BUDURWAR ZUCIYA

13-14

by @zahrasurbajo

Bayan an tashi agurin taron direct gidan iyayen amarya aka wuce,inda daga canne kuma aka ɗauko amarya zuwa gidan mijinta.

"wai yanzu haka zamu zuba ido muna kallo Alhaji yayi aure amma ko tsinke be bamu na faɗar kishiyaba yaya?"cewar hajiya lami cikin damuwa.

"hmmmm ni kuma ba shine ya dameniba,wancan ɓangaren daya jibga dukiya aciki shine abunda yafi damuna dan alamu sun gwada ciki zesa amayar tashi,amma mu kuma be gyara mana namuba"cewar hajiya hanne.

"ayko be nemi zaman lafiyaba wallahi dan nide bazan zuba ido ina kallonshi yamin rashin adalciba"cewar hajiya lami.

Haka sukai ta tattauna maganar,har zuwa lokacin da ƴan kawo amarya suka iso gida ya kaure da guɗa da ƙamshin turaren wuta kasancewar zee asalinsu ƴan medugurine.

Babban falon gidan aka wuce da ita inda su hajiya lami suke zaune da mutanensu da suka zo yimusu dannar ƙirji,

Bisa alada nan aka gabatar musu da zee dake lulluɓe cikin mayafi mazaunin abokiyar zamansu gamida roƙon su ruƙeta amana.

Har wajan goma na dare sannan suka  gama watsewa ƴan rakiyar amaryar,aka barta se kuka take aɗakinta ita kaɗai,

Alhaji se sha ɗaya na dare ya iso gidan dan tsarabarsa ta shiga ɗakin amarya,inda ga mamakinsa su hajiya hanne ya samu tsaye a bakin ƙofar shiga ɓangaren amaryar kowacce fuska ba walwala.

"dama kai muke jira ka dawo"cewar lami.

"gashi kuma a halin yanzu sauri nake zani gun amarya banida lokacin yin wata magana yanzu"ya basu amsa.

"wallahi in har kaga mun baka guri ka shiga gurinta to ka sallamemune,amma baze yiwuba wallahi"cewar hajiya hanne.

Ya fahimci da gaske suke hakanne yasa ya dubesu yace "me kukeso?"

"miliyan hamsin hamsin zaka turawa kowacce acikinmu na faɗin kishiya nba hakaba wallahi daren yau muda ƴaƴanmu semun maidashi daren da bazaka taɓa mantawaba"cewar lami afusace dan se yanzunema da taga yadda yake rawar jikin zuwa gun amaryarne taji kishi me zafi na taso mata.

Murmushi alhaji yayi be ce komaiba ya tura musu kuɗin,dan dama hakan ya ware ze basu,yana gama turawar ne yace"to seku bani hanya in wuce tunda na tura"

"amma kasan de baka kyauta mana ba ko?"cewar hanne.

"in Allah ya kaimu gari ya waye,semu tattauna akan wannan maudu'in"cewar Alhajin gamida raɓawa ta tsakiyarsu ya shige ya kullo ƙofar.

Haka suka bar ƙofar ɓangaren zuciyoyinsu cunkushe da ɓacin rai,dan basu ga alamun zaa musu adalciba daga yanayin tsarin da alhajin ya ɗauko.

Shiko ango yana shiga yasamu amarya har zuwa lokacin kuka takeyi,hakanne yasa ya ajiye ledojin hannunshi gamida cire babbar rigarshi,ya ƙarasa inda take.

Akaro na farko kenan daya miƙa hannu ya ruƙo hannunta,cikin sigar rarrashi yake magana"zee kukan ya isa haka pls,bafa wani garin aka kawokiba,kina gari guda da ƴan uwa da iyayenki,kuma aduk lokacin da kika so zuwa inda suke zan kaiki,kuma nida ke ba auren dole bane bansan kukan me kikeyiba,kinmin alƙawarin zaki dinga min kwalliya me kyau,ni na ɗauka ma zanzo in samu kinimin har ina taho miki da choculate"cewar alhaji.

Da sauri zee ta yaye mayafin dake kanta ta ɗago cikin zumuɗi tace "da gaske ka kawomin choculate ɗan shilana?"

"na kawo miki gasu can a leda harda kajin amarcinki ma duk na siyo miki"cewar alhaji yana murmushi.

Ayko da saurinta ta dire akan gadon ta nufi,inda ledojin suke ta fara firfito dakayan ciki,sosai ta shiga farinciki ganin choculate da yawa acikin ledar,ayko nan ta fara buɗewa tana ci,seda ta cika bakinta dashi sannan ta waigo ta dubeshi tace tana murmushi"kai aure niimane ɗan shila,kaga wai nice nake shan choculate cikin kwanciyar hankali ba tare da antymaryam ta dameni in sammataba,haka itama ummana bata dameni da cewa in rage shan zaƙiba,kai wallahi aure da daɗi"cewar zee ckin farinciki,da aduniyarta choculate na ɗaya daga cikin abubuwan dake sata nishaɗi..

Seda ta gama shan choculate ɗin sannan alhaji yasata suka ɗauro alwala suka zo suka gabatarvda sallah ta nuna godiyarsu ga Allah,sannan ta miƙe taje ta sauya kayanta zuwana barci a toilet,sannan ta fito,

Samu tayi shima alhaji yana zaune daga shi se gajeren wando,dan ya tuɓe kayanshi shima,ay zee na arba dashi atuɓe kawai ta fara yimasa dariya tana nunashi tana tafa hannu,ta isa gabanshi,tamiƙa hannu tana mulmula masa tunbi dan shine abinda ya bata dariyar tace"wallahi cikinka irin na sayyid ɗin anty hauwaƙanwar ummana lokain da aka yayeshi haka cikinsa yayi tumbulele"ta faɗi tana sake tuntsurewa da dariya har tana kwanciya ajikinshi.