HARAMTACCIYAR GADA

CHAPTER 3

by @hafnancy

*HARAMTACCIYAR GADA.*


_*{Haɗuwar rayuka da ƙaddara ta tattara wuri guda.*🔥💔}_


*NA*


*HAFSAT MUSTAPHA ('Yar Mutan Naija).*


*SADAUKARWA GA UWARƊAKI NA: HAJIYA ZAINAB AHMAD (Hajiya Mama). Amincin Allah da ni'imominsa su tabbata a gareki Uwata.*


 *BOOK 1*

    

  *Page 3.*


A daddafe Yallabai ya yi sati biyu don gaba daya tunaninta ya gama rikitar masa da k'wak'walwa gashi har an kwashi lokaci bata neme shi, hakan yasa ya cire rai da ita ya ci gaba da rayuwarsa.


A sati na hudu da ya kama wata guda sai ga kiranta. Sosai ya cika da farin ciki kwarai, amma sai murna ya koma ciki don ta nuna ita bazata iya aurensa ba kuma ta gaya masa dalili don bata b'oye alak'ar dake tsakaninta da 'yarsa Samha ba, da kuma kasancewarta mazauniya a gidan mata. Duk yadda yaso ya nuna mata cewa hakan ba wani abu bane taki ta fahimce shi saboda tana tsoron Samha sosai.


Har ce masa tayi zasu iya shinfiɗa rayuwa asirrance amma in yaga bazai iya ba to ya fita daga rayuwarta don ba zata iya aurensa ba.


Ba haka yaso ba! 


So ya yi ya aureta!


Ya so ya mayar mata da darajarta ta 'ya mace data rasa!


Amma haka nan yana ji yana gani ya biye mata suka fara rayuwa asirrance don kawai baya so ya rasata. Haka idan ya tashi tafiya zai dauketa su bar gari zuwa kasashen waje inda ake masa gine-ginen gidajen abincinsa. Har watanni fiye da biyu ko uku suke kwashewa.


Allah ya jarabci Yallabai da mugun son Jidda. Yana sonta matuk'a fiye da tunanin mai karatu. Sam bai so irin kazamar rayuwar da suka shimfid'a ba. So ya yi su rayu akarkashin inuwar aure, don tana nuna masa soyayyar da bai samu irinsa wurin Nafeesa ba.


Jidda tana da k'yawawan dabiun da shi kansa wasu lokutan yakan zauna yayi ta tunanin to meyasa take wannan rayuwar?


Amma idan ya tuna cewa kowa da tasa kaddarar tunda gashi shima Allah ya jarabce shi da fadawa cikin kazamar rayuwa. Rayuwar da bai tab'a tunanin wayen gari ya tsinci kansa aciki ba, in ya tuna haka sai kaga yana mata uzuri, don bawa baya wuce kuskure.


Gashi sosai yake sakar mata kudi shiyasa ko kadan bata da matsalarsu sai dai taba wani, kuma kamar Haidar haka ta rik'i Yallabai. Bayan shi bata muamala da kowa kuma fatan ta Allah yasa daga shi bazata sake canza wani ba.



**KOMAWA LABARI.**

   **A wannan Ranar**

    _*5:PM*_


"Ina son ganin duk wata mace da ke gidan nan! kowa ta fito ina da magana saboda wata shegiya ta chakule ni."


Jidda ce ta fito tsakar gida tana ɗaga murya bayan ta gama chat da Saffy. Yanzu so take ta san 'yar iskar da ta bawa Uwarɗaki labarin abin da ya faru.


Sake ɗaga murya tayi ganin kowa ya yi banza da ita bayan ta tabbata duk kunnin da ke gidan ya ji abin da ta faɗa.


Ta ce"Mai kuka maida ni? Ina magana kun yi banza dani. Ku jira ku ga abin da zai faru idan baku fito ba."


Jidda bata fiya ɗaukan zafi ba sai an ƙure ta. Bata kai ga rufe baki ba taga matan da ke gida sun fito har Saffy. Sai dai bata kalli inda take ba don bata ita take ba, ta dubi matan da suka fito suna jifanta da kallon banza.


