Episode 6
by @zahraroyal
*GANGANCI*
©️ZAHRA ROYAL STAR
*TALLAH TALLAH TALLAH*
LADY'S BEAUTY PALACE
MACE SAIDA GYARA
SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE?
KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU?
KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI?
KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA?
Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa,
Shin kinason ki koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?ko kina neman inda za,a gyara maki Kai ne wato saloon
To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,
MAZA KI ZIYARCI LADYS BEAUTY PALACE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,
LADY'S BEAUTY PALACE
ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻
Zumar kiba
Zumar breast
Zumar hips
Zumar infection
Zumar sliming
Zumar sabon budurci
Back to virgin
Abayas
Atamfa
Lace
Hijabs
Supplements
Kayan yara da dai sauran Su kuma muna bada sari yadda zaki siya Ki samu riba kema
Location Katsina state
WhatsApp or call ***
TikTok Hajara Rabiu ( Ladys beauty place)
PAGE 6
AMRA POV
zaune suke akan darning table suna breakfast, Mom ta kasa hakuri ganin yadda Amra ta fito da wata irin shiga ta k’ananun kaya ta ce.
“Shin wai Amra ban hanaki irin wannan shigar bane koda Yaushe?”
Turo baki Amra tayi tana aje chokalin da take cin abincin dashi tana kallon Daddynta dake cin abincinsa hankalin kwance. D’agowa yayi suka had’a ido ta k’ara shagwab’ar masa da fuska kamar zata saki kuka.
“Please Mom Amra ki barta ta karya cikin salama mana, ina sauri ne zamu fita tare da ita zata je shopping na kayan da zatayi tafiyar nan dasu, kuma kina son b’ata mana time”
Baki sake Mom ta aje ruwan da take shirin kai bakinta tana kallon Daddyn da mamaki ta ce.
“Au ba’aza fasa tafiyar nan ba dai ko?”
Shiru yayi mata saita dawo da dubanta wajan Amra da tayi saurin d’auke kanta gefe tana turo baki.
“Wato ke baza kiji shawarar dana baki ba akan fasa tafiyar nan ba ko Amra? Ina guje miki yin tafiyar da zata zo kina dana sani a cikin rayuwarki daga ke har Mahaifin naki wallahi”
“A’ahhh haba Kharima miye haka kike magana akai ne? Addu’a fa zakiyi mata taje ta dawo lafiya amma zaki tsaya kina wasu maganganu marassa kan gadon irin haka”
Sauke lumfashi Mom tayi tunda taji Daddyn ya kira sunanta tasan maganar ta shigesa sosai dan haka ta kallesa sosai ta ce.
“Ni mi yasa bazaka tab’a sauraran abunda nake so bane akan Amra idan ta ce dole tana son abu? Sai kawai mu rink’a biye mata?”
“Bana son irin maganganun nan, tafiya ce Kharima Baza’a fasa ba idan yaso idan ta dawo bazata k’ara tafiya wata k’asar ba saida mu”
Yana k’ara maganar ya mik’e kamar jira Amra take ya mik’e itama ta tashi tana d’akko mayafinta tasa a saman kayan jikinta zata bi bayan Daddy Mom tayi saurin kwatsa mata tsawar data mugun firgitata a zabure ta dakata Mom ta nuna mata hanyar saman bene tana cewa.
“Maza ki koma ki sanyo Hijab, idan kika sake kuma wallahi kika je shopping d’in kika kwaso kaya k’ananu irin na sawar arna zaki ci ubanki ne wallahi”
Ta idasa maganar babu wasa akan fuskarta, Amra lokacin har wasu hawaye sun taru a cikin idonta, dan ba’a saba mata tsawa irin haka ba. Ganin babu Daddy a parlon bare ya kwaceta yasa ta dole kumawa ta sako Hijab d’in har k’asa tana tafiya tana b’ata fuska danji take kamar ta saka k’aya a jikinta tayi mugun takurata dan tafiya da ita kamar zata kifa a k’asa haka take tafiyar tsabar bata saba saka Hijab har k’asa irin haka ba.
Sadda ta fito tana kallon Mom da kallon ta tausaya mata ta ciro Hijab d’in idan yaso ta saka wasu kayan, sai taga Mom ta juya mata baya ta ci gaba da abunda take yi, ganin haka yasa Amra sakin wani kuka Mom najinta tayi banza da ita.
