Chapter 20:RDBG
RAUNIN DA BA A GANI
Meefat ink ✍️ writers
MC yasake duban envelope dinda ke hannunsa sai ya danyi murmushi kafi yace cikin sautin daya ciki hall din “ alright everyone our next recipient is from the…foculty of pharmacy” nan take daliban pharmacy suka fara ihu da yafi, MC yabude envelope din ahankali yakaranta sunan dake ciki sannan yadaga microphone “our next award goes to a student who has shown outstanding commitment, academic excellence and dedication throughout her studies” sai ya dan dakata na wasu seconds, hall din yayi shuru “Miss Ruhaina Ahmad” ruhaina tadaskare a inda take zaune “me?” tafada idanunta suka bude sosai fina ma ta juya tana kallonta tana murmushi tace “tashi mana ruhy” ruhaina ta kalli stage din sannan ta kalli fina da samha kamar wacce bata yarda da abunda kunnuwanta suka jiba. A hankali tamike daga kujerarta nan take aka fara tafi wasu daga cikin abokanta suka Mike suna tafi ita kuma takasa boye murmushin da ya bayyana afuskarta, azan ya juya yana kallon wacce aka kira tabbas inba idonsabane to ita ce wacce yake tason ganin fuskarta tunda suka hada ido ganinta yake yayinda take tafiya zuwa stage cikin nutsuwa, ruhy ta isa stage ta hau matakalar ahankali MC yamikamata hannu “congratulations miss ruhaina” sauke kanta ahankali tai batareda tamika nata hannun ba tace “thank you” MC ya juya wajen audience “ and to present this special award, we would like to invite the executive director of yola holdings group of companies Mr Muhammad azan yola” hall din yasake kaurewa da tafi yayinda idon kowa yakai VIP section, Jayne yadan karkato ahankali cikin rada yace “go on my man” a yadda Jay yayi wa azan magana cikin rada dayawa daga cikin mutane sun dauka Jay ne CEO ba azan ba, daya ke azan yadau kamannin mahaifiyarsa ne sak kuma kammanin turaine dashi shiko Jay yadau kamannin mahainsa wanda yakasance kani ga mahainfin azan wasu sukan ce sudin tagwayene duba da irin tsantsar kamannin dasukeyi, awani sai'in ma mutane suna dauka cewa daddy ne ya haifi Jay ganin yafi kamada shi akan y'ay'an cikinsa toh ayauma hakanne ta kasance.
Azan ya mike ahankali yana jin wajen uncomfortable dan shi bamaison zama acikin yawa ahaka dai yataka ahankali ya nufi stage din, kallonsa take har ya karaso kana ganinsa kasan cewa shidin ruwa biyune, MC yamika masa hannu sukayi musabaya sai ya mikamasa plaque sannan ya kalli ruhaina dan sunkuyar dakai yayi yana kallon fuskarta da kyau yace “ congratulations"sai tadan sunkuyar da kanta itama tace “thank you” sai ya mikamata award din lokacinda ta karbi plaque din sai aka fara daukansu ahoto ta ko'ina sai azan yama wani jami'in companynsu dake tsaye agefe sign, zuwa yayi ya mikamasa wani envelope sai yamika wa ruhy yana murmushi yace “a small gift from yola holdings” sai ta karba tace “thank you sir” MC ma yana murmushi yace “once again let's give her a round of applause”hall din ya cikada tafi. Juyawa tayi tana shirin komawa wajen zamanta sai MC ya dakatarda ita “one moment please” sai ya kalli azan yace “sir, will u like to say a few words to our award recepients?” azan yadan kalli ruhaina sannan ya kalli microphone dinda MC ke mikamasa sai yakarba yayi shuru na dan lokaci kafin yafara “ success doesn't come because someone is lucky, it comes because someone refuses to give up” hall din yayi shuru ana sauraro yacigaba “ I congratulate everyone, keep working hard, keep learning and never underestimate what your efforts can achieve"sai aka fara tafi ruhy tadan daga kai takalleshi ahankali tace “thank u sir” sai ya gyada kai yana murmushi yace “keep going” MC yayi murmushi bayan ya karbi Microphone sai aka cigabada kiran sauran foculty wasu manyan suna bada scholarships wasu internships wasu kuma suna alkawarin daukan aiki bayan kammala karatu da haka aka kammala taro, manya suka fara fita yayinda sauran ma suka bi baya. Acikin hall din kawayen ruhy na zagaye da ita suna kallon award din sai samha tace “yau dai ruhy kinzama celebrity gake ga bature” ai sai suka kwashe da dariya sai farida tace “very handsome bature” suka dinga dariya sai fina tace “kumuje waje mudau hotona dan yaukam sai anjimu a social media” dahaka suka fice daga hall din.