"Wacece ta je ta gayawa uwarɗaki ana samun matsala da Saffy? Ta fito ta nuna kanta."


Kai tsaye wata ta ce"Na san Azagwai ce domin bamu da munafuka kamar ki a gidan nan."


Azagwai tana gefe tana kirga kuɗin data karɓa na jama'a da take bi bashi, tana jin an ambace ta ta daka tsalle ta ce"Saboda Azagwai ce aka raina ko? Tunda nake gulmace-gulmace ban taɓa tunkarar uwarɗaki da duk wani zance na 'yan gidan nan ba saboda na san yin hakan na iya sa ta kori duk mai kawo mata matsala. Ni kuma ba zan so ace nayi sanadin da zai sa a kori wata daga gidan nan ba don ba mamaki da wannan mafaka ta dogara."


Da sauri Jidda ta ce cikin ɗaga murya"Ya isa haka! Ba taraku nayi domin ayi caa! ba. Ita wacce ta kai gulman na san tana ji na, idan kuma bata gida na tabbata gargaɗin da zan yi tabbas zai isa kunnenta. To ta kiyaye, idan ta kuskura ta sake zagayawa ta kai wa uwarɗaki gulma sai na ci mutuncinta."


Kamar daga sama ta ji ance"Idan kuma nace ni ce fa? Da abin da za ayi ne?"


Cike da mamaki kowa ya kalli SALA, wato mataimakiyar Jidda wacce ta fi kowa yawan shekaru a gidan.


Babu wanda ya ce uffan domin sosai ake shakkarta ganin cewa ita ce ta biyu mai faɗa aji a gidan. Amma daidai da ita itace Jidda kuma ita ma tana ɗaga mata kafa ne saboda ita ce Shugaba. 


Kwata-kwata basa jituwa da Jidda saboda bata biyayya balle tana ganin ta fisu shekaru. Sannan tana adawa sosai da Jidda don ganin cewa ta fita matsayi a wajen uwar ɗakinsu. Ita ce number 002 na gidan mata a yayin da Jidda take 001. Duk wata mace a gidan tana da ID number ɗinta.


Murmushin takaici Jidda tayi ta kalli SALA ta ce"Ban yi mamaki don kin fito kin nuna kanki ba, haɗa rikici a wajenki ba wani abu bane. Duk rikicin da kike haɗawa ba a taɓa kai wa uwarɗaki gulma ba, ana yin shiru ne ba don ana tsoronki ba. Sai don a rufa miki asiri amma ke burinki ki tona na wata."


Saurin taran numfashinta ta yi"Sai ta tona nawa tunda na tona nata." 


Abu kamar wasa fa rigima ta barke tsakanin Jidda da SALA. Da SALA taga ba sarki sai Allah sai ta hakura ta kyaleta.


Saffy dai kala bata ce ba amma ta kudira a rai ko ba yanzu ba sai ta nuna wa SALA ɓacin ranta kamar yadda ta ɓata musu.


Bayan komai ya lafa, Jidda ta koma ɗaki tana tunanin inda zata kai Saffy don bata jin zata iya bari ta rayu a gidan mata. 


Tana zaune ta rafka uban tagumi sai ganin SALA ta yi ta faɗo ɗakin ranta a matukar ɓace.


Jidda ta dubeta ta ce"Me kika zo yi?" Ta furta hakan cikin zafin rai.


Ba tare da ta damu da irin kallon da take watsa mata ba ta ce"Zuwa nayi muyi magana."


"Magana? Ko dai kin biyo ni har ɗaki ne kici mutunci na?"


"Ba cin mutuncinki nazo yi ba! Magana nazo mu yi kan wannan yarinyar da tasa mu musayar yawu."


Jidda ta ce"To, ina jinki."


Sai data zauna kan couch, sannan ta fara magana"Ita wannan yarinyar da aka kawo gidan nan tana so ta jawo matsala. Saboda haka nayi tunanin idan aka bada kararta wajen mai gidan zai sa ta gane kuranta."


