SEED OF DESTINY
by @maryam730
Tambarin kan zaki ne a jikin gate ɗin,sai ƙyalli yake.Yayin da manyan security lights suke haska ko ina. Cameras suna nan kusan kowanne lungu da saƙo, wasu a bayyane, wasu kuma a ɓoye cikin tsarin ginin.
Tsayawa tayi a bakin gate ɗin,tana ciro wani card a jakarta tayi scanning ,sai daya gama tantance ta kafin gate ɗin ya buɗe kanshi.Shiga tayi gate ɗin farko, parking space ne gari guda,sai wasu manya-manyan motoci a gurin.Wani gate ɗin ta nufa wanda yafi wancan kyau da tsari.A nan securities ne birjik, masu kalar kaki daban-daban.Sojoji da ƴan sanda sunfi yawa,saboda sai ka rantse barikin sojoji ne ko headquarter ƴan sanda.Gaba ɗayan su babu rahama a fuskar su.Ga wasu hatsabiban makamai a hannun su kamar za'a yaqi.Qarasawa gurin tayi,duk da sun santa amma sai da su kayi searching ɗin ta Kamar wata Ƴar ta'adda kafin su barta ta shiga.
Wani qaton Compound ne,ya subhanallah it's extra luxury complex,amma nan babu mota ko ɗaya saboda baa bari shiga second gate da mota sai mai gold card.Guri ne da ya haɗa komai da komai guri guda.Kama da ga Five star restaurant mai girman gaske, luxury hotel, private suites, conference rooms, VIP lounges,gurin games kamar su chess, hockey, polo, da kuma babban event halls da ake amfani da su wajen manyan taruka da abubuwan da ba kowa ake gayyata ba.
Ga ƴan gari GRAND CREST aljannar duniya ce da gurin manya- manyan mutane ke zuwa.Amma ah duniyar ƴan siyasa wata duniya ce daban wacce dokokin da sirrika masu girma.
Babban ginin yana da deep ivory da dark charcoal colour,yayin da golden details suka zagaye windows, pillars da entrance ɗin. Ba launi ne mai haske ba, amma yana da wani irin elegance da yake sa mutum ya san tun kafin ya shiga cewa wannan ba guri ne na qananan mutane ba.
A kowane ɓangare na wurin akwai security personnel sanye da black suits. Wasu suna tsaye a entrances, wasu suna sintiri, wasu kuma suna kula da monitors daga security posts.Ƙofofin shiga na dauke da scanners,cameras suna kallon kowane movement,sensors suna nan a wuraren da mutane ba sa iya ganewa. Kuma abin da ya fi ban mamaki shi ne yadda komai yake cikin nutsuwa,babu hayaniya,babu tashin hankali.
Wucewa Maleeka tayi zuwa hallway ɗin da ya haɗa babban entrance da sauran sassan gurin. Floor ɗin an yi shi da polished black marble wanda yake sheƙi har yana mayar da reflection ɗin fitilun da ke saman ceiling.Wanda yake dauke da wasu luxury chandeliers masu unique design suna qarawa gurin elegance.
Babu hayaniya sosai,sai sautin waqa da yake tashi a hankali a hankali.Komai a tsare yake,daga kan lighting har zuwa furnitures ɗin gurin hallway ɗin.
Sanyin air-conditioning ya sauka akan fuskarta da wani cool and luxury scent da yayi mixing da . Wurin ya kasance spacious, clean and almost unnaturally quiet. Babban chandelier mai tsananin kyau ya rataye daga ceiling,yana bada wani cool haske mai laushi akan polished marble floor.
Reception area yana gefe guda, restaurant ɗin kuma yana can gaba, yayin da elevators suke gefen dama suna kaiwa hotel floors da private suites.A wani gefen kuma akwai hanyar da take kaiwa zuwa conference rooms da babban event hall.
Elevator ɗin da zata Kaita ɓangaren offices ta shiga.Ita kanta elevator ɗin abin kallo ce.Office ɗin manager ta nufa,kwankwasawa tayi aka bata iznin shiga.Shiga tayi da sallama ɗauke a bakinta , wata babbar mace ce zaune akan kujera tana danna waya ɗagowa tayi tana murmushi ta buɗe mata hannu tana cewa 'daughter har kinzo", hugging ɗinta Atti tayi tana cewa "Ay Anty JAMILA na ma ɗan makara" murmushi hajiya jamila tayi tana kara rungumota tana cewa "nadan wani abune ya riqe ki, ya makaranta yasu Ummu " atti ce tace " lafiyar su qalau Alhamdulillah,ummu ma ta ce ta na gaishe ki " Hajiya Jamila tace "ina amsawa " ,tashi "atty tayi tana cewa Anty bari in qarasa ciki ", "toh shikenan nima zan shigo anjima".Fita tayi ,hajiya jamila na binta da kallo.Ita dai Allah ya ɗaura mata ƙaunar wannan yarinya jin ta take kamar ƴar cikinta wallahi.
Bayan ta bar office ɗin, nufar changing room tayi nasu na ma'aikata ta canja kayanta.Ta fito tana cire face mask ɗinta saboda dokar gurin kenan.Direct cikinp main ground floor na restaurant ɗin ta shiga.
Duk da kusan kullum sai tazo,amma kullum in tashigo sai taji kamar yai ta fara zuwa.
