RU'UYAA (The dreams we never lived)
1. ...Farko...🖋️
by @autum17
Turawa na cewa, “Be careful what you wish for.” — Ka yi hankali da abin da kake fatan samu.
Na ji wannan karin magana ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba,amma duk da haka, ban taɓa tsaya wa na yi tunani a kai ba. Ban taɓa tsammanin akwai ranar da zan waiwaya baya in ce:
“Inama ace na tsaya na yi tunani a kan wannan kalmar kafin na furta abin da na furta ...”
Tun ina ƙarama, ban taɓa samun kyakkyawan tunani game da kaina ba. Abubuwa da yawa da suka faru da ni ne suka koya min ganin duniya da idon tsoro. Kullum ina cikin ƙoƙonto da shakku.
Ban isa ba...ban kai ba....babu wanda ya damu da ni...ban cancanci a so ni ba...ban da kyau...ban iya ba
Sai kuma tambayar da ta fi kowacce sanyaya min jiki:
“Har abada, abubuwan da kike ta addu’a a kansu, za ki taɓa samu? Akwai wanda zai so ki? Idan fa kika ƙare rayuwarki ke kaɗai?”
A daidai lokacin da nake cikin ruɗani da rashin yarda da kaina, lokacin da zuciyata ta karye ta tarwatse zuwa ƙananan pieces, sai ya zo.
Kamar wata da ke haska sararin sama mai duhu, ya fara tattaro ragowar zuciyata yana gyara ta da soyayya mai ratsa zuciya da ɓargo.
Na ɗauka shine nawa...na manta da wancan abin da na taɓa roƙa..
Na manta da abin da na faɗa cikin rashin sani, cikin rashin tunani, ba tare da na fahimci nauyin addu'ar da nake yi ba.
Duk cikin rashin sani ne..da rashin wayo.
Sunana ABEEDAH ABDUL WAHHAB
Haifaffar garin Zamfara , amma yanzu muna zaune a Kano, a Kofar Mashi. Mu uku ne kawai a gidanmu—ni, Mama da ƙanwata Asma'u.
Babanmu ya rasu tun muna ƙanana. Hakan yasa ba mu san shi sosai ba. Danginsa ko sau ɗaya basu taɓa leƙowa ba,ba taimako, ba tambayar halin da muke ciki...
Mama ita kaɗai ta raine mu har muka girma ni shekaruna goma sha bakwai, Asma'u kuma goma sha shida.
Amma idan ka kalle mu, abu na farko da za ka ɗauka shi ne Asma'u ce babba.
Ba don shekarunta sun fi nawa ba, sai don Allah Ya yi mata ƙira da ke sa ta zama kamar babbar mace. Kyakkyawa ce kamar matar novel—ba wai kyakkyawa kawai ba, tana da kaifin basira, iya magana da kuma natsuwa.
Ni kuwa?
A ganina, babu wani abu da mutum zai kalla ya yaba,bani da cikar halitta kamar Asma'u...Fuska? Ba kyau. Ƙwaƙwalwa? Ba wani abu. Shape ɗina kamar 1
Hakan ya sa na zama insecure,har tafiya nake yi da hannuna a gaban hijabi..cikin shekaru goma sha bakwai na rayuwata, babu wanda ya taɓa tsayar da ni da sunan soyayya.
Amma Asma'u?
Tana da farin jini sosai duk da ba kulasu take ba,ba wai ina kishin Asma'u ba ne Allah Ya kiyaye.
Na yarda ta fi ni kyau. Ta fi ni zubi da tsarin halitta. Amma...
Me ya sa mutane ba sa ganina?ai ni ma mace ce ko?ni ma na cancanci a so ni ko?
Dan kawai jikina bai girma ba ai ba kyaun halitta ake dubawa ba,kyaun hali dana zuciya shine jigo...
Na tuna lokacin da nake JSS2.
Akwai wani yaro da na taɓa rubuta wa letter saboda ina son shi,ba ƙaramin ƙwarin guiwa na tattaro ba wurin juye abinda zuciya ta ke ciki saman paper nan,amma da ya karanta, maimakon ya ba ni amsa cikin mutunci, sai ya zaɓi ya wulakanta ni a gaban kowa.