Jidda ta numfasa ta ce"Sai kika ga hakan shine mafita? To yanzu da an koreta fa? Kina ganin hakan ba wani abu bane?"


SALA ta mulmula idanu ta ce"Ni ina ruwana? duk wacce ta kawo matsala idan baki ɗau mataki ba, zamu sa uwarɗaki ta yi waje da ita. Ke ma kin san da ace ina da iko ne da tuni mata da yawa sun bar gidan nan." Ta ida magana cikin kunar rai.


Jidda ta kura mata ido, sai da tayi kamar minti 2 tana nazarinta kan ta ce"Ai na daɗe da ganin take-takenki amma ki sani ko ni bani da ikon koran wata daga gidan nan balle ke."


Zata sake magana Jidda tayi saurin ɗaga mata hannu"Tashi ki fita, bana so ki sake furta wata kalma."


Sai data miƙe sannan ta kalleta a wulakance ta taɓe baki ta ce"A shekaru ina gaba da ke! Matsayinki a gidan nan ne ya baki damar raini. To, ki bar ganin ina kyaleki wallahi darajar uwarɗaki kike ci shine yasa nake hakuri ina biyayya a gareki."


Tana gama magana tasa kai ta bar ɗakin a yayin da Jidda ta bita da kallo. Da ace SALA ke matsayin da Jidda ta hau, da an zuba mulki na zalunci. 


Ita dai ta san bada wuta da take yi a gidan tana yi ne kan waƴanda suke da rashin ji. Amma ita SALA nuna iko ne da ita.


Kiran Samha ne ya katse mata tunani. Gabanta ya fad'i amma ta daure ta daga.


"Ki same ni gida yanzun nan akwai d'an tattaunawa mai muhimmanci da nakeso muyi ni dake."


A zaune take amma jin abin da ta fad'a yasata mik'ewa akidime da waya akunne tana fad'in"U….uwarɗaki meke faruwa?"


Tsaki taja tace"Cewa nayi ki zo gida ki sameni akwai maganar da nakeso mu tattauna a kai. Na so inzo da kaina amma bana d'an jindadin jikina ne. Kodayake ban faɗa miki ba, hmm I'm pregnant fa."


Ta furta cike da farin ciki tana shafa cikin, ita dai Jidda kamar wawiya haka takoma. Tsoro ne fal ya cika ranta, gani take kamar Samha ta gano alakar dake tsakaninta da mahaifinta ne don zuwa yanzu alakar tasu ta kara ƙarfi.


Sai data sake jin saukar amon maganar nata sannan ta dawo daidai"Ki min addu'ar samun 'ya mace nayi miki alk'awarin sa wa 'yata sunanki *JIDDATULKHAIR* sabida nuna godiyata agareki! hakik'a kece silar arzik'ina! akanki na fara samun ribar gidan mata! kuma har gobe a sanadinki nake ganin mahaukatan kuɗaɗe don sosai kike tafiyar min da kasuwanci fiye da zatona. Ina tsananin alfahari dake a koda yaushe ALKHAIRINA."


Ta ida magana tana nuna jin daɗinta, ita kam Jidda hawaye ne masu radad'i suka zubo mata.  


'Ace wai alfahari ake da ita ta hanyar aikin sheɗan?'


'Me zai faru muddin wataran Samha ta farga da sanin alakar da ke tsakaninta da mahaifinta?'


'Bayan kuma ta bata dukkan yardanta?'


"Kiyi maza ina jira kuma ki tabbata kin suturta jiki yadda nake so don gidana zaki zo. Ba zan lamunci shigar jan hankali ba."


Dif! ta katse wayar ayayin da Jidda tabi screen da kallo.


"Ya rabb! Ina tsoron haɗuwa da Samha, ba mamaki ta gano alakar da ke tsakanina da mahaifinta shiyasa take son ganina. Kodayake ban ji tashin hankali a muryarta ba tunda har nuna min tayi tana alfahari dani. Ba mamaki kuma kan Saffy ne take nemana domin a tattauna game da matsalar da ake samu da ita."