Har saida wani mai gadin gidan nasu yayo sallama cikin parlon yana cewa Hajiya Alhaji na waje a cikin Mota yana jiran k’aramar Hajiya, ya ce ace ta fito su tafi.
Mom bata iya cewa k’alaba har Amra tabi bayan mai gadin suka fice.
Sai lokacin Mom ta saki wata ajiyar zuciya tana yin tagumi hannu biyu-biyu, wannan tafiya ta zame mata alak’ak’ai a cikin ranta, mi yasa take jin kamar idan Amra d’in ta tafi bazata sake ganinta ba? Kodai kawai ta shirya su tafi tare wata k’ila hankalinta da tunaninta sai yafi kwanciya? Jinjina kai kawai tayi tana ayyanawa a cikin ranta bari su dawo ta tari Daddyn da maganar.
A wajan Amra tana bud’e Motar ta shiga batai magana ba har driver yaja motar suka fara tafiya da sauran Motocin dake bin bayansu guda biyu, Daddy na kusa da ita yana waya ya dad’e yana amsa wayoyi kamin ya sauke ya dubeta ya ce.
“Yaya dai My Daughter?”
Kamar jira take ta sakar masa kuka tana kallonsa ido cike da hawaye ta ce.
“To ba Mom ba ce Daddy wai dole saina saka Hijab ba, kuma duk ta takurani saura kad’an ta tab’e ni k’asa na fad’i ba”
“Sorry Amra kin San dai halin Mom naki, kuma ma ai Hijab d’in tafi miki kyau, baki kalli kanki bane?”
Amra na turo baki ta girgiza kai, Daddy ya shiga rarrashinta yana cewa.
“A ina kike so ayi shopping d’in”
“Yawwa Daddy mu biya ta unguwarsu Rooma zamu d’auketa da Asy”
“Baki rabu da Rooma kamar yadda Mom d’inki ta ce?”
Amra saita b’ata fuska sab’anin da data fara murmushi.
“Daddy wallahi Rooma bata da matsalar komai, kawai dai ita haka yanayinta yake dama sai Mom taga kamar bata gari bace”
Jinjina kai kawai yayi duk da shima Rooma d’in bata yi Masa ba, to amma tunda y’arsa nason ma’ala da ita baida damuwa akan hakan, Amra bata masa k’arya, tunda tace bata da matsala so shima ba wata matsala bace a wajansa.
Wata unguwa suka je bayan Amra ta gaya ma drivern inda zasu fara zuwa, shi kam Daddy dama Mota Uku ce ke bin bayansu dan haka ya tsaya ya ce ma Amra su tafi da Mota biyu shi zai shiga d’ayar zai wuce yana da mahimmin wani abu, suyi shopping d’in yadda suke so karta wani damu ya bata ATM nasa.
Bayan wucewar Motar Daddy Amra ta shiga kiran Rooma a waya, da ihu da murna ta suka fara wayar kamin ma ta kashe wayar sai Gasu sun fito, da yake daga gidansu Rooma da bakin titi fitowa kawai zakai daga gida sai bakin titi.
Dole Mom tak’i su Rooma domin daka gansu zaka fara cewa tabbas zubinsu zubin karuwai ne irinma masu ajin nan wadda suka dad’e a harkar barikin nan. Rooma sanye take da wani sikit yayi mugun matseta ya fito da dirinta sosai sai wata riga datasa ita kuma ta sauka daga bayanta ta d’an rufe mata mazaune kad’an, daga gaba kuwa da kyar ta rufe cibiyarta dan motsi kad’an idan tayi ana iya hango cibiyar tata, ga uban kitson doki tasha wadda ya saukar mata har duwawu an wani bazashi, sai wani d’an mayafi data d’ora saman kan wadda dashi da babu duk d’aya. Asy kuwa ita sanye take da Abaya k’arar Dubai itama tasha kitson doki an bazashi mayafin Abayar ma a kafad’a akasa shi, su duka suna da hujan hanci har biyu irin na gaggun y’an barikin nan.
Suna shiga motar suka fara sakin shewa suna tsokanar Amra Wai ya zata zo masu da Hijab kuma tana abu kamar kanta bai waye ba, ya zata b’ata masu tafiya kuma?…………