Har yau, maganganunsa suna nan a raina.
«“Ke yanzu, dan Allah baki ji wani abu ba a ranki? Kalle ki, dan Allah! Yanzu ke a tunanin ki ke mace ce? ƙirji kamar allo, baya kamar plate, fuska kamar ƙwarangal, baki da kyau, baki da shape, gashi kusan kullum ke kike ɗauko na ƙarshe a ajinku, amma shine za ki kalle ni ki ce kina sona? Gaskiya wannan shine mafi munin cin mutunci da wani ya taɓa yi min!”»
Maganganunsa sun rusa ni fiye da zaton mai karatu,mutanen da ke zagaye da mu kuwa, dariya suke irinta ƙeta ɗin nan
Ba su taɓa bari ko rana ɗaya ta wuce ba tare da sun tunatar da ni abin da ya faru ba...na yi kuka kamar raina zai fita...Mama da Asma'u sun yi ta lallashi da nasiha, amma komai ya zama kamar ana zuba ruwa a dutse.
Ƙirjina har ciwo yake yi saboda yadda abin ya shiga zuciyata..na daina fita sosai.
Domin daga lokacin da ɗaliban makarantarmu suka hango ni, shikenan. Tsokana za ta fara—ko ina, ko a gaban wa,ni kuma ban iya kare kaina,saboda ina ganina ƙasa dasu...
Kusan kullum idan na fita, nakan dawo da hawaye a idona..daga nan na fara addu'a..na roƙi Allah Ya yi ni kamar sauran mata
Ya ba ni abin da yake ba mata...na yi kuka...na yi sadaka...na yi magiya...amma babu abin da ya canja...saboda wasu lokuta zaka yi komai da komai da kake tunanin zai sa ka samu cikar burin ka amma sai kaga ba haka ba..
Zuciyata ta ƙara ƙuntata,abu kaɗan sai in fashe da kuka...idan na ga wasu mata ƙirji a cike, sai in kalle su ina tunanin:
“Inama ace nima nawa haka suke...”
Daga baya na fara saka bra,hakan ya ɗan ba ni ƙwarin gwiwa..amma da zarar na je makaranta, sai tsokanar ta dawo..suke kirana flat board
Sun riga sun san cewa ba ciko na gaske ba ne...sai na daina sawa,baƙin cikina har zuba yake, musamman idan na kalli Asma'u.
Alhamdulillah.
Yarinyar kamar matar novel.
Gashinta har tsakiyar baya,nakinta ƙarami. Hancinta kamar pencil. Idanunta manya masu kyau. Shape ɗinta mai ɗaukar hankali. Natsuwa. Iya magana.
Kamar dai duk wani abu da ake bai wa matan novel, Asma'u tana da shi—over and over.
amma tsawonmu kusan ɗaya.
Ni ma doguwa ce, amma ba ni da ƙiba sosai. Wasu lokuta nakan ji kamar rashin ƙibata ma yana daga cikin dalilin da ya sa nake haka...gashina kuwa?taurin tsiya ne dashi,da ƙyar yake saukowa idan na yi kitso...wurin taje shi sai na kusa sakin fitsari.
Fuskata ɗauke da wani special abu da ba kowa ke da shi ba, PIMPLES...
Manya manyan pimples ne suka dabaibaye min fuska..duk abin da na yi na magance su da magungunan gida, sai dai su ƙara yawa.
Na yi amfani da magungunan ƙyamis ma, amma maimakon su taimake ni, sai suka ƙara lalata min fuska ta hanyar barin tabo
Wasu lokuta har kuka nake yi saboda waɗannan abubuwan..amma ban daina neman hanyar da ƙirjina zai girma ba...ko pimples ɗina su ragu...ko gashina ya yi tsawo...ko yanda zan zama kamar matar novel Mai shape da kyau ba
Duk yanda na yi ƙoƙarin kada in haɗa kaina da Asma'u ko wata mace da ta fi ni kyau, na kasa...duk da na san hakan baƙin ciki kawai yake ƙara min.
