kudad'e in har zaka bar mun ita ta zamo tawa ni kadai "
Washe haqora yayi yana sosa kai yace"Ai ba damuwa ni dama ba aurenta zanyi ba kawai abokiyar hutawa ta ce, don haka ban kudin kawai inyi tafiyata "
Girgiza kai Yallabai yayi yana jinjina abun aransa, atake kuma yayi masa transfer d'in 10m.
Haidar kamar zeyi hauka don be tab'a ganin irin wannan kudi acikin acct d'insa ba. infact dak'yar yake iya had'a miliyan uku, ita kanta Jidda ba wani kudin kirki take samu awajensa ba kawai tana dai tare dashi ne don ita ba kamar sauran 'yan barikin bane da suke huld'a da maza da yawa ba.
Sai gashi ayau Haidar ya nuna mata halinsu na maza, ta zab'e shi akan kowa hatta da waƴanda suka fishi abin hannu, ta zab'i yin muamala da shi kaɗai ta rike masa amana amma gashi ayau shi ya yaudareta, kodayake haka dama barikin yake.
Runtse idanu tayi wasu zafafun hawaye suka gangaro mata tana jin sanda Haidar ya sumbaci hannunta ya ce "Jidda bazan taɓa manta dake ba! ke ɗin me goshin arzik'i ce. Gashi ta sanadinki na samu mahaukatan kudin da ban tab'a gani ba, sweetheart kiyi hakuri ba yaudararki nake shirin yi ba illa i want to move on! kema nasan u will love to move on, dan haka ya zama dole ki canzani ayau, i will always love you Jidda dan ke d'in ta dabance da sauran matan....Enjoy your moment with The founder/Owner of Alkaleri's Kitchen har zuwa lokacin da shi ma Allah ya dibar masa arayuwarki. Lokaci na expire ki sani shima tafiyarsa zaiyi ya barki, Saiki sake laluɓan wani kuma, and the process continues har sai an gama yayinki, haka ita dama 'yar kwalta take sam bata da daraja....."
"Ina tsammanin ko uwarka ce ayau ta fito tana yawo bai dace ka gaya mata hakan ba! ka sani kowacce 'ya mace tana da darajarta don ita d'in uwa ce. Mace ce duk mulkin mutum da dukiyarsa sai da ita yake kara kima a idon mutane. Ka sani idan babu 'ya mace arayuwarka tofa rayuwar taka bazata tab'a tafiya daidai dana sauran mutane ba. Ka dinga darajasu ko ayaya suke! karka kuskura ka shiga tsakanin Allah da bawansa, kowa yaji da nashi zunubin. Kuma ai ire-iren naku ne ke ɓata matan kwarai, in kasan da gaske kana sonta kamata ya yi ka aureta ba wai ka lalata mata rayuwa ba."
Kaca-kaca ya masa Jikinsa yayi sanyi sosai ita kuma Jidda taji wani irin sanyi da natsuwa ya shigeta a karon farko tunda duniya ta ƙwaye mata baya. Nan take Yallabai ya birgeta, gashi da jikin hutu, shekarunsa 59 amma nan sai ka rantse ma Haidar me 35 ya girme shi.
Bayan wucewar Haidar Ya dubeta ransa a dan bace yace"Dama rayuwar da kike yi kenan? ban so ace an samu irin haka attattare da ke ba! sai dai bazan dora ayar tambaya akanki ba don komai na faruwa ne bisa dalili da kuma zanen kaddara, gayamun wacece ke ?"
"Kar ka so sanin ko wacece ni don har abada bazaka tab'a samun amsa ba."
Ta furta tana kokarin danne kukan dake neman cin k'arfinta.
"Ina tambaya ne don aurenki nake son yi, ba rayuwar kazanta ce ta kawo ni gareki ba "
Ya fad'i hakan babu alamun wasa.
Mamak'i ne ya cikata don bata tab'a haduwa da mutumin da tashin farko ya nuna aurenta yakeso ba. Ita kanta zata so auren amma muddin ta amince da aure, za'a nemi sanin asalinta wanda already ta riga ta rufe babinsa a rayuwarta. Sanin asalinta shine dalilin daya sa batun aure ya fice a ranta.
Haduwa da yar'uwarta Saffy ke k'okarin tunatar da ita cewa lallai fa tana da asali. Abu na biyu kuma wanda ke mata tayin auren shi d'in baya jerin waƴanda zata iya aura. Wannan mahaifin uwar ɗakin ta ne.
"Zan ara miki lokaci kiyi nazari! Aure ko bariki? Wanda kika zab'a a ciki saiki tuntubeni ga complimentary card d'ina."
Ya dire mata sannan yayi gaba cike da aji sai binsa da ido ake.
Muje next page domin jin yadda ta kaya tsakanin Jidda da Yallabai
Zaku rika samun daily update amma ban da Saturday's and Sunday’s.
NAGODE ALL🙏
HAFNANCY📚✍️
***.