Atti ta ƙarasa shiga cikin makeken restaurant ɗin,tana nufar bangaren da yake ɗauke da wani tanfatsetsan kitchen.Shiga ke da wuya ƙamshin abinci ya daki hancin ta.Kama daga na gargajiya dana ƙasashe daban-daban. Kitchen ɗin ya cika da hayaniya,wasu waiters na shiga suna ɗaukar plates, wasu kuma suna fita suna serving customers,yayin da chefs ke ta girka abinci iri-iri making the place lively.
"Assalamu Alaikum!" Atti ta faɗa cikin fara'a tana wucewa, tana gaisawa da ma'aikatan restaurant ɗin ɗaya bayan ɗaya. Kusan kowa ya amsa mata da murmushi, alamar ta zama kamar 'yar gida a wajen kuma kowa ya santa.
Ƙarasawa tayi wajen wasu yan mata guda biyu da musulma da christian,da suke busy suna shirya trays."Madam Makaroni" ,Musulmar ta faɗa tana murmushi.Atti ce ta harare tana cewa"Yanzun ne HALIMA na makara fisabillilahi,duk wannan uban sammakon da nayi?"
Christian din ce ta yi murmushi tana cewa " ƙyaleta mana, ai saboda yau ta rigaki zuwa ne, shi yasa take ta mana fi'ili ",Halima ce ta taɓe baki. "To ai gaskiya nake faɗa",Atti ta girgiza kai tana murmushi. "Batta dai SONIA,Allah ya shirye ta.Dukansu suka sa dariya.
A daidai lokacin, wata black beauty ta shigo kitchen ɗin dauke da murmushi a fuskarta, Atti ta fara hangowa,sai ta karkatar da kai tana murmursh,Atti ce tace"Ehen... ga Salma tattabarun soyayya nan,ai tunda ban ganki ba, nasan kina can kina ƙona zuciyar wani".Kitchen ɗin ne gaba ɗaya ya kaure da dariya,
Salma ta tsaya tana musu hararar wasa. "Wallahi ku ba za ku bari mutum ya huta ba,kullum sai kun samu wanda za ku yi wa dariya".Atti ta yi murmushi daya kara fitar da asalin kyanta na shuwa arab tana cewa"Mu kuma? Haba Salma,da ga faɗa gaskiya",Sonia da take dariya har da riqe ciki ce tace,"Ke dai Atti, yau kin tashi da rigima",Atti ta ɗaga kafaɗa,ta na bata amsa da "Ba rigima ba ce... observation ne",Halima ce ta yi dariya tana cewa"Kin ji Turanci",Salma ta girgiza kai tana murmushi. "Allah dai ya ƙara muku hankali."
Atti ce ta fara karbar trays ɗin da su Sonia suka shirya tana fitar da shi ,aiki suke yi cikin tsari da nutsuwa,ba abinda ke tsayar da su inba musulman cikin su da suke sallah ba,har karfe 7:00,sai kuma lunch da sukayi.Qarfe 7:00pm tayi a nata kiraye-kirayen sallar magrib inda time din tashin su yayi.Sai kuma yan night shift zasu karɓa.Head of staff ne ya shigo suna kiran shi Mr Samuel fuskar shi a washe, ya ɗaga murya yana cewa ""Ladies and gentlemen... Kowa in ya gama ya tafi meeting room!".Nan da nan kitchen ɗin ya rikice da hayaniyar farin ciki saboda sun san salary ne yazo.
Kitchen ɗin suka gama gyarawa tsaf kafin ƴan night shift suzo.Meeting room suka nufa gaba ɗayan su.
Zama su kayi suna hirar su qasa,ana wasa da dariya.Hajiya Jamila ta shigo,inda kowa ya fara gaishe ta ,ita kuma ta amsawa cikin wasa da dariyar da suka saba.An gama gaisawa sannan aka fara meeting gadan-gadan.Sai daya ɗauke su lokaci me tsaho kafin su gama.Bayan an gama meeting ne, Mr Samuel ya fara kiran suna ɗaya bayan ɗaya ana bawa Kowa envelope ɗinsa,godiya su kayi kowa ya koma gurin sa.
Bayan an gama rabon ne Hajiya Jamila tayi gyaran murya, murmushi da rahamar fuskar ta na ɗaukewa.Fito da wata baƙar takarda ta rubutun ja jikin ta tayi.
__________
Titin Lagos yayi duhu sakamakon qarshen wata da ake ciki.Garin yayi Shiru na ban mamaki. Yayin da dare ya zama mahutar bawa ,a gurin wasu shine lokacin harqalla.Wasu motocine baƙaƙe biyu ke gudu na tashin hankali a kan titi kafin kuma su rage gudu suna jeruwa.Window ɗin motocin aka zuge ta ciki ,gaba ɗaya kayan jikin su baqi qirin baka ganin komai hatta da hannun su da baqar safar hannu .Mutumin dake cikin motar dama ne ya miqo hannun sa da wata jakar qarfe.Bude jakar yayi yana nunowa na ɗayar motar.Daloli dari-dari ne cike a jakar bandir-bandir.Rufewa yayi ya miqo mai .Shima ɗa yan xiro hannu sa yayi da wani kati baqi da rubutun ja a jiki,da tambarin zaki a jiki.Exchanging sukayi,ba tare da sun furta Ko kalma ɗaya ba.Jinjina 👍 su kayi wa juna kafin suka qara wa motocin gudu ɗaya tayi hagu ɗaya tayi dama.........end of chapter 3.......
By
Written by
Muraimaa Naabba ✍️✍️