Na kan ɗauki kaina a matsayin mara godiyar Allah,ya kamata in gode masa saboda yadda Ya halicce ni,amma na kasa.
Musamman idan na tuna yadda ake cin mutunci na saboda hakan..
Wata rana wasu 'yan matan ajinmu naji suna magana game da abubuwan da mace za ta iya yi idan tana son ƙirjinta, mazaunanta da hips ɗinta su ciko da sauri.
Nan take na riƙe komai,na fara yi,ina yi ina addu'a.
Ina kuma jin wani irin farin ciki idan na tuna cewa watakila ba da daɗewa ba ni ma zan zama “cikakkiyar mace”sai dai me?na yi na gama,babu abin da ya canja,sai ɗacin rai da na kwasa.
Na sake faɗawa cikin ƙunci da damuwa,har sallar dare na fara yi, ina roƙon Allah duk yadda zan iya,amma abin ya ci tura,daga ƙarshe na haƙura da gwada komai...duk da ba duka ba,
Ba wai na daina fatan samun abin da nake so ba ne,sai dai na fara tunanin cewa watakila babu abin da zai canja.
Idan na saka hijabi, ba na iya sauke hannuna ƙasa,ina gudun kada a ga ƙirjina...kun dai san maza da kallon tsiya...
Idan iska ta kaɗa hijabi, sai in gyara shi nan take don kada ya manne a jikina,don kada a ga bayana ya yi kamar plate..domin mutane haka suke faɗa,nima sai na yarda
Amma duk da haka, ban tsira daga maganganunsu ba,wasu har suna kirana suke da mayya.
Dalili?
Idanuwana,ruwan toka ne, masu duhu, kuma shape ɗinsu yana kama da na mage.
Mutane sun sha ganin mage da daddare mai irin wannan ido, don haka suka ƙara gasgata cewa ni mayya ce.
Har wasu suke gargadin 'ya'yansu su nisance ni,lokacin da na shiga SS3, da farko babu ruwana,bayan yadda aka ci min mutunci a SS1 da SS2, na rasa ƙarfin guiwa.
Ina tsoron shiga cikin mutane.
Ina tsoron kada wani ya faɗi wata magana da za ta sa in yi kuka.
Amma ban tsira ba.
Ganin abin nasu gaba yake, ba baya, yasa na fara koyon tsayawa wa kaina.
Ko da ba sosai ba.
Akwai wani malami bayarrabe da ke kirana Abeedatuwo,wai shi ala dole sai yace Abeedatu
Abin na ba ni haushi sosai,mutane suka lura,sai suka ɗauki sunan suka manna min shi,wasu ma har Abeedah ba sa cewa...
Tuwo kawai.
Ba a makaranta kaɗai ba,har gida abun ya biyo ni.
Gidanmu gidan kara ne.
Ɗaki ɗaya tak muke da shi, kuma dukkanmu tare muke kwana.
Gidan haya ne.
Mu talakawa ne—talakawa tuguf-tuguf.
Ni nake aiki a wani hotel don in sama mana abin da za mu riƙe kanmu da shi.
Mama ba ta son zuwa na wurin,amma babu yadda muka iya.
Mama tana matuƙar ba ni tausayi.
Ta tsufa, amma har yanzu burinta guda ne,ta ga mun zama wani abu a rayuwa.
Duk da tsufarta, har yanzu tana son ta yi aiki a duk inda za a biya ta, don ta inganta rayuwarmu.
Amma ba zan iya bari ta yi hakan ba.
Shi ya sa nake aiki.
Asma'u kuwa, tunda ta iya lalle da kitso, ita ma takan yi,a haka muke gudanar da rayuwarmu, cikin rufin asirin Allah.
Aikin hotel ba shi da sauƙi,musamman idan ka haɗu da wasu customers marasa mutunci
Shi yasa koyaushe nake tafiya da ƙaramin kwalbar turaren yaji dake ɓoye a jikina.