Share hawayen fuskarta ta yi sannan ta mike ta watsa ruwa. Bayan ta fito ta zura doguwar riga 'yar kanti sannan ta dauko hijab d'inta Jalbab ta ɗora a sama wanda ya sauka har kasa. Wannan shine karo na biyu da zata ziyarci gidanta don ba zuwa take ba, kuma babu wata 'yar gidan mata da Samha ta yarda ta san gidanta in ka cire Jiddan.


Tana fitowa 'yan gida suka fara mata wasa ana yaba kyan da tayi, amma iya murmushi ta yi saboda Jidda akwai kasaita.


Saffy na ganinta ta dakata da share ƙofar ɗakinta tana kallon yadda ake koɗa 'yar'uwarta. Ji tayi ƴar'uwarta ta birgeta, har bata san lokacin data ce "Kai amma Yaya kin min kyau sosai."


"Ke!....kin san me kike faɗa kuwa? ki shiga taitayinki."


Idanun mutane ne ya dawo garesu don ba a ga dalilin da zai sa ta ɗau zafi don kawai an kirata da Yaya ba.


Shiru Saffy ta yi don sai a yanzu take tuna gargaɗin da Jidda ta yi mata. Sai dai anya zata iya ɓoye alaƙar da ke tsakaninsu kamar yadda ita Jidda ke so kuwa?


Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta kalleta bayan ta tanadi abin da zata faɗa"To ki yi hakuri amma ai ba laifi bane don na kiraki da Yaya. Kar ki manta kina gaba da kowa a gidan nan, ba a shekaru ba sai don kin kasance mace ta farko da ta fara rayuwa a wannan gida."


Jidda ba tayi magana ba tasa kai ta fice, don shirunta shi ne alheri. Idan za ta tsaya ta biyewa Saffy sai sun sa an gane akwai alaƙa ta musamman a tsakaninsu.


Bayan fitar Jidda aka yi caaaa! A kan Saffy. 


Wata da ke wanke kwanuka a ƙofar ɗaki ta ce"Wannan yarinyar akwai shisshigi fa! ita ala dole sai ta cusa kai ta shige jikin shugaba. To, bari ki ji sai kin jira saboda akwai tarin mutane a gabanki masu yaƙin son shiga jikinta, sun ci bauta kuma har yau basu samu shiga ba, balle ke da kika shigo jiya-jiya."


Wata ta cafe"Ki bar ɓatar da yawun bakinki, kawai zuba mata ido ta bi sawun 'yan wahala."


Saffy bata biye musu ba ta koma ɗaki, tana ɗaga musu kafa ne saboda ganin idon Jidda amma lokaci na zuwa da zata ajiye nauyinta da take ji ta kwance musu don ta fahimci idan ka nuna kai shiru-shiru ne sai ayi ta takaka.


Bayan shigarta ɗaki ta murmusa ta ce"Kuna maganar shisshigi, da ace kun san matsayin da nake da shi a wajen Jiddatulkhair da baku haɗa ni da wasu 'yan wahala ba."


Sai kuma tayi tunanin alakar gidan mata fa daban yake. Ko ciki ɗaya kuka fito babu wanda ya damu da wani, kowa rayuwarsa kawai yake. Sai dai bata tunanin Jidda za ta watsar da ita.


 ****


Hadiza na gama gyara kai gidan mata ta nufo. A daidai lokacin da ‘yan gida suka yiwa Jidda caaa! A wannan lokacin ita Hadizan ta iso. Amma ta kasa fitowa sai kurawa ƙofar gidan ido da tayi.


Sai a yanzu ne ma take tunanin ko hanyar da take shirin bi domin ganin ta natsar da Samha daidai ne ko ba daidai ba? 


Shi wannan hanya za tayi amfani da wata a cikin gidan mata ne domin ganin ta cusawa Samha ƙunci. Amma ba kowace yarinya ne za taso amfani da ita ba sai wacce take da matsayi a wajen Samha.