Duk wani ɗan iska da ya nemi yi min rashin mutunci, sai ya ga tijara,an sha kai ƙara ta wurin manager saboda hakan,ya sha yi min faɗa da barazanar kora
Amma bai taɓa aiwatar da hakan ba,saboda Allah Ya jefa wani irin ƙauna ta a zuciyarsa..ba ƙaunar soyayya ba.
A'a.
Irin ƙaunar da mutum zai yi wa ƙanwarsa.
Akwai akwai wasu jigon mutane da bana so...Masu kuɗi.
Ba wai na tsane su gaba ɗaya ba,amma kawai kasancewarsu kusa da ni yana iya sa haushi ya taso min...a ganina, suna ganin kansu kamar su suka fi kowa.
Kamar kowa ƙasa da su ne.
Kamar kowa bawansu ne.
Suna da girman kai, jijji da kai da ɗagawa.
Ni kuwa duk lokacin da Allah Ya kai ni aiki a ɗakin wani mai kuɗi, idan ransa yana dubu, sai na ji raina ya ɓaci.
Amma babban abin da ya sa bana son masu kuɗi shi ne tunanina...
A ganina, rayuwa tana zuwa musu da sauƙi.
Duk abin da suke so suna samu saboda suna da kuɗi,ba sai sun sha wahala kamar mu talakawa ba,kuma a tunanina, ba su da tausayi ko kaɗan.
Yau Lahadi ,gobe Monday,bayan sallar La'asar, Mama tana zaune a barandar ɗakinmu tana kallonmu.
Asma'u kuma tana wanke uniforms ɗinmu,ni ina tsaye da madubi a hannu na ina kallon pimples ɗina.
Haushi ya cika zuciyata kamar zan cije wani abu,amma me?na sauke ajiyar zuciya, sannan na ɗauki wata gora da na zuba ruwan shinkafa,na samu wuri na zauna..
“Asma'u, ɗan zo ki shafa min ruwan nan a kai!”na faɗa ina ci gaba da kallon madubi,ƙarshen kitsona na riƙe a hannu ina ja, ko zai sauko aƙalla ya ɗan wuce wuya.
Amma shegen abun, saboda taurin kai, ya ƙi ƙara tsawo,can na ji Mama tana dariya.
Ɗagowa na yi na kalleta, fuska ta kamar zan yi kuka.
“Shine kike min dariya ko?”
Na faɗa a shagwaɓe,rufe bakinta ta yi
“A'a, wai gani nayi kina ja'in-ja da abun...”
Sai ta sake tuntsirewa da dariya da dariya,Asma'u da ke shanyar hijabi saman igiya na tayata... na cika na yi fam
Mama ta kalle ni.
“Wai shi wannan ruwan shinkafar, aikin sa meye? Mene ne amfanin sa?”Cikin turo baki na ce,
“An ce fa yana da Aminu acid!”
Kafin in ƙarasa, Asma'u ta fashe da dariya.
“Ke, tuwo! Amino acid ake cewa, ba Aminu acid ba!”
tsaki na ja kamar bakina zai katse,ganin yadda suka maidani abun dariya ya ƙara ba ni haushi.
“Ko uban me ake kiran shi! Shi Aminu acid ɗin yana sa gashi ya yi ƙarfi sannan yana haɓaka girman gashi!”
Na faɗa a harzuƙe...Mama ta kalle ni da murmushi.
“Ke da gashin ki yake nan kamar ƙirigi, har da comb kika karya mana tsabar yadda yake da tauri, shine kike neman wani ƙarfin gashi kuma?”
Na daure fuska.
“Idan gashin yayi tsawo zan sa masa relaxer! yayi kamar irin na indiyawa..”
Wata irin muguwar dariya Asma'u ta saki har da riƙe ciki.
“Waih! Sallar da ta wuce kin manta abin da relaxer ta yi miki kenan? Ta kwashe gashin ki kika koma kamar talle mai shayi! Black Indian!”
Miƙewa na yi na bi ta da gudu...itama bata jira niba ta ɓoye bayan Mama su biyun suna dariya...
“Ayi haƙuri Anty Tuwo!”
Niko sai huci nake kamar wata zakanya.
“cewa fa tayi ina kama da talle mai shayi!”
Mama ta ɗaga gira.
“Toh, ko shine surukin namu?”
Wata irin ƙara na fasa, na faɗi ina birgima.
Su kuma suka cigaba da dariya.
Kafin daga ƙarshe Mama ta jawo ni jikinta.
Asma'u ma ta rungumeni ta baya.
Mama ta shafa bayana a hankali.
“Ina roƙon Allah Ya nuna min ranar da za ki karɓi kanki yadda Allah Ya yi ki, Abeedah. Ya nuna min mijin da za ku aura ku biyun nan. Kuma ya nuna min ranar da Tuwo za ta girma ta dena shagwaɓa...”
Ta faɗa cikin wani yanayi mai wuyar fassara.
Na ji Asma'u ta ce,
“Ameen.”
Ni kuwa na yi shiru.
Ban sani ba ko zan iya rayuwa wata rana ba tare da Mama da Asma'u ba.
Ina matuƙar son rayuwarmu yadda take.
Ba na son komai ya canja.
Bana son komai ya yi yawa.
Ko ya yi kaɗan.
Ina son komai ya kasance yadda yake.
A ganina, yawan abu yana sa mutum ya ɗauki ni'ima a matsayin abin da ba komai ba, har ya kasa ganin albarkar da Allah Ya ba shi.
Amma idan abu bai yi yawa ba, sai mutum ya koyi tattali.
Ya koyi godiya.
Ya koyi ganin abin da yake da shi a matsayin ni'imar Allah.
“Tuwo, ba ki ce Ameen ba!”
Asma'u ta katse min tunani....
“Na ce a zuciyata munafuka.”
Na amsa ina jan gashinta.
Ta yi dariya.
“Kada ki ɓaɓɓake min gashi, ni dai!”
Mama ta girgiza kai.
“Ku ɗaga ni kada ku ƙarasa ni!”
Sakin gashin Asma'u na yi, na ƙara shigewa cikin jikin Mama na kwantar da kaina.
Asma'u ta tashi ta ɗauko ruwan shinkafar, ta miƙa wa Mama, sannan ta koma ta cigaba da aikinta.
Mama ta fara shafa min ruwan a gashina, tana yi min tausa a hankali.
Na lumshe idanuwana.
A wannan lokacin, zuciyata ta yi shiru.
Kuma a cikin wannan shiru, na yi wata addu'a.
Ba don ƙirji na ya girma ba.
Ba don pimples ɗina su ɓace ba.
Ba don gashina ya yi tsawo ba.
Sai don wata rana Allah Ya kawo min ranar da zan amshi kaina yanda nake.'..babu abinda yakai karɓar kanka a yanda kake daɗi
Ranar da zan kalli madubi ba tare da na tsani abin da nake gani ba.
Ranar da zan iya tafiya ba tare da hannuna ya riƙe hijabi saboda tsoron maganganun mutane ba.
Ranar da kalmomin mutane ba za su ƙara samun ikon karya ni ba.
Ranar da zan iya cewa:
“Wannan ni ce.”
“Kuma ban da abin da zan gyara domin in cancanci a so ni.”
Ban san cewa a wannan lokacin, ina addu'a ne ga wata rayuwar da ba zan taɓa iya hasashen yadda za ta zo ba.
Ban san cewa wata rana zan waiwayi wannan ƙaramar yarinyar da ke kwance a cinyar mahaifiyarta, ina kallon ruwan shinkafa yana jika gashinta, sannan in fahimci ainihin ma'anar kalmar da ban taɓa ɗaukar muhimmancinta ba.*
Be careful what you wish for.
Domin wani lokaci...
Allah yana amsa addu'arka.
Amma amsar ba koyaushe take zuwa cikin irin yanayin da ka zata ba.
***
RU'UYAA…📖
₦500 ne idan ya kammala zai koma 800
Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay
Shaidar biya ta ***
Autumn writes 📖🖋️