Ta so yin amfani da Jidda ganin cewa ita Samha tafi fifitawa, sai dai taki bata haɗin kai. A yau data ji labarin Saffy, taga dai babu wani jituwa a tsakaninta da Samha sai take ganin kamar idan har ta taki sa’a ita zata iya bada haɗin kan da ake so.


Dakyar ta fito ta nufi gidan, suka yi kicibus da Jidda a bakin ƙofa. Da sauri Jidda ta ja da baya gabanta na dokawa sakamakon tunowa da aikin da Hadiza keso ayi don ganin ta kawo ƙarshen zamansu a gidan.


Fadada fara’a Hadiza tayi tana "JIDDATULKHAIR!.....Mace mai tarin alkhairi." 


Ta furta tana mai zare farin tabarau a fuskarta hakan ya basu damar kallon juna cikin k'waya da k'wayar ido. 


"Barka da warhaka..." 


Fuska a murtuke Jidda ta gayar da ita sannan ta raɓa gefenta ta fice. Ko ba a faɗa ba ta san har yanzu Hadizan na kan bakanta ne, tana ganin idan ta matsa mata sai ta fallasa ta.


Duk da cewa Hadiza ta san ba wajenta tazo ba amma sai ta ji aranta tana so ta sake bata dama a karo na ƙarshe ba mamaki wannan karon a dace ta saurareta ba sai ta nemi ganin Saffy ba.


Da hanzari ta dakatar da ita "Da magana fa a bakina, wai meyasa kike min haka?"


Cak! Ta tsaya ta juyo ta kalleta ta ce"Abin da kike so in yi bana ra’ayi kuma idan kika kuskura kika kai ni wuya kinji na rantse miki da sarkin daya busa min numfashi zan haɗaki da uwarɗakinmu don ta san halin da ake ciki."


Ta ida magana da zafinta, nan da nan Hadiza ta sha mur! don bata tsammaci jin hakan daga gareta ba.


Cikin ɗaga murya tace"Ki je abinki na tabbata a gidan nan dai ba za a rasa wacce za ta iya bani haɗin kai ba. Uwarɗakin taku kuma kin daɗe baki kai karana wajenta ba."


Uffan Jidda bata sake cewa ba tsabar takaici, tasa kai tayi gaba abin ta. Da Hadiza ta tabbatar da gaske ba haɗin kai zata bada ba, ta bi bayanta da sauri ta sha gabanta.


Cikin ɓacin rai ta ce"Kina nufin ba zaki bani haɗin kai ba? Baki fi ni son Samha ba da kike ganin kamar ina so na ƙuntata mata ne. Ƙullin da nake so in yi na faɗa miki so nake mu tsoratar da ita ko hakan zai sa ta daina cutar da yara."


"Ke a ganinki ni zan baki haɗin kai na baƙanta ma matar da take matsayin uwa a gare ni? Ko a mafarki ba zan iya ba."


Hadiza ta fusata ta ce"Ina da labarin wata Saffy, matsalar da take haifarwa a gidan nan yasa nake tunanin da zan samu haɗin kanta zata iya aiwatar min da aiki da kyau."


A razane Jidda ta ce"Aunty Hadiza!!!"


Ta ambaci sunanta tana buɗa mata ido har sai da Hadizan ta ɗan firgita.


"Ki je ki yi ƙullin da kike so kiyi amma karki kuskura ki shiga gonar wannan yarinyar." 


Tana gama magana tasa kai ta yi gaba, ta bar Hadiza nan tsaye da mamakin abin da yasa ta hana mata ganin yarinyar. Sai dai gargaɗin da Jidda tayi bai sa ta hakura ba, dole ta magance abin da suke fuskanta.


Ta ce "Duk yadda za ayi sai na haɗa ƙullin nan don ba zan zuba ido ina kallon Samha tana cutar da ‘ya’yan mutane ba."


Tana gama faɗin haka tasa kai ta shige mota da nufin ƙara dawowa idan ta sake sabon shiri.






#HaramtacciyarGada

#2026 Novel

#HAFNANCY📚✍️

***/***


*NAGODE ALL❤